*MASARAUTAR MAYU!*
*WRITING AND STORY*
*UMMUH HAIRAN*
*MARUBUCIYAR*
👇🏻
AMINIYA KO KISHIYA
HABIBULLAH
QUEEN FARHA
GIDAN UNCLE
ADANDI
WACECE NI
AURAN BAZAWARA
DHOOM ISHAQ
MATAR LAMEER
DUBAI
AND NOW👇🏻
MASARAUTAR MAYU!Free *P 7-8*
Kallon Baiwa Zurjar Najmah tayi tace “toshi meye yasa yake bibiyata?" Miqewa tayi tace “ya kasance yanada wani fitinannen kyau da akayi ittifaqin babu macen da zata burgeshi face ke daya sannan Kuma ya kasance gamayyar halitta tsakanin jinsin mutum da aljanu wannan dalilin yasa babu wata mace da ake hasashen zata dauki halittarsa saike kadai,
Zuwa yanzu Yarimah Nurain yakai mizanin da yake buqatar mace wannan dalilin yasa ya fantsama neman sanin inda zai nemoki aka tabbatar masa a jiya kina hanun Yarimah Isham Kuma shima yanada burin mallakarki ne wannan dalilin yasa ya taso tawagar jaruman zaratan aljanu wanda ya kasance shine jagoran tafiyar suka nufo wannan nahiya tamu domin daukarki su tafi dake nahiyarsu.
Malaman addininsu da manyan matsafan duniya sunyi ittafaqin cewa kasancewarki tare da Yarimah Nurain yana nufin lalacewar Shirin manyan matsafan duniya saboda ke kin kasance wani haske cikin hasken sihirinsu wanda dashine suke sanin me duniya take ciki..."Suns tsaka da wannan tattaunawar sukaga wani duhu yana mamaye idanuwansu har takai ga basa ganin komai hattada tafukan hannayensu tare da wata iska me qarfi wacce ta janyo durqushewarsu suka dunqule guri guda bayan kamar wucce wani gajeran lkc sai sukaga komai ya fara washewa cikin daqiqa goma sha uku wani haske ya mamaye ko Ina suka sauke ajiyar zuciya tare da qoqarin miqewa amma sai Najmah ta kasa miqewa tajita kamar a daddaure.
Dago idanunta tayi ta saukesu akan wani jibgegen tsuntsun kanari da tunda take ko a tarihi bata tabajin lbrnsa ba, kafin ta dawo daga wannan nazarin taji ya cafeta ya cillata a bayansa ya daga manyan fuka-fukansa yayi fiffika ya tashi ya karci qasa ya keta hazo da ita,
Abinda ya qara harzuqa tsoronta ta rinqa mirginawa domin tayo qasa amma ta kasa, saima wata iska da ruwan kibbau da akeyi mawa wannan tsuntsun kanari Amma yaqi dakatawa da uban gudun da yake shillawa da ita har saida suka ratse katangar birnin Jawal suka keta fadar Zamhar suka Kuma ketawa ta cikin birni Zauhar suka lula sararin samaniya.Dukan bayan tsuntsun takeyi da qafafun ta shikam kamar ma bayaji sai sake sama yakeyi gashi maganar duniya tsuntsun yaqi kulata, babban abinda ya gigita duniyar ta shine yanda duk wani nau'i na sihirinta yaqi aiki.
Ganin batada wata mafita yasata zubawa sarautar Allah ido itadai a haka har bacci ya dauketa batasan meye ya faru ba sai farkawa tayi taganta kwance a saman wata dardumar kilishi gefenta ga wasu kyawawan yammata nan sunata yi Mata fifita alamu sun nuna sansaninsu ne,
Zabura tayi ta miqe da sauri taga Suma sun miqe tare da Dora hannunsu saman goshinsu mamaki ya cikata ta zuba musu ido tana kallonsu tare da nazarinsu daya bayan daya har tazo kan wata yar dattijuwa sannan tace “inane nan kudin su waye waye yasaku ku satoni?"
Qasa dukka sukayi da kansu wannan dattijuwar tace “gabanki da bayanki salamun ya shugabar kyawawan duniya haqiqa mu mun kasance bayi a gareki munabin umarnin ubangidanmu ne Yarimah Nurain yabamu umarnin ko quda kada mu bari ya sauka saman fatarki ya abar qaunarsa Sarauniyar masarautar Fazbar"Numfashi ta sauke tare da sauka dagakan kilishin ta fara taka qafarta cikin yashin dayake mamaye da gurin ta sunkuya ta debi yashin ta dagashi ta hurashi ta zuba masa ido ta kalli inda yakeyi ta karkade hannunta ta juya ta bawa inda iskar takeyi baya ta daga hannunta tare da lumshe idonta ta fara bautarta suka zuba Mata ido wannan ya kalli wannan wannan ya kalli wannan harta gama ta matsa jikin wata qorama da ruwa yaketa gudu ta sanya hannunta ta diba tasha ta Kuma tasha sannan ta wanke fuskarta.
Wadannan Bayi suna tsaye suna kallonta harta gama ta miqe wata jikinsu ta dauki wata baqar riga ta matsa ta miqa mata ta sanya hannu ta karba ta zame ta jikinta suka rufe idanunsu har saida ta gama shiryawa sannan suka gabatar Mata da danyar Madarar raqumi da gasasshiyar hantar saniya sai gurasa me zuma.
Da farko qinci tayi saida taji wata cikin hadiman tace “ya shugabata muna fatan ki kasance cikin aminci da yardar ubangijin Annabi sulaimanu dan Dawud babu abinda zai sameki ke kin kasance abar girmamawa a garemu tare da yardar ubangidanmu da yake filin daga yana fafatawa domin cikar muradinsa, ya umarcemu damu kula dake fiye da yanda zamu kula dashi ya umarcemu da kada mu barki ki shiga wani hali na kadaici ko damuwa sannan ya umarcemu da idan ya wucce kwana hudu bai dawo sansaniba mu daukeki mu tafi dake masarautar Qubhar mu kaiki gurin mahaifiyarsa Sarauniya Badiyyah"