MASARAUTAR MAYU
_Ki biya ta wannan acc din 0255526235 Fauziyya Tasi'u Umar GTB_
_Idan katine ki dauka hotonsa ko pin lambobinsa ki tura ta WhatsApp number 09013718241: idan VTU ne ki tura ta wannan number_
👇🏻
_09031307566_*MM 21-22* Murmushi yayi Mata yace “meyesa kikeso ki san wani abu game da rayuwarki ta baya?" Sake kwantawa tayi a jikinsa tace “kawai dai inason sani ne yakai mijina jikina yana fadamin akwai wani abu boyayye a game dani"
Gyara zamansa yayi ya dago fuskarta yace “haqiqa kin kasance mace mafi qololuwar daraja a wannan zamanin da kowanne namiji harma mata yan uwanki suke burin mallaka badon komai ba saidon samun damar qaruwa da sirrin da ubangijinnmu ya tanada a jikinki ki"
Nan take ya warware Mata komai game da ita tare da cewa “haqiqa yake matata kiyi sani a halin yanzu mahaifanki suna hannun taqadirin mushrikin nan da kuke fautawa a baya wato boka rundatu yana azabtar dasu da nau'uka na azaba kala² domin kawai su sanar dashi inda kike, saboda azabar da yakeyi musu nasa aka zare kariyar birnin nan guda daya domin ya samu damar ganin inda kike alhmdllh ya gani harma yayo hawa ya taho Nahiyar nan domin qwatarki ya tafi dake"
Kallonsa takeyi jikinta a mace tace “amma meye yasa yakeson mallakata shima?" Miqewa Yarimah Nurain yayi ya nufi dakin baccinsu da ita ya zaunar da ita bisa gado yace “wani bangare na duniya sunason mallakarki saboda amfani da jininki domin daukakar darajarsu inda wasu kuma kaso masu yawa sukeson mallakarki domin karbar wannan zoben dake hannunki a yayin da yayan sarakai irina keson mallakarki saboda su massheki sadakarsu suke kallonki sunajin dadi i zuwa yanzu masu burin mallakarki domin budurcinki ya haska buwayar izzarsu da daukakarsu sun riga sun makara kasancewar ni daya Ubangiji ya bawa wannan damar saura mataki na gaba wanda duniya ta miqe tsaye dominsa"Numfashi yaja ya fara shafa saman kanta tare da durqushewa ya dora hannunsa saman qirjinta yace “idan ya kasance ubangiji ya nuna buwayarsa a karo na biyu mun samu rabo a dararenmu guda biyu an sake samun cudanyan gamayyar halitta a karo na biyu to shakka babu hankalin matsafan aljanu na duniya zai qara tashi kasantuwar suna baqin ciki da cudanyar biyu a cikin daya,
Idan har jinsin halitta biyu ya hadu tsakanin jinsin mutum da aljanu to wannan da da aka samu a wannan kadaici yakan tashi da wani qarfi na buwayar duniya a inda yakan zamewa jinsin mutane dama aljanu abin shayi, kamar daini a yanzu Yake wannan Mata tawa kiyi sani akwai damarmaki da yawa da zaa iya ratso birnin Faris a shigo fadar Fazbar amma kasantuwa ta a cikinsa ya hana wannan damar tasiri, abu dayene zai kasance gushewar nasarata akan duk Wanda mukayi gaba da gaba dashi, ba komai bane wannan face fadawa abinda yake barratacce daga abinda Allah ya halattamin da daga nau'in qawa da jin dadin rayuwa, tabbas a ranar da wannan qaddarar zata fada kaina zanyi baqin ciki mara misali harma zan kasance cikin marhabin da mutuwa ta fiye daci gaba da rayuwa Najmah ba komai bane wannan abu face zina tabbas duk ranar da hakan ta faru nikuma zan iya kashe kaina duk da nasan bazan iya kare kaina da komai ba sai abinda Allah ya kareni dashi"
Kallonsa takeyi a mamakance tace “me zaisa hakan ta faru dakai bayan ka kasance me raba darenka wajen bautar ubangijin muslumci ka kasance me kiyaye dokokinsa sannan Kuma ina tare dakai?"Lumshe idonsa yayi yace “gabbai sukanyi yaqi kamar wasu sadaukai amma basa iya yaqi da alqalamin qaddara saidai sukayi qumaji wajen kauce Mata, Yake matata kiyi sani kamar yanda ake farautarki a matsayi mabambamta nima haka matan sarakunan aljanu da yayansu dama na bil'adam suke farautata Abu daya yake kareni cikin kariyar Allah shine suturta fuskata da nakeyi na kasance tun Ina yaro mahaifana basa barmin fuskata a bude wannan umarnin Gurail Uzair ne har kawo lkcn da kika kasance mata a gareni, kin kasance kece mutum ta uku data taba ganin fuskata a zahiri, kema don kin kasance mata ne a gareni dole ne ko ban bayyana miki kaina da rana ba zan bayana miki da dare wannan dalilin yasa naga banga amfanin boye miki abinda ya kamata ki sani ba"
Jinjina Kai tayi tare da Dora hannunta saman qirjinsa ya dago ya hauro gadon ya rufeta da faffadan qinjinsa tare da zuge musu labulen sutura ya dora hannunsa a kan qirjinta yana zagayewa tare da wasa da duk wata gabba ta jikinta itama tana tayasa sunajin dadinsu sosai namijin gaske ya mantar da ita tunanin inda zata fara domin samo iyayenta, ya jiyar da ita dadi mara misali a wannan rana sun kasance cikin wata ni'ama ta musamman har zuwa yamma sallah kawai ke tashinsu suyi suci yayan itatuwa su sake komawa cikin halwar qauna,Koda dare ma bai fita ba yana manne da matarsa sunata bawa furensu ruwa qauna ce me qarfi take shiga tsakaninsu wacce kowannensu yakejin idan babu daya bazai iya rayuwa ba, masoyan asali basusan cewa ga wata qura can ta tunkarosu ba.
Haka rayuwa taci gaba da tafiya a yanzu Najmah nada sati uku da zama cikakkiyar mace duk yanda Yarimah Nurain yakeso ya dauketa su fita domin zagayawa kilisa iyayensa sun hanasa kullum cewa sukeyi su bari akwai lkc hakanan suke hqr har zuwa lkcn da canje canje suka fara bayyana a tare da Najmah na shigar ciki jikinta.
Wayyoh murna a wannan masarauta Sarauniya Badiyyah da Sarki Fauwaz kamar su hadiye yayan nasu shikuwa Yarimah Nurain sai wani sussunne Kai yakeyi tare da tsananin kunyar matar tasa da iyayensa baya yarda su hada ido da daya daga cikinsu, itakam Najmah mamaki kunyar mijin nata take bata ita da take mace bataji kunyarsa ba sai shine yakejin kunyarta.Haka suke rainon wannan ciki cike da kulawa da tattali har zuwa lkcn da yakai watanni uku a lkcn ne Kuma jita jitar samuwar cikin ta karade duniyar wannan qarnin, wata rana suka shirya domin zuwa Qudhar masarautar Sarauniya Badiyyah kasancewar dama watanni take rabawa tsakanin masarautar Fazbar da Qudhar.
Sunyi shiri na ban mamaki tare da shirya dakaru suka dauki hanya tafiyar qasa ce zasuyi bisa dawakai kasancewar Gurail Uzair ne ya shawarcesu da suyi hawan turba saboda a wannan lkcn gungun matsafan aljanu suna meeting na yanda zasuyi su sace Najmah da abinda ke cikinta.
Haqiqa Allah yakan bawa kafiri dama ne akan mumini bawai don kasawa ba aa saidon gwada qarfin imanin muminin da Kuma qara dulmiyar da kafiri cikin duhun bata bayyanan ne, hakance ta faru da wannan ayari.A rana ta ashirin da hudu daren goma sha hudu da fara tafiyarsu suka isa wani kyakkyawan daji me cike da ni'imar dogayen bishiyoyi da tsaunuka gami da ciyayi masu sanya zuciya kwadaituwa da yada zango a gurin, Gimbiya Najmah dake kwance jikin Yarimah Nurain ta dago ta dubeshi shima itan yake kallo tayi masa murmushi tace,
“Haqiqa zuciyata ta kwadaitu da son hutawa a gurin nan, kayiwa Dakarun musulumci umarnin bincikar dajin idan lfy yake su kafa mana tanti zanso hakan Kuma zanji dadi yakai mijina" shiru yayi yana nazarin mgnrta kafin daga bisani ya sauke numfashi yace “kinsan dai da cewa farautar rayuwarki akeyi"
Murmushi tayi tace “na yarda da cewa babu abinda zai sameni face abinda ubangijin Muslumci ya qadarta min nidai inason gurin nan mijina kayimin alfarmar nan" baiso tsayawar ba saidai yanason farantawa matar tasa hakanne yasashi bada umarnin dakatawa take dakaru suka tsaya yayi musu Umarnin bincikar dajin haka kuwa akayi suka bazama suka shiga dajin suka dubashi sosai ganin babu wata alama ta wani abu na cutarwa suka dawo suka kafa tantina tare da tafiya neman ruwan sallah, tafiyarsu keda wuya Gimbiya Najmah ta shiga tantinsu ta kwanta bacci me dadi ya dauketa, yana zaune yana kallonta yana shafa cikinta yaji wani qugi yana tasowa ta qarqashin qasa ya zabura ya miqe tare da zare takobinsa ya tsaya yana jiran tsammani._Assalamu alaikum_
_Masoyan wannan lbr na *MASARAUTAR MAYU* da suke amfani da Facebook amma basa WhatsApp Kuma zaku iya samuna ta account dina na Facebook kamar haka._
Username
👇
Fauzat Tasi'uPlease ki tabbatar kin/ka shirya turo kudinka kafin kiyimin mgn, kada ki manta katin MTN na dari biyu ne zaki/ka turo nayi add naki/ka a group dina, na gode.
# *UMMUH HAIRAN*
![](https://img.wattpad.com/cover/237332698-288-kdf95e1.jpg)