*MASARAUTAR MAYU*
*UMMUH HAIRAN*
*PAID BOOK*
_Gareku masoyana inason nasan kunasona tayayan zan amince da abinda bakunanku ke furtawa?_
_Karki damu kedai kiyi qoqarin nunamin qauna ta hanyar siyan littafina_
_Regular 200 VIP 500_
_Ki biya ta wannan acc din 0255526235 Fauziyya Tasi'u Umar GTB_
_Idan katine ki dauka hotonsa ko pin lambobinsa ki tura ta WhatsApp number 09013718241: idan VTU ne ki tura ta wannan number_
👇🏻
_09031307566_MM 17-18 Lamar Yarima Isham da Aljana Nurayyah kuwa lkcn da Nurayyah ta gama fada masa dalilinta nason zuwa fadar Fazbar, sai tayi want surkullenta wani maridin aljani ya bayyana gabanta ta dubesa tace “a cikin sa'o'i sittin nakeso ka isa masarautar Fazbar.
Sujjada yayi mata daidai lkcn da shima Yarima Isham ya kira nasa aljanin yazo suka dunguma sararin samaniya basa tsayawa sai idan sun kasance suna buqatar wani abu cikin saa kuwa basu samu wata matsala ba saboda saida suka daure dazukan kafin tahowarsu haka suka rinqa keda dazuzzuka sa kwazazzabai wani lkcn da alqaryu,
Suna tafe ne suna tsara yanda zasuyi su sace Gimbiya Najmah inda qasan zuciyarta Nurayyah take shirya yanda zata kashe Isham ta mallaki Najmah ita kadai wanda takeda tabbacin ita hanyarta ne kawai zata samu damar mallakar zuciyar Yarimah Nurain.A lkcn da sukaci rabin tafiyar sai ya kasance hanya ta kwace musu dole saida suka sauka a cikin wani daji me yawan bishiyu da dogayen tsaunuka suka nemi bakin wata qorama suka sauka suna ganin ruwan suka nufeshi da sauri saboda qishirwar da sukeji sukasha suka wanke jikinsu suka koma sukayi shimfida kowane ya kishingida domin hutawa, ashe Basu sani ba shi wannan guri da suka kwanta qasansa idan wani maciji ne da ya safe shekaru dari takwas a gurin ya kasance girman yayi girman tsaunin Uliyal khaulah wanda ya kasance shi kadai da matarsa suke rayuwa a wannan daji babu wani mahaluqi da yake ratsowa cikinsa ya fita lfy face sun massheshi gawa.
Koda Yarimah Isham yayi arba da wannan maciji wanda girman kansa ma kadai abin sanya zuciya cikin wasu wasine, sai ya zabura ya miqe ya zare takobinsa itama Aljana nurayyah hakan tayi sukaja da baya cikin halin tsoro saboda iyakar bincikenta data shafe shekaru tanayi Bai taba nuna Mata zata hadu da wata matsala a hanyarta ta zuwa fadar Fazbar ba, wata iska sukaji ta taso cikin wani matsanancin yanayi Mai dauke da wata baqar qura take dajin yayi duhu bishiyu suka rinqa karyewa tare da wani sauti mara dadin sauraro, haka suka wanzu a gurin suna masu toshe kunnuwansu saboda tsab wannan sautin zai iya kurmantar da mutum,
Sun shafe tsayin sa'o'i sannu a hankali iskar raguwa har ya kasance ta tsaya cak suka bude idanuwansu kawai sai sukaga dajin ya zama fili fetal aikuwa suka zabura suka miqe cikin mamakin wannan aiki na sihiri kawai saijinsu sukayi a cikin sarqa an dauresu akayi sama dasu can qololuwa sannan aka sakesu sukayo qasa cikin wani mawuyacin hali kafin su gama direwa Yarimah Isham ya baza wata tabarmar tsafi suka fado kanta suka abin mamaki kafin su miqe wannan jibgegen maciji yayi wata kururuwa yayo kansu baki bude.Cikin zafin nama Yarimah Isham ya miqe shima yayi wani gunji kawai sai ya zama macijin turus wannan maciji yaja ya tsaya suna kallon kallo lamarin daya fusata wannan macijin yayi tsalle da nufin fadawa kan Isham amma sai Isham ya goce ya fadi qasa tim cikin saa Isham ya caka masa wata yar qaramar wuqa a tsakiyar cikinsa take yayi wata haniniya ya saki kururuwa me gunji data sanya kwazazzabai suka rinqa ruftawa jini ya rinqa ambaliya Amma duk da haka bai risina ba Saida ya kaiwa Yarimah Isham raruma ya yankeshi da manyan haqoransa take naman gurin ya zagwanye ya zamana ya narke cikin tsananin azabs Yarimah Isham yayi baya taga taga zai fadi nan take Aljana Nurayyah ta kawo masa agaji ta hanyar kafa tsinin takobinta a tsakiyar kan macijin yayi gunji yayi gunji ya fadi gefe Tim yana matagugu,
Abinda yabawa Aljana Nurayyah damar sabar Yarimah Isham ta azashi bisa aljanin daya daukoshi suka bar dajin tare da wannan maciji da yaketa kururuwa, bude wata jaka dake rataye a wuyanta tayi ta dauko wani garin magani ta bude inda wannan maciji ya sari Yarimah Isham taga yanda dafin macijin yasa jikin Yarimah Isham yayi baqin qirin, da sauri ta zazzaga masa maganin ta lullubeshi da wani bargo sihiri data samar dashi a lkcn na tsayin saa guda sannan ta budeshi.Tana budeshi ya miqe zaune yana rarraba ido ta kece da dariya tace “haqiqa Kai sadaukine duk da kasancewar wani lkcn jarumta bata qwatar rai daga hannun masheqi Amma hikima takan zama mafita a lkcn da aka tsinci Kai cikin gararin fadawa Wani Qangi me wuyar kaucewa.
Numfashi ya sauke ya dauki battar ruwansa ya bude ya kwankwada ya zubawa hanya ido sukaci gaba da lulawa cikin gajimare batare da kowa yace da kowa komai ba zuciyar Yarimah Isham tana gurin Gimbiya Najmah wacce ya jarabtu da tsananin qaunarta gashi tana neman yimasa nisa tabbas yazama wajibi a gareshi ya sare kan Yarimah Nurain domin tabbatar da cikar izzarsa, ya zama doke ya dawo da Najmah cikin rayuwarsa ya zama dole ya sanya zoben Zaujatul Noor a yatsansa domin samun damar mallakar daular Askan wacce ta kasance itace babbar daular aljanu a wannan lkcn wacce take qarqashin jagoranci Sarauniya Badiyyah wacce a yanzu duk aljanin da yake musulmi to qarqashin iko da buwayar mulkinta yake.
Itakuwa Nurayyah babban burinta a duniya rayuwa da Yarimah Nurain Koda kuwa bazai sota ba tanason cika burinta da alqawarin da tayiwa Mahaifiyarta Bokanya Juhaira na kasancewa dashi tare da karya masa tsaronsa ta hanyar aikata Zina da ita wadda ita dayace hanyar da zata samu damar aiwatar da qudurinta na kashe Najmah ya kasance ta dawo da matsayinta na baya na zamowa Sarauniyar kyawawan duniya ta wannan qarni da samuwar Najmah yasa aka daina zancenta idon duniya ya tashi daga kanta ya koma kan Najmah ya kasance duk wani me qarfin iko da fada aji a duniya burinsa ya mallaki sirrin Nasarar dake jikin Najmah da kuma kwatar zoben Zaujatul Noor da yake hannunta a halin yanzu wanda takeda ittifaqin Najmah batama san amfaninsa gareta ba ita dai kawai ta daukeshi adone a gareta.***********
Bangaren Boka Rundatu kuwa tunda ya baro kogon dutsen qursu da yake rayuwa a ciki yaketa buga saarsa amma ya kasa samun damar ganin halin da Najmah take ciki har sai daren cikar Zoben Zaujatul Noor sannan ya samu nasarar yayewar hijjabi tsakaninsu ya hangeta kwance tana bacci dakarun aljanu musulmai dubu hamsin suna gadin ta ta sama da qasa gabas da yamma kudu da arewa.
Yaga lkcn da Sarauniya Badiyyah ta tashi yaga lkcn da aka aiko Mata saqo amma baiji meye aka fada Mata ba yagadai ta tashi ta fito ta nufi dakin da Najmah ke bacci yaga sanda ta tasheta yaga sunyi mgn nan ma baiji maye suka tattauna ba, yaga sanda taja Hannu Najmah suka fito a lkcn yaso aikawa a satota amma aljanin da zai tura yace a wannan daren babu wanda ya isa ya ratsa birnin Faris gabadayansa balle ya samu damar shiga masarautar Fazbar.
Haka dole ya hqr yaci gaba da kallon yanda abubuwa suke kasancewa har zuwa lkcn da suka shiga ga Yarimah Nurain yaga lkcn da Nurain yaja Najmah ya rungumeta tare da sumbatarta har zuwa lkcn da Sarauniya Badiyyah ta juya ta fita kawo lkcn da Yarimah Nurain ya daga Najmah ya nufi turakarsa da ita daga wannan bai qara samun damar ganin komai ba.Hakanan yayita bugawa tunda yasan qarshen mgnr a yau Yarimah Nurain zai tara da Najmah wanda hakan na nufin ya mallaki wannan sirrin nasarar dake jikinta rikicin zai kons tsakaninsu dashi tunda zai kasance yanzu shine me juya kowa da komai hakan na nufin karyewar daulolin tsafi, faruwar fari da karyewar tattalin arzikin qasashen da suka kasance kafurai masu bautawa addinin tsafi da addinin gargajiya.
A lkcn da yaketa wannan qoqarin na hana shigar wani Abu tsakanin Yarimah Nurain da Najmah a daidai lkcn ne yaji wata siririyar murya ta saki qara tare da kabbara gami da mamayewar wani haske daya mamaye duniya gabadayanta wannan lkcn duk wani matsafi dake rayuwa a doron qasa Saida ya zabura ya miqe tsaye miqewar da suka kasa komawa su kwanta kasancewar sun dade da sanin wannan haske abinda yake nufi.
Wani ihu Boka Rundatu ya taqarqare ya fasa wanda ya sanya aljanin dake sauke dashi direwa a saman tsibirin Uliyal khaulah dake tsakiyar teku saukowa Boka Rundatu yayi ya fadi a qasa ya rinqa birgima yana ihu shikenan ta faru ta qare Nurain yasan Najmah ya mace shirinsa na shekara sama da dari ya rushe kaico da wannan mummunar tabewa da asara da yayi,
Miqewa yayi ya shige cikin wani kogo da yasa aljanu suks samar masa cikin kwana uku ya baje kayan tsafinsa ya matsa jikin wutar sihirinsa ya dauki tsawirar zanen halittar Najmah ya dora saman wutar ya dauki wani ruwa ya zuba samanta ya fara karanto wasu siddabarunsa tsayin lkc sannan wata aljana ta bayyana ya dubeta yace “ki kasance tare da wannan taswirar domin samun damar cikar burinki na duniya, fadin haka keda wuya wannan aljana ta shige jikin wannan taswira take saiga Najmah ta tashi, Boka Rundatu ya sheqe da dariya yana cewa “nasara! Nasara!! Tabbas nasara tawace zan yaqesu dake".......*UMMUH HAIRAN*