*MASARAUTAR MAYU!*
*_(HISTORICAL AND ADVENTURE)_**WRITING AND STORY*
*UMMUH HAIRAN*
LAST FREE PAGE
FREE *P 13-14*
TUNISIA Lamari ne me wuyar ganewa rayuwa me cike da tarnaqi ita take gudana a fadar boka Rundatu tsakaninsa da Uddatu mahaifin Najmah da Uddaru, al'amura sun jagule duk yanda yake suke tunanin sauqi abin ya faskara alqaluman tsafi sun kasa tasirin hango musu halin da Najmah take ciki dukkannin bala'insu yana tsayawa ne a bayan Dutsen Najalal Irdah.
Sosai yake azabtar da Maharbi Uddatu da Uddaru a cewarsa suna sane suka bayar da cikon nasararsa wa Yarimah Nurain kullum yake sawa anayi musu azaba kala ashirin da biyar duk da haka Uddatu yaqi cewa komai Abu daya take maimaitawa cewa “haqiqa na kasance Mai biyayya wa umarninka nida yata da matata bamu kasance masu bijire maka ba saidai kai ka kasance ka bamu umarni wajen zuwan Najmah bikin Jawaleey wanda har ya zamo silar salwantar muraden manyan matsafan duniya"
Saboda baqin ciki saida Rundatu ya kwana guda yana kukan jini tare da kebe kansa cikin wani dakin sirri ya rinqa hada surrukan da yake tsammanin zasu kaishi ga nasara.Duk bugun da zaiyi saidai ta hango masa dishin hoton Najmah cikin halin suma shima hoton baya fita gabaki daya saidai wani bangare nashi lamarin daya qara dugunzuma hankalinsa ya fito da shirinsa, tsakiyar dare ya dauki wani qaho ya fara busawa take ginin koton ya fara girgiza yana daddarewa cikin daqiqa sittin wani shirgegen aljani ya bayyana a gabansa yayi sujjadah.
Munin aljanin ne yasanya Uddaru sulalewa ta suma shikuwa Uddatu fitsari ya rinqa saki a wando, boka Rundatu ya kece da wata mahaukaciyar dariya data sanya tsuntsayen dake saman bishiyoyi yin fiffike su tashi yace “na hango matsafiya Nurayyah ta hada hannu da Yarimah Isham zasu dauki hanyar zuwa Qasar Farisa a nufinsu na isa fadar Fazbar haqiqa yaro da goruba sai lasa domin Bokaya Juhaira ta kwana uku a bakin birnin tare da shugaban maridan duniya Marisol suna jiran ranar da Yarimah Nurain zai fito kilisa da Najmah wanda ta wannan hanyar ce kawai zasu samu damar karbarta,
Yakai wannan babban hadimi nawa inaso kayi gaggawar daukata ka kaini tsuburin Uliyal khaulah ni anan zan jirayi zuwansu zan tsaya ne duk wanda ya samu nasara saina kasheshi na karbeta daga hannunsa idan naso na kasheta bayan na cire zoben zaujatul Noor daga yatsanta idan Kuma naga dama na barta na massheta sadakata"Saurin kallonsa Uddatu yayi ya zagayeshi tare da sanya wata yar qaramar wuqa ya caki qirjinsa jini ya zubo ya sanya wani qoqo ya tare bai damu da ihun da Uddatu yakeyi ba ya matsa gaban Uddaru itama ya caki qirjinta jinin yayi tsartuwa ya tara ya cakuda dana mijinta ya matsa gaban wata wutar tsafi da takeci balbal ya dora wannan qoqon ya dauki wani ruwan sihiri ya zuba a ciki jinin yayi tsiri yayi tsiri ya koma cikin qoqon take wani wari ya turnuqe gurin.
Wani baqin duhu ya gauraye ko Ina tare da wani kuka me kama dana mage, wani gurnani ne ya rinqa tashi take wani haske ya kewaye gurin abin mamaki kawai sai sukaga wata budurwa ta taso daga cikin qoqon nan me tsananin kama da Najmah da sauri Uddatu ya washe baki yana cewa “yata ta dawo garen...."
Rufe masa baki Uddaru data farfado tayi tace “ba ita bace tabbas wannan kofi din yatace ba yata bace" dariya boka Rundatu ya kece da ita yace “da ita zan yaudaresu na kwace ta gaskiyar" yana fadin haka ya dafe bayan wannan aljani me manyan fuka-fukai take aljanin yayi wani shawagi ya cure guri guda ya zama qura ya keta kogon dutsen ta fita a guje.
Lamarin daya sanya duk wata halitta dake gurin durqushewa har saida rugugin da qurar ta haddasa ya lafa sannan komai ya koma tafiya daidai.********
Acan kuwa fadar Fazbar lkcn da Najmah ta yanke jiki ta dadi cikin wani mawuyacin yanayi a daidai lkcn ne Sarauniya Badiyyah ta umarci Yarimah Nurain daya tashi yaje yagano lfyr matarsa, yana zuwa ya tarar da ita cikin wannan mawuyacin halin da sauri ya matsa ya sanya hannayensa ya dagata cak ya dorata saman gadon tare da zuba mata ido yana nazarinta.
Murmushi yayi tare da sanya hannunsa ya fara shafa kanta dogon kwantacce gashinta daya kwanto har saman girarta ya dauki hankalinsa, sosai ya shagala da kallonta yanajin shauqi da haka shima ya zame ya kwanta a gefenta yana hura mata iska a fuskarta har bacci ya daukeshi,
Zuciyarsa wasai yanada yaqinin cewa idan ta farka bazata tuna komai ba balle tabashi matsala wajen cikar muradansa tabbas shi ya kasance me saa cikin rayuwarsa, tsayin wannan rana haka suka yini suna baccin gajiya yana rungume da ita a faffadan qirjinsa.
Qiraye kirayen sallah ne ya tasheshi ya zame jikinsa daga nata a hankali yaja Mata bargo ya rufeta tare da sumbatar dan qaramin bakinta ya fice da sauri ya turo Hadima Ishmiyya yace taje tayi gadin gimbiya hakanan Najmah ta kasance cikin dogon bacci me kama da suma na tsayin kwana da yini inda a cikin gdan sarautar aketa shagalin biki babu amarya, kasancewar Yarimah Nurain ya sanar da iyayensa tana cikin halin baccin fitar sihiri a jikinta ya sa basu wani damu ba saidai suje su leqata su dawo.
