*MASARAUTAR MAYU!*
*_(HISTORICAL AND ADVENTURE)_**WRITING AND STORY*
*UMMUH HAIRAN*
*MARUBUCIYAR*
👇🏻
AMINIYA KO KISHIYA
HABIBULLAH
QUEEN FARHA
GIDAN UNCLE
ADANDI
WACECE NI
AURAN BAZAWARA
DHOOM ISHAQ
MATAR LAMEER
DUBAI
AND NOW👇🏻
MASARAUTAR MAYU!
AND
WANK QANGIFREE *P 11-12*
**********
BIRNIN JAWAL
Tsayin sa'a guda ana jiran fitowar baiwa Zaujar da Najmah Shiru babu labarinsu lamarin daya tashi hankali Yarimah Isham ya tashi wani amintaccen bafade yace yaje turakarsa ya gane masa meye yake faruwa, fita bafaden yayi ya nufi fadar Yarimah Isham din Koda zuwansa sai ya hangi qofar fadar a bude mamaki ya cikashi ya cusa kai ciki cikin tsananin mamaki da tunanin abinda yake faruwa,
Shigarsa keda wuya ya iske baiwa Zaujar kwance cikin halin suma al'amarin daya tashi hankalinsa ya juya da gudu ya koma dandalin taron ya fadi gaban Yarimah Isham yace “ka gafarceni yakai Yariman duniya haqiqa wani al'amari ya faru domin kuwa naje na tarar da baiwa Zaujar cikin halin Suma a daure da sarqar al'amudi,
Wata zabura manya fadawan dashi kansa sarki Jamal din sukayi kowa ya Kai dubansa ga shugaban bokaye Irdam shikuma a lkcn aka qara masa qaimi da qumajin aikinsa yayi wata kururuwa saiga sama ta bude tsuntsu Dilshad ya bayyana bayansa dauke da Najmah kafin su gama mamakin yanda akayi wannan tsuntsu ya ratso masarautarsu ya keta ta babbar fadar tsafi ya shiga turakarsa Yarimah Isham ya dauke Najmah kawai sai sukaji sukuwar dawakai tare da kabbara.Take sadaukai suka shata layi kasancewar su dama sun kasance kullum cikin Shirin ko ta kwana suke take suka gyara tsaiwa wasunsu Kuma suka fara ruwan kibbau wa wannan tsuntsu tare da tashin tsuntsayen tsafinsu sukafi bayanshi abin mamaki yana keta hazo ya bacewa ganin nasu tsuntsayen.
Kafin isowar Yarimah Nurain yarimah Isham yayi wani ihu ya suke zuciyar wannan bawan daya tura ya gano masa meye yake faruwa take bawan ya fadi gawa ya daga takobin ya lashe jinin jikinsa na wata irin karkarwa kamar ana kada masa kugen yaqi ya fito filin cikin tsananin tashin hankali sadaukansa suka rufa masa baya wani mahaukacin yaqi ya ruguntsume qura tayi tsiri ta tashi sama ta lullube mayaqan baka iya hangen komai sai tartsatsin wuta cikin qura da haniniyar dawakai da ihun mazaje wani bangaren kuma kabbarar dakarun musulumci kawai ke tashi.
Gumurzu yayi gumurzu sai zubewa maza sukeyi amma zuciyoyinsu sun kasa rusuna kowa burinsa yaga yakai abokin karawarsa qasa, duk yanda yarima Isham yaso yakai ga isa wa Yarimah Nurain yayi masa kisan sauro amma ya kasa saboda yaqin na sumamene basu shirya masa ba kuma kada ma sun shirya fada da jarumi Nurain sai dubu ta taru.Tabargaza dakarun rundunar mayaqan Yarimah Nurain sukeyi bata wasaba Saida ya kasance sun zubar da kashi sittin cikin dari na sadaukar masarautar jawal inda Suma aka zubar musu da sadaukai da dama amma basukai kwatan wanda suka kwantarwa da Yarimah Isham ba.
Abinda ya qara harzuqa zuciyar Yarimah Isham yayi wani ihu daya sanya birnin karbar amon muryarsa ya rikide ya zama wani haske ya rinqa zagayawa a tsakanin dakarun musulumci duk inda ya zaga Saida kaga gawarwaki na zubewa a qasa kamar sassabar gona aikuwa shima Yarimah Nurain ya taqarqare ya runtuma uwar kabbara ya diro dagakan dokinsa ya shafi dokin ya bace bat ya zare zare takobin muzhar takobin da kakansa sarki Uqdah mahaifin Sarauniya Badiyyah ya yaqi tawagar aljani Baghzar a zamanin sa ya ci gaba da maimata kabbara da kalimatusshahada ya keta cikin hasken ya rinqa saran hasken babuji babu gani,
Wani irin tururi ina narkakkiyar dalma yana ratsa Yarimah Isham take ba tare da shawara da kowaba wannan hasken ya bace ya fadi qasa Tim Yarimah Nurain ya nufeshi kafin ya Isa gareshi ya miqe ya nufoshi suka ruguntsume da wani azabbaben yaqi wanda ya haddasa qasa ta rinqa girgiza kowannensu yanaji da zafin nama da sadaukanta.Wannan yaqi shine ya daukesu har tsayin kwanaki biyu babuci babusha babu sallah ga musulmai har saida suka barnata rundunar mayaqan ta masarautar jawal sannan Yarimah Isham yayi muguwar galabaita a matsayinsa na bil'adam shikuwa Nurain ko a jikinsa in zaa shekara ana yaqin baijin komai.
Gumu tayi gumu har takai Yarimah Isham ya fara gani dishi dishi ga raunukan da Yarimah Nurain yayi masa da suketa malalar da jini, yanagaf da faduwa wata iska ta taso me qarfin gaske ta rinqa zubar da duwatsu tana kakkarya bishiyoyi ta dauke Yarimah Isham tayi sama dashi abinda ya kawo qarshen wannan yaqin a karon farko.
Nan take mutanen dake cikin masarautar suka rinqa guduwa suna shigewa gidanjensu suna kullewa abinda ya sanya Yarimah Nurain bada umarnin a debe gawarwakin musulmu suje bayan gari suyi musu sallah su binne, haka kuwa akayi nan take dakarun suka rinqa debe gawarwakin suna dorawa bisa dawakai shikuma ya hau kan nasa dokin ya nufi inda aka kwatanta masa gidan iyayen Najmah domin ya daukosu ya tafi dasu masarautar Fazbar amma bisa rashin saa yaje ya tarar da gidan a rushe babu alamun an taba halittar gda a gurin saima wata baqar qasa data maye gurbin gidan.