MASARAUTAR MAYU

830 13 2
                                    

       *MASARAUTAR MAYU*
*_HISTORICAL AND ADVENTURE_*

*WRITING AND STORY*

*UMMUH HAIRAN*

*MARUBUCIYAR*
           👇🏻
AMINIYA KO KISHIYA
HABIBULLAH
QUEEN FARHA
GIDAN UNCLE
ADANDI
WACECE NI
AURAN BAZAWARA
DHOOM ISHAQ
MATAR LAMEER
DUBAI
AND NOW👇🏻
MASARAUTAR MAYU!

Free *P 9-10*

Qasa Najmah tayi da kanta cikin yanayin mamakin wannan sarqaqqen qulli daya qulle zuciyarta tanaji tana gani aka zaunar da ita saman wasu kujeru guda biyu da aka qawatasu da kwalliyar dutsen lu'ulu'u  da jauhar dubanta Yarimah Nurain yakeyi sosai ta dago idonta cikin alqabbar dake lullube da fuskarta suka hada ido yayi saurin dauke idonsa tare da dora hannunsa saman wani tire na gold ya dauki wani siririn zobe da yaketa walwali da daukar ido ya sunkuya a gaban Najmah ya zura hannunsa ya kamo hannunta ya lumshe idonsa daidai lkcn da fadar ta dauki wani shiru,
Yatsanta ya kama ya zura Mata zoben tare da Kama hannunta nata sosai cikin nasa yanajin dumin jikinta na saukar masa da wata kasala ya janyo hannunta daidai fuskarsa ya dora hannunsa nata a goshinsa, fadar ta dauki wani ihu suna fadin “Allahu Akbar shagali Jama'a musha lemo muci dabino mu some raquma yau yariman mu ya zama angon gimbiya Najmah" wasu hawayene suka zubo mata batasan sanda ya janye hannunsa daga nataba ya koma ya zauna wani dattijo ya shigo shima da yan bidi'arsa a bayansa ya gurfana gabanta ya ajiye wani qaton tire ya fara wasu addu'o'i na tsayin wani lkc kafin ya zana qasar ya dago ya kalli Yarimah Nurain yace “haqiqa wannan auren akwai albarka a cikinsa harda rabo Amma akwai rikici me yawa da zai biyo bayan kammaluwar komai"


Jinjina masa hannu yayi  ya miqe ya fice hakadai mutane kala² sukayita shigowa kowa yana nasa surkullen a cewar Najmah ya fita Sarauniya Badiyyah ta miqe ta qaraso inda Najmah ke zaune ta kamota tace “atashi daga taro gimbiya ta gaji tana buqatar hutu"
Tana gama fadin haka ta kamo Najmah ta miqar da ita ta nufi wata hanya da ita ashe bangarenta Sarauniyar Badiyyah ne,  basu tsaya ba saida suka dangana da wata babbar fada Sarauniya Badiyyah taja ta tsaya daidai lkcn da barorin suks rinqa zubewa a gabanta ta dubi wata amintacciya daga cikinsu tace.
“Ki Kai gimbiya wancan dakin da aka tanada dominta ina buqatar ta huta sannan ta kasance cikin tsaron Allah kafin lkcn da zaa gama shagalin biki a miqata ga mijinta" Kama hannunta wannan baiwa tayi ta nufi wata qofa ta bude suka shiga nan din ma wani bangare ne abin kallo da qawa an qawatashi da duk wani qyale-qyalen zamani da duk wani Abu na more rayuwa da jin dadinta, gwauron numfashi Najmah ta sauke ganin yanda wasu kyawawan yammata suketa bayyana duk inda ta juya,
Zagayesu sukayi suna wata irin waqa me ratsa jiki a haka suka rakata wani daki suka tsaya a bakin qofar ita da wannan amintacciyar baiwar ga mamakinta sai taga wannan baiwar ta zube a gabanta tace “ranki ya dade sunana Ishmiyya na kasance baiwa a wannan masarauta Kuma daya daga cikin amintattun bayin da Sarauniya ta zaba domin kasancewa tare dake da baki kulawa shin ko kina buqatar wani abu?"


Lumshe idonta tayi ta budesu akan Baiwa Ishmiyya tace “ina buqatar sanin abubuwa da yawa game da wannan masarautar da kuma dalilin da yasa Yarinmanku yake boye fuskarsa sannan da dalilin da yasa aka satoni aka kawoni cikinta shin wanne addini kukeyi Kuma wanene ubangijin Annabi Sulaimanu Dan Dawud da naji kuna yawan ambata a cikin wannan masarauta?"
Qasa wannan baiwa tai da kanta tace “ki gafarceni ya shugabata cikin tambayoyinki biyu kawai nake da ikon baki amsa sauran kuwa bakida me baki amsa face mijinki shugabana Yarimah Nurain" da sauri ta sake cewa “mun kasance munayin aure ne idan abin bauta Harsan ya amince ganyen suturar mace ya fadi a gaban mijin da ya zabs Mata sannan ne zaa kaisu yasa musu albarka daga haka sai su fara zaman aure to ku ya naku auren yake kasancewa albarkar wa kuke nema a cikin aurenku?"
Murmushi baiwa ishmiyya tayi a ranta tace “kafuri kafuri ne dama akwai wani abin halitta da zaka nemi albarkarsa da sahalewar sa cikin al'amuran rayuwarka?" Amma a fili sai tace “insha Allah zan baki wanna amsar Amma da farko ana buqatar kiyi wanka ki sha madara sai mu zauna nayi miki bayanin abinda kikeso ki sani ya shugabata"


MASARAUTAR MAYUWhere stories live. Discover now