6

540 72 14
                                    

"Da fatan kin samu natsuwa yanzu Baby, kin dai ji abunda Umma tace,ki qara haquri, sannan kiyi ta mata addu'a da fatan alheri"

Ina kwance akan cinyar Maheer, yana shafa gashi na yana fa'din haka, ni kam murmushi kawai nake yi, yanzun muka gama waya da Umma take shaida mana Kaka Habu Qanin Mahaifin Abba ya nemi da su zo Zaria ita da Abba yana son ganin su, fata na dai Allah yasa ya daidaita mun mahaifa na, dago kai nayi na kalla kyakkyawar fuskan Maheer tare da fa'din

"Nagode da kulawar ka a gare ni"

Qwanqwasa qofa mukaji anayi, tashi yayi dan yaje ya ga suwaye, muryoyin qanne na da qawaye na naji, kafin Maheer ya dawo cikin 'daki har na kai bakin qofar 'dakin, murmushi nake ta musu dan naji da'din ganin su, Hafsah ce ta fara cewa

"A kwana a hantse Amarya, na ga har kin qara haske ne"

Nan dai su kai ta tsokana na, da Maheer ya ga abun ba na qarewa bane yace ze je wurin abokin shi Umar ya dawo, raka shi nayi har bakin qofa ina ta shagwaba, rungume ni yayi tare da yi mun peck a goshi, nan qawaye na suka cigaba da tsokanan mu

**** Maheer be dawo ba se gab da magariba, bayan munyi Sallah Maheer yace ze maida su gida da kanshi, nima na dage akan se na raka shi, muna cikin haka Umar yazo, nan ko yace ya hutar da shi ya zauna tare dani shi ze kai su gida, Sallama nayi masu muka koma cikin gida ni da Maheer, bayan mun zauna ne yake shaida mun sunyi waya da Umma ta har ta ce mai jibi zasu dawo Kaduna Inn Sha Allah, da'di naji a zuciya ta saboda nayi dacen miji me kula da ni sannan kuma me damuwa da matsala ta, abincin da ya anso daga gidan su muka ci, bayan mun gama mukayi sallah sannan muka 'danyi kallo, can da ya ga alamun barci ya fara kwashe ni ya ce mu tashi mu shiga daki.

_______________________________
Wasa wasa abun ba wuya yau har munyi wata  10 da aure ni da Maheer, ansa ranar auren Fadeelah qanwar Maheer da abokin shi Umar, Umma ta kuma tuni ta dade da komawa gidan Abba na, komai ya zama dai dai, se dai 'dan sabanin da baza'a rasa ba tsakani na da Maheer wanda dama dole ne in dai zaman aure ne, ina nan ina zuwa makaranta dan a yanzu ma na kusa kammalawa.

Ina cikin shiryawa zanje gidan su Maheer in gaida Umma daga nan in biya gidan mu se naji sallamar Haajarah, parlor na fito na same ta, bayan mun gama gaisawa take sanar dani ita ma an sa ranar auren ta nan da wata uku masu zuwa, nan ta fara tsokana ta tana cewa

"Besty qila ma bazaki zo aure na ba dan nasan lokacin qila ma kinyi nauyi"

Murmushi na fara yi sannan nace

"ke ni wallahi ban da komai"

"Aiko ya kamata kiyi sauri ki samo mun yaro ko yarinya ta"

Kafin in amsa mata mu kaji muryar Maheer yana fa'din

"Gaya mata dai, nima na ji har yanzu shiru"

Cikin mamaki nace

"Laa habibi dama ka dawo"

"Eh na dawo" kawai ya ansa da shi

Ta'be baki nayi kawai, se na yi tunanin qila an bata mai rai ne a waje, Suna gama gaisawa da Hajarah ya shige 'dakin shi, bin shi nayi cikin 'dakin, samun shi nayi yana qoqarin cire buttons 'din rigar shi, zuwa nayi gaban shi dan in taya shi cirewa, ina saka hannu na ya cire nashi ya bari in cire mai buttons 'din, kai na na 'daga na kalle shi sannan nace

"Baby ya na ga ranka a bace kamar anyi maka wani abu"

Girgiza kai yayi sannan yace

"A'a ba abunda aka mun me kika gani?"

"Na ga kamar baka cikin jinda'di ne, yanzu dai kayi wanka se in baka abincin ka, tin da ka dawo ma ai se muje gidan su maman tare ko"

"Alright my love"

Fita nayi na samu Hajarah, gani nayi tana qoqarin yafa gyalen ta

"Ha'a lafia ke kuma se ina?"

Miqewa tayi tare da fa'din

"Ahmad yazo ne muna sauri, akwai inda zamu, dama shi ya kawo ni ya gangara qasan layin ku ne gidan wani Friend 'dinshi"

Kallon ta nayi tare da fa'din

"Iyyee jinda'di our latest couple in town, to muje na raka ki"

Cewa tayi

"A'a wallahi na hutar da ke, kije ki kula da mijin ki, in ya fito ki fa'da mai na tafi"

"Toh shikenan ze ji, a gaida mun da ango"

______________________________
Gidan mu muka fara zuwa daga nan se muka je gidan su Maheer, Se da mukayi Sallahn Isha'i sannan Maheer yace in fito mu wuce, har gurin mota Mamar shi ta rako mu tana mana se da safe, har mun shiga mota se yace ma mamar shi

"Yauwa Mama gobe zamu je asibiti Inn Sha Allah"

Matsowa kusa da motar tayi tare da fa'din

"Waye ba lafia?"

Ni kam bance komai ba saboda a iya sani na lafia qalau muke dukan mu, Maheer ne yace mata

"A'a ba rashin lafia bane, akan maganar haihuwa ce"

Wani irin kallo Mama tayi mai tare da fa'din

"Haihuwa kuma, watan ku nawa da aure da zaka fara bin likitoci kana tambayar su game da haihuwa"

Ni abun mamaki yake ta bani, dan tin da ya fara maganar nake ta kallon shi

"A'a mama ba wani abu bane kawai dai a duba lafiyan mu ne"

Yamutsa fuska mama tayi tare da cewa

"Toh Allah ya kyauta, se da safen ku, ban san hanzarin me kk yi ba"

Tana gama fa'din haka tayi shigewar ta ciki

Don't forget to vote, share and comment and  I need followers too, kindly show some love and follow me, I will follow back, you can also DM me I will reply back Inn Sha Allah, thank you for all the support, I really appreciate ❤️❤️

Dedicated to Chuchujay

Aishatu Ameerah ❤️❤️

TASNEEM 1 in TASNEEM Series✅Where stories live. Discover now