18

357 62 4
                                    

Suna fita daga 'dakin na fashe da kuka, duka su Umma a tare su ka matso kusa dani su na ta bani haquri, can dai kukan nawa ya ragu, kwantawa nayi ina ta kallon sama, Mama ce tace ma Umma

"Hajia Amina zamu tafi gida, mun bar Saheeb a wurin wata qanwa ta, anjima zamu dawo Inn Sha Allah, me za'a dafo muku?"

Umma tace

"Ayyah Allah Sarki, dan Allah kar ki damu kanki Hajia wallahi babu komai, da kin huta a gida ma ai kinyi qoqari"

Mama ta sake cewa

"A'a wannan dai kina so ki nuna mun cewa ke ka'dai kika haifi Tasneem ne"

Umma tayi murmushi sannan tace

"A'a wallahi ai kema 'yar ki ce, to a dafo duk abunda kika ga yayi"

Murmushi Mama tayi sannan tace

"Toh shikenan ba damuwa"

Matsowa Mama tayi kusa dani sannan tace

"Neem Neem, bari mu je mu dawo ko"

Murmushi nayi sannan na riqe hannun ta nace

"Toh Mama se kin dawo"

Fadeelah ma matsowa tayi ta riqe hannu na, sallama mukayi sannan nace mata ta gaida mun da Saheeb kuma anjima ta zo da shi, bayan sun tafi ne ita ma Zahrah tace zata je gida ta dawo, Umma ce ta ce ma Ummi ita ma ta bita gida taje ta huta anjima se ta dawo, su ma sallama sukayi da mu sannan su ka tafi, 'dakin ya rage daga ni se Umma, kujera ta 'dauko ta zauna kusa dani sannan ta riqe hannu na, cewa ta fara yi

"Tasneem kiyi haquri kinji, komai kika ga ya faru da bawa to muqaddari ne daga ubangiji, kiyi haquri dukkan me haquri yana tare da Allah"

Kuka na fara yi sannan nace

"Umma ta wallahi ni na bar ma Allah komai, qila zama na da Maheer ba alheri bane, Allahn da ya ha'da mu shi ya raba mu, amma Umma ba abunda yake mun zafi kamar ina ta addu'a in sama haihuwa amma har yaro na ya gama rayuwar shi a ciki na ban san da shi ba, Umma na ga samu na ga rashi, Ina ma ace nasan yana cikin jiki na, Ina ma ace lokacin da yake jiki na nasan da shi da na fa'da mai ina son shi kuma da na tayi mishi addua"

Hawayen fuska na Umma ta share mun da hijabin ta sannan tace

"Kamar yadda kika yarda Allahn da ya ha'da ki da Maheer shi ya raba ku to haka nake so ki yarda Allahn da ya baki wannan yaron da ya amsa shi ze qara baki wani, kuma ya fi ki son shi ya kuma fi ki sanin dalilin da yasa yayi haka, Haba Tasneem kar ki bani kunya nasan kina da tawakalli da imani, kuma nasan kina da juriya da haquri, To ina so ki qara a kan wanda kike da kinji Tasneem 'dita?"

Ce mata nayi

"Haka ne Umma, amma Umma akwai zafi wallahi, abun akwai zafi, ji nake yi cikin qirji na yana mun zafi"

Hawaye Umma ta fara yi sannan tace

"Na sani 'ya ta, wallahi na sani amma ki qara haquri, ke da Allah ma yake son ki, baki ga dik irin abunda Maheer ya miki ba amma har yanzu mahaifiyar shi tana son ki ba, baki ga ita Ameerah da take ta jinda'din abunda Maheer ke miki ba baki ga mahaifiyar ta tana son ki sosai ba, Ina son ki, Abban ki yana son ki, qannen ki suna son ki, To ko dan saboda mu ki daure kinji Tasneem, kiyi haquri, ki qara haquri"

Qara riqe hannun ta nayi sannan nace

"Toh Umma ta, Inn Sha Allah zanyi yadda kika ce"

Murmushi tayi sannan tace

"Allah ya baki iko, Allah ya miki albarka, shi kuma babyn ki Allah ya sa me ceton ki ne"

"Ameen" na amsa mata da shi, muna ta hirar mu se ga Nurse ta shigo, hannun ta riqe da Pad 'dayan hannun kuma drip ne, sannu tayi mun sannan tace mun ya kamata in chanja Pad 'din da ke jiki na, se a sannan na ankara cewa akwai Pad a jiki na, sannan na tuna miscarriage nayi dan haka dole in buqaci Pad, ajiyar zuciya nayi sannan Umma ta taya ni na tashi zaune, qoqarin taimaka mun Umma tayi dan muje in chanja Pad 'dina se Nurse 'din tace mata kar ta damu tayi zaman ta ita zata taya ni, toilet muka shiga ni da Nurse 'din, muna cikin bayi naji kamar muryar Abba na, Ina fitowa daga bayin na ga aiko shine, rungume shi nayi shi ma ya riqe ni, Ina son Abba na shima yana so na sosai dan duk yafi so na a cikin yaran shi, sannu ya yi ta mun, bayan na zauna yace

"Ambabyn Abba ya jin naki"

Dariyar sunan da ya kira ni nayi dan haka yake ce mun tun ina qarama kuma ina son sunan sosai, amsa mai nayi nace

"Naji sauki Abban Ambaby"

Dariya muka yi gaba 'daya sannan Umma ta ce

"Kai da baka kunyar 'yar fari"

Ce ma Umma yayi

"Wannan se ke, ni 'dan zamani ne, kalle ni da kyau ki gani"

Yana fa'din haka yana 'daga mata gira, dariyar shi mukayi ta yi sannan ya fara tambayar Umma garin ya nayi accident, Jan shi tayi suka fita waje, bayan kamar minti 15 se ga shi sun shigo, fuskar Abba a 'daure, sallama yayi mun sannan Umma ta raka shi, bayan ta dawo take gaya mun cewa Abba yayi fushi sosai sanadiyyar jin Maheer ya sake ni amma dai ta lallashe shi ya ce ba komai haka Allah ya tsara, cewa nayi

"Allah Sarki Abba na, Allah ya huci zuciyar shi"

Umma ta ce

"Ameen"

Wayar Umma ce ta fara qara, 'dauka tayi tare da yin sallama, bayan ta gama gaisawa da wanda take wayar se ta miqo mun tace mun Umar ne abokin Maheer mijin Fadeelah, amsar wayar nayi daga hannun ta, gaisawa muka yi sannan yayi mun sannu, shaida mun yayi cewa yayi tafiya ne amma yana dawowa ze zo ya gaida ni, godia nayi mai sannan mukayi sallama, se a sannan na tuno da qawata Hajarah, saurin ce ma Umma nayi

"Umma dan Allah ki kira mun Hajarah, bata san ina asibiti ba, wata qila har an kai ta ma"

Se Umma tace

"Allah sarki, hankali na ya 'dagu wallahi nima, kin san muna dawowa daga gidan bikin Ummin Ameerah ta zo ta same ni"

Wayar Hajara ta kira se taji a kashe, wayan mamar Hajarah ta kira nan take fa'da mata abunda ya faru, nan tayi ta ma Umma jaje sannan ta fa'da ma Umma ai ana hanyar kai Hajarahn Kano, da yake a can zata zauna, amma zata kira ta in suka isa ko bata same ta ba zata kira wayar 'daya daga cikin en kai amaryar se ta fa'da ma Hajarah, cewa tayi a gaida ni sannan suka yi sallama.

Tnx for supporting me with your votes, reads and comments, I really appreciate it and I love you all

Dedicated To Chuchujay

Aisha Ameerah❤️

TASNEEM 1 in TASNEEM Series✅Where stories live. Discover now