31

364 55 11
                                    

Zufa kawai nake yi ina ciza lebe, wani irin ciwon baya na ke ji kamar bayan ze tsage, cika na mur'dawa kawai yake yi, azaban da nake ji baya iya misaltuwa, na rasa me zanyi ma, kuka zanyi ko dariya ban sani ba, Nurses 'din da suke kai na gaba 'daya sun ru'de su ma, hawaye kawai suke yi saboda suna tausaya mun, ga mutuwar miji na ga azaba da nake ji, wata nurse ce tace mun

"Sannu Sannu kinji, Allah ze sauke ki lafia, na duba CM 'dinki har yanzu da saura, ki daina pushing se nace kinyi kinji"

Hannun ta na riqe na ce

"Hmmm Umhumm, washhh baya na, Allah gani gare ka, ya Allah ya Allah, Ina mama na dan Allah ki kiraa munnn ittaaa"

Kuka na qare fashewa dashi, da gudu aka je aka kira Umma ta shigo, hannu na ta riqe tana ta yi mun sannu, sannu kawai take mun tana hawaye.

Bayan na gama duk wahalar nan kuma ban haihu ba, ce ma nurses 'din nayi su bari in je waje, wadda ake ce ma Sister Sakina tace bari a kira Doctor, likitan yana zuwa yace su barni inje waje in zagaya, sannan yace in ta hawan bene ina saukowa, Umma ta riqe ni muka fita waje, muna fitowa na ga su Zahrah, Siyama, Fadeelah, Mama, Abba, Hafsah, Ummi , Ameerah duk sunyi cirko cirko, Ina fitowa suka bini suna ta yi mun sannu, Umma ke ansa su ni ko magana na kasa yi, hanyan wurin bene(stair case) muka nufa ni da Umma na dafa ta, sannu take ta yi mun, muna kaiwa wurin staircase se naji Umma tace

"Maheer anan ka tsaya"

Gaida Umma yayi sannan ya fara mun sannu, kallon shi kawai nake yi, se nishi kawai nake yi, idon shi ya cika da kwalla yana ta zare su, saman bene muke ta  hawa ni da Umma, se mun kai qarshe se mu qara sakkowa, se ciwon ya lafa mun can se inji kamar an tsikare ni, hawaye kawai nake yi ina nishi, cewa nayi

"Umma, Umma wallahi nagaji, Umma Nagode, Wai Allah, washh"

Sannu Umma take ta yi mun, wata Nurse ce tazo wurin mu tace mu dawo labour room 'din, muna komawa ciki tace ma Umma zasu yi mun Inducing wato zasu saka mun ruwan naquda, Hawaye na fara yi saboda naji ance ruwan suna da azaba, kuka kawai nake yi saboda zafin da nake ji baya misaltuwa, bayan sunyi mun inducing amma duk da haka ban haihu ba, ana nan ana ta abu 'daya.

***Wasa wasa tinda la'asar nake Labour amma har qarfe 10 na dare tayi ban haihu ba, qarshe likitan su ka yi magana da Abba yace gara kawai ayi mun operation, Na wahala sosai ban ta'ba tunani haka naquda take ba, azaba yayi azaba, jinkirtawa aka qara yi aka ce a bari a gani in qarfe 11 tayi ban haihu ba ayi mun operation 'din kawai, qarfe 11 ko tanayi aka fara shirye shiryen shiga dani theatre, dik azabar da naji ban haihu ba yanzu gashi zan qara jin wani sabon azaban, Nurse ce tazo ta ce mun zata yi mun shaving, shaving gashin qasan mara na tayi mun da wani razor 'dinsu, dik da bana barin gashi amma dai se da ta qara shaving wurin, cathether (roban fitsari) aka saka mun sannan aka shigar dani theatre room, wani siririn gado aka kwantar da ni sannan doctor ya bani wani pillow yace in taso in riqe, rungume pillow 'din nayi, ce mun yayi in duqar da baya na in lankwashe sosai, allurar tsakiyar baya yace za'a mun yace kar in motsa, cewa yayi dani in har na motsa akwai illa saboda zan iya zama paralized, hankali na a tashe yake dan jin maganar da ya gaya mun, sun gwada BP na ya hau, cewa suka yi da ba dan operation 'din ido a bude zasu yi mun ba da baza'a iya yi ba in har jinin mutum ya hau, Doctor 'din cewa yayi in kwantar da hankali na zan haihu lafiya Inn Sha Allah, lankwashe baya nayi sannan aka tsira mun alluran, ana gamawa aka samun rigar theatre aka kwantar dani, wani labule aka sa mun aka rufe inda zan dinga kallo, banji komai ba, Doctor 'din se ja na da surutu yake yi ina amsa mai, daga ganin alamu bai san nayi bacci, cewa yayi dani

"Tasneem yanzun nan zaki ga babyn ki, kin shirya gani kuwa"

"Eh" nace mishi da murya ta da ta shake saboda kuka, Adeel 'dina kawai nake tinani, da yana nan da se yafi kowa farin ciki, kukan Baby naji kawai, wani irin ajiyar zuciya nayi, Doctor yace mun

"MashaAllah, babyn ki ta iso duniya, kin samu ta mace"
sannan ya 'dago mun ita yace mun

"Kin ganta ko, fara ce sosai Tabarakallah, wannnan balarabiya ce MashaAllah"

Akan qirji na aka 'daura mun ita, hawaye suka fara zuba a ido na, MashaAllah kawai nace sannan Doctor 'din yace mun

"Wannan babu inda ta bar Doctor Adeel"

Wani abu naji ya tokare ni a qirji na, kuka na fashe da shi, haquri suka yi ta bani sannan aka tafi da babyn don a gyara ta, na kai kusan minti 30 ana kimtsani, daga nan aka fitar dani aka kaini 'dakin hutu, su Umma duk suna 'dakin suna ta 'dokin ganin baby na, sannu aka yi ta mun ana ta 'daukar babyn hoto amma duk da haka jikin kowa a sanyaye yake saboda rasuwar Adeel, fuska na na juya ina ta kallon gefe, Nurse ce ta shigo ta qara amsan baby na sannan bacci ne ya kwashe ni.

Can cikin dare na farka na ga Umma a kusa dani, daga ni se ita a cikin 'dakin, baby na kuma tana bacci a cikin gadon ta na jarirai, Umma na jin farkawata ta bu'de idon ta, ciki na ne ya naji yana ta mur'dawa ya qulle yana ta mun ciwo, salati kawai nake yi Umma tana yi mun sannun, kiran Nurse taje tayi se Nurse 'din da tazo ta fa'da mata ai yana faruwa, wai kayan ciki na ne suke komawa inda suke, ce mata tayi ko da haihuwa nayi da kai na se nayi haka sannan tace kar Umma ta damu zan daina, zafi kawai nake ji Ina ta addua a zuciya ta.

😭😭😭Ni kai na da nake rubuta Page 'dinnan ba da'di nake ji ba, Tasneem tayi matuqar bani tausayi, Allah ubangiji ya bata lafiya, ya raya abunda ta haifa sannan ya ji qan mijin ta.

Allah ubangiji ya saka ma iyayen mu da alheri ya basu gidan aljanna firdausi, it's not easy to be a mother.

Allah ya bamu haihuwa da sauqi, ya sauki masu ciki lafiya.

Dedicated To Chuchujay

Ameerah Aisha❤️❤️

TASNEEM 1 in TASNEEM Series✅Where stories live. Discover now