36

341 50 20
                                    

Daga bayi na fito bayan na idar da wanka na 'daura alwala, sallar isha'i nayi sannan na karanta qur'ani, bayan na gama na duba waya ta na ga Jabeer yayi mun message cewa nan da minti 30 ze zo, doguwar rigar atamfa na 'dauko na sa, atamfan milk colour ne tana da flowers brown a jikin ta, hijabi brown na 'dakko na aje akan gado, under wears 'dina na saka sannan na sa doguwar rigar, turare na fesa ka'dan saboda bana so aji shi, powder ka'dai da kwalli da lipstick na shafa a fuska na, 'dan kunne da agogo na saka, sannan na chaje gashi na na sa ribbon na 'daura dankwali na, Ina cikin shiri na Noorie ta shigo 'dakin tana cewa

"Mami! Mami! jo ci ga shofia tayi shabon qawa (Mami! Mami! Zo ki ga Sofia tayi sabuwar qawa)"

Hannu na ta fara ja alamun inzo muje, cewa nayi da ita

"Tsaya tsaya Bibinuyi, shiryawa nake yi"

Cigaba tayi da ja na, da na ga ta matsu se na tsayar da ita na duqa na 'dafa ta nace

"Sofia The First ce tayi sabuwar qawa?"

Gya'da mun kai tayi, hannun ta ta sa a baki ta fara sha, cire mata hannun nayi a baki nace

"Stop it, ba na hana shan hannu ba? "

"Eh" tace

Sannan ta aje hannun nata, qara gyarawa nayi sannan na 'dauki waya ta da hijabi na, takalmi na sa sannan nace mata mu je in gani, muna kaiwa bakin qofa ta saki hannu na ta ruga da gudu ta barni a tsaye, girgiza kai nayi sannan na koma cikin 'daki na, qara gyarawa nayi sannan na sake fitowa, muryar Noorie naji tana cewa

"Ni bana washa da Ayaan juka na yakeyi (ni bana wasa da Ayaan duka na yakeyi), amma ti Ayiyan baya juka na tine aboci na (Amma shi Aryan baya duka na shine aboki na)"

Abba kuma yana ce mata

"To meyasa kike tsokanan Ayaan 'din?"

Cewa ta qara yi

"Wai jan nace miti baybeya iyin yadda Mami tate te mai (wai dan nace mishi barbela irin yadda Mami take ce mai)"

Dariya Umma da Abba suka kwashe da shi gaba 'daya, nima da murmushi na nazo nace

"Baby Noorie Sarkin Surutu"

Umma ce tace

"Jabeer 'din yazo ne?"

"Eh yazo" nace mata

Sannan Abba yace

"Ki gaida shi toh"

Cewa nayi

"Toh Abba ze ji Inn Sha Allah "

Noorie ce tace

"Mami ina da ti (Mami ina zaki)"

Cewa nayi

"Zanje waje ne Bibinuyi zaki je ne"

Girgiza kai tayi alamar A'a, se na ce mata

"Zo muje yanzu zaki dawo"

"To" tace sannan ta saki hannun Abba ta zo ta riqe mun hannu na, ce ma Umma nayi

"Umma Ina Ameerah?"

"Tana 'daki yanzu zanje in duba ta ma gara da kika tuna mun"

Fita nayi na samu Jabeer a mota, gaisawa muka yi sannan nayi mai iso cikin qaramin parlor, yana zama yace ma Noorie tazo wurin shi, hannun ta a baki taje ta same shi, cewa nayi

"Noorie remove that finger from your mouth"

Cire hannun tayi a baki sannan Jabeer yace mata

"What's your name?  Ya sunan ki?"

TASNEEM 1 in TASNEEM Series✅Where stories live. Discover now