*بسم ا لله لر حمن لر جيم*
🌳🌳🌳🌳🌳🌳
🌳🌳
*GྂUྂDྂUྂ Aྂ JྂEྂJྂIྂ*
🌳🌳🌳🌳🌳🌳
🌳🌳*₴тояу щяїттёи Ьу*
*ᏃᎯᏂᖇᎯ ᎯᏰᎴᏌl{mᏫm ᎯᏂlᎯᏁ}*
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''https://www.Facebook.com/kainuwawritersassoc
🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚
*filin gaishe gaishe*
*jinjina da gdy gareku masoya na* *wanda nasani da wanda bansani ba yanda kuka bibiyi lifftafina ina gdy sosae kuma ina matuqar qaunar ku naso na lissafu ku amma ina busy Allah yabar qauna*🅿-3⃣4⃣➡3⃣5⃣➡🔚
Anya kuwa ba khalifa bane wannan ?
Domin muryan sa naji a ƙarshen maganarsaNa shiga uku ni dauda gashi na basa takardun nan
Amma duk iya makircinka zaka haɗu da dauda ne ya koma cikin parlorn jikinsa na masa zafi ga tashin hankali ga zazzabi
Doctor yasa aka kira masa ya duba sa domin jikin na ƙara masa zafi sosae ga ƙaiƙayi wani lkc har kwakwalwarsa yakejin ƙaiƙayin
Khalifa kallon takardun yayi sannan yayi murmushi a mota babu mai mgn har suka isa hotel din da suka kama sukayi othern abinci
Suka watsa ruwa kafin suka zauna domin suci abincin
Saeed ne yafara kyalkyala dry ba ƙaƙƙautawa nabeel Ahmad ma suka hau tayasa domin sun gano dryn da yakeyi
Sameer da khalifa suka sake baki suna kallonsu
Sameer yace lpyr ku kodai kafin mu baro gidan dauda yabaku abu kunsha ne ?Cikin dry saeed yace wlh ban taba tunanin dauda asalin zindiƙin jahili bane kamar haka ace baka san mutane ba amma ka ɗauki takardun dukiya mai tsaban yawa kamar haka kabasu lallai dauda asalin maloho ne
Sameer ma dry yasa yace ai irin su dauda mugunta ne aransu kwata kwata basu sa komai agaban su ba
banda mugunta anya irin su dauda suna tunanin mutuwa kuwa?Ahmad ya ɗan sassauta dryn sa yace ina kuwa mutane masu halin dauda zasuyi tunanin mutuwa bayan su bazasu mutu ba ai shi makashi gani yake kamar baxai mutu ba
Saeed yace wlh kuwa inaji dauda shine a gate din farko ya ƙarashe mgnr da sakin wata dryn
Khalifa yace gate din farko kamar ya?
Saeed yace na gadin duniya mana khalifa yayi murmushi domin mgnr su tabashi dryAhmad yace yanzu gobe zamuje da jami'an tsaro aka masa ko dan gsky mutane ire iren dauda barinsu cikin al'umma babbar hatsari ne
Khalifa ya girgiza kai yace ko daya ba gobe za akama dauda ba
Duk gabaki daya suka tsaya suna masa kallon tuhuma mai kake nufi khalifa?
Murmushi takaici yayi idonsa suka ƙaɗa sukayi jaa yace inaso sai dauda ya rasa ma tsuguni domin harta takardun gidan abba wanda daudan yake zaune yana nan acikin wa innan takardun kuma dauda bai siya wata kadara ba balle ya tsira dashi
Nabeel yace ai shi duk a tunaninsa kun mutu ya kashe ku shiyasa yake cin karan sa ba babbaka
Sameer gobe zamuje da kai zaka siye gidan abba na gwarimpa wanda dauda ke ciki amma kafin nan zanyi mgn da my wife domin tasan halin da ake ciki
YOU ARE READING
GUDU A JEJI
ContoGUDU A JEJI, LABARI NE MAI CIKE DA TAUSAYI, CIN AMANA, HASSADA, KYASHI DA SON ZUCIYA, KARKU BARI A BAKU LABARI, KU HANZARTA KARANTAWA DAN KU JI ME LABARIN GUDU A JEJI YA KUNSA, KU DAGA JI KUNSAN AKWAI CAKWAKIYA, KU DANNA MIN VOTE KU YI FOLLOWING DIN...