Chapter 20

421 52 3
                                    

*NA TAFKA KUSKURE..!*

*Wattpad:Janafnancy13*
_Mallakar:Janafty_💞

*20*

"Wurin ma'ajiyar hotuna tafara shiga domin tadan san kan waya domin Aisha yayanta yataba bata wata tecno D3 _my first phone wo...Ammh sai da akasamu barawo ya saceta_😡abun mamaki hotunan Dr ne dana Adil kawai aciki kala kala iya kallonta wani suna kwance wani suna zaune wani yagoyasa gasunan dai sai iya kallanta,abun da yaba Safeena mamaki shine shin uwar yaron nan basu tare da Dr ne domin taga koda sau daya bata ganta acikin hotunan ba sai dai shi da Dr to kodai ta rasu ne..? tayi saurin rufe baki aranta tana cewa"Da ta rasu da Ummi ta fadamin"haka dai taita kallon hotunan babu hoton daya burgeta sai wani hoton Dr yana sanye da american suit,black and white ya daure wuyansa da tektie baki kansa yasha gyara yana maiko hannunsa sabe da rigar likitocinsa yana mikama Dr Tahir abu abakinn wani office ya juyo da gilashin dayake karamasa da kwarjini yana dariya aka dau hoton hakoransa farare reras suka bayyana hakika yayi kyau matuka a hoton wanda har Safeena tayi serving dinshi a Fuskar wayar saboda kyan dayayimata.

tana cikin daki taji sallamar Aisha suna gaisawa da Ummi kafin tatambayi Safeena Ummi tace mata tana ciki da Sallama Aisha ta shigo Safeena ta amsa tana fitowa daga uwardakan Ummi hannunta rike da waya tace"Yar halak yanzu nake zencencenki araina"Harara ta sakarmata kan tace tana zama kan kujera"Bawani nan ai ni wlh baruwana dake yanzuma zuwa nayi naji lpy baki zuwa mkranta kwana biyu"..?Zama Safeena tayi kusa da ita tana fadin"Allah sarki kawar arziki...Dalilin dazai kawoni kenan"Tafada tana dafata mikewa tayi ta isa ga botikin dake dakin tasanya kofi ta debo ruwa tana juyowa taga Aisha rike da wayar tana juyawa cike da mamaki gabanta ta ijiye ruwan tana fadin"Sha ruwa Aisha kafin muyi mgana"Shuru Aisha tamata tana bin wayar da kallo chan ta shafa saiga hoton Dr ya bayyana wow...Shine abunda Aisha ta Furta tana bin hotonn Dr da kalon kafin tadago tana kallon Safeena datake kallonta tace"Kawata waye wannan gayen..?...Ke wayarma tawaye wai? Safeena tayi mirmishi ammh aranta taji zafin yadda Aisha take kallon hoton Dr tana Shafawa cike da shawa'a da    burgewa _ho kishi🤔 tashi tayi ta isa ga windo  Dakin kafin tace *MIJINA NE* da saurin Aisha tace"Mijinki kuma? tafada da sigar tambaya da mamaki juyowa Safeena tayi tana mirmishi tace"Eh...Mijina ne Aisha wanda Abbah yadauramin aure dashi kusan wata daya dawani abu da suka wuce"Sororo Aisha tayi kan ta mike tsam ta ijiye wayar takama hanyar ficewa tana fadin"Kinga nidai nayi gaba don aiki nake na fito ban iyawa da shirmenki Safeena"Safeena tayi mirmishi tace"Wlh da gaske nake Aisha nima yadda kikaji haka naji lokacin da Abbah ke fadamun"cak Aisha ta tsaya kan ta waiwayo tace"Wai da gaske kike Safeena..?"Karasowa tayi tadafata kan tace"Da gaske nake Aisha dama shine abunda zai kaini gidanku kenan".

Tsuru tamata da ido kafin tazame hannun Safeena ta isa ga wayar tashafa hoton Dr ya bayyana ta nuna ma Safeena tace"Kina Nufin wannan balarabe ko ince bature shine mijin naki..?

Dariya Safeena tayi kan ta isa kusa da Aisha ta amshi wayar ta kurama Dr ido tace"Kema kina tamtama ko Aisha..?"tafada tana kallonta kan taja hannunta su isa kan kujera tacigaba dacewa"Nima haka naji lokacin dana fara tozali dashi amatsayin mijina Aisha wlh babu karya Dr Safwan sale Safana shine mijina"Aisha tayi shuru tana kallon Safeena kan tayi wuf ta rumgumeta tana fadin"Kawata u ar so lucky wlh....Nayi murna sosai lalle kin tabbata mai sa'a

Nan Safeena ta warwarema Aisha komai tundaga farko har karshe Aisha ta jinjina kai tace"Ikon Allah kenan Safeena wlh in Allah yaso ka da Ni'imarsa bbu mai hanawa...Kinga abun Allah ko"Safeena tace"wlh ko amafarki bantaba tsammani ba Aisha sai gashi Allah da ikonsa ya zartar da komai"Aisha ta jinjina kai tana kara tabbatarma da Safeena ita mai Sa'ace.

Haka Aisha takoma gida tafadama mamanta ita kin yarda tayi sai da tasawo hijabi tazo ta tambayi ummi,Ummi tace"da gaskene kana ta yarda tasa albarka tareda da addu'an zaman lpy.



NA TAFKA KUSKURE..!Where stories live. Discover now