Chapter 18

399 41 7
                                    

*NA TAFKA KUSKURE..*

*Wattpad:Janafnancy13*
_Mallakar:Janafty_💞

*DEDICATED TO:My Momma Hajja Hadiza muhammed Ba'are*

*18*


----- Dukkansu barcinsu rabi da rabine domin kowani dakika zuciyoyinsu suna bugawa da sunan juna,amassallaci kusa da gidan su Safeena suka yi sallah sun  gaisa da Abbah sundade tare suna mgana har Dr Safwan yafadama Abba,da zarar ya koma ammh insha Allahu yana komawa zai tanadarma Safeena inda zata zauna sai susa lokacin da za'a ayi bikin Abbah yafadamasa kar ya takura kansa Safeena kanwa take agurinsa.

suna dawowa sukayi wanka domin yau monday tushen aiki suna da aiyuka a hospital,shiyasa Allah yasa shi Dr yana ijiye kaya amota kamar yasani dinkinsa daya amso wajen kala uku su ya dauko ya sanya daya yabama Tahir daya kafin karfe bakwai sun zama ready.



itakuwa Safeena tana idar da sallar asuba bata komaba,fita tayi ta share gida tagyara dakunan tazo ta musu abun karyawa kunun tsamiya tamusu da kosai daman tana tashi waken tafara wankewa,sai ruwan zafi wanda yaji citta da na'ana'a tashirya cikin riga da sikat na leshi milk and green kayan fiteed ne sun amsheta sun mata das da ita green din hijabinta ta tasaka,dogo har kasa ta dauki kayan akwando tama Ummi Sallama hakika Ummi taji dadin ganin yadda yarta bata Nuna wani damuwa ba duk da dai tasani aurene kawai ammh Dr Safwan ba ajin yarta bane _Abun Allah kenan_



Koda ta isa da kaya niki niki ta iske daga cikin gidan ankawomusu soyayyen arish da kwai harda kayan tea ta iskesu sun shirya ta duka har kasa tana gaishesu Tahir ne ya amsa yana dariya kan yace"Tashi mana amarya mun amsa gaisuwar aie"Shikuwa Dr Safwan tunda Safeena ta shigo kamshim humran data sa yashakeshi yarasa Natsuwarshi kallonta yake cikin wani yanayi wanda ya kasa gane kanshi Dr Tahir daya Fahimci haka ya fice ya basu wuri.



Tana nan durkushen kanta na kasa tana wasa da gefen hijabinta gaban na tsananta faduwa domim tasan wannan kallon nashi mai kadamata yayan Hanji yake mata ahankali tadago kanta caraf suka hada ido yana tsaye sanye cikin wani farin yadi milk mai sansti bayi da kauri tunda har ana hangan farar vest din dake jikinsa hulan kasan zannah bukar ce fuskarsa tayi fayau da ita yana furta da Annuri Kamar daren goma sha tara duka hannuwansa ya rumgume akirjinshi,kasa jaye idanunta tayi jitayi kamar kasa baza ta iya daukanta ba saboda wani kasala ke rufeta tsigar jikinta na tashi yarr!!!

saurin jaye idanunta tayi saboda tana gab da zubewa agurin mirmishi yayi kawai ya jawo kwandon data shigo dashi ransa yamasa dadi dayaga kunun tsamiya da kosai,masha Allahu yasha sosai kosan ma yaci sai ruwan na'ana'a shima yasha kadan ammh kowani lokaci tadago idanunsa na kanta,yana kammalawa yasa tissue yagoge baki ya mike yana fadin"Alhamdulillah...Yafada yana kallonta kai tsaye ya isa kusa da ita bata ankara ba shima ya durkusa har gwiwansu na gogan juna da Hanzari taja baya kallonta yayi kan yace'"yan matana yakamata amin ramgwame naga wannan kwalliyar kan in Tafi"Yafada yana wani lumshe idanunwanshi tuni jikin Safeena yafara rawa takasa dagowa sai ma kara dunkule data keyi cikin hijabi wani yanayi keJan Safwan yayi saurin mikewa kada yabi shawaran zuciyarsa na Rumguman yar mutane.

Wayoyinsa ya Dauka yayi Hanyar ficewa yana fadin"Shikenan tunda kin Hanani ganin Halas dina"yafada muryansa kamar zai yi kuka,taga da gasken  ficewa zaiyi da sauri ta mike cikin rawan murya"Am.... _*UNCLE*_"cak ya tsaya kafin ya waigo yana kallonta so yake ya tabbatar da itace takirasa da Unku kai verry interresting.


Cikin kunya matsananci ta yaye hijabinta ta rike hannunta kanta na duke tace"kayi hakuri…"tafada dajan Numfashi kamewa Dr Safwan yayi yana kallon Safeena tun daga sama har kasa yake kallonta idanunsa na yawo ko'ina ajikinta Safeena doguwace mai dauke da doguwar fuskar gashin idanunta sun matukar burgeshi structure din jikinta shi ya tafi dashi uwa uba Nonuwanta dasuke cike tab atsaye suna masa maraba cikin mutuwar jiki da wata irin fitinanniyar murya ya Furta'Tsarki ya tabbata ga ubangijin dayayi wannan Halittar...."Yafada still idanunsa kyam akanta ita kuwa yadda idanunsa ke yawo ajikinta haka takejin wani sanyi na ratsata kamar wacce zata yi masassara,cikin tafiyar kasaita ya karisa kusa da ita yasa hannunsa ya tallabo habanta yana fadin"Baki kyautamin ba Sam Safeena daki Ka hanani ganin wannan kyakyawan suran taki da wuri"Ya fada yana kokarin sa idanunsa anata itakuma taki saima runtse ido da tayi zuciyarta na bugawa tsuru yamata da ido yanajin wani magnet najansa wanda baisan sadda yasa Hannunsa duka biyu ya rumgumota ba yamata kyakyawan tarba afaffadan kirjinsa.

NA TAFKA KUSKURE..!Where stories live. Discover now