Chapter 32

371 29 2
                                    

*NA TAFKA KUSKURE.."!*

*Wattpad:Janafnamcy13*
_Mallakar:Janafty_💞

*DEDICATED TO:My Momma Hajja Hadiza muhammed Ba'are*

*32*


"Momma ta shiga motar direct suka wuce S&S SAFANA SPECIALIST HOSPITAL Ma'ana asibitinsa suna zuwa suka rufi kanta dashi da Dr. Tahir don bai yarda sauran sun tabamai mata ba Alhamdulillah sun gano ciki dan sati hudu da kwana biyu wata daya kenan,buguwar datayine jini ya yanke mata anyi saurin xuwa asibiti dat why cikin bai zubeba sun yi nasarar tsaida jinin suka mata allurai suka kaita dakin hutu.

Sakina tadade tana kuka nadama mai karfi ta shigeta lokaci daya domin tasan duk takamarta da Safwan take gashii yanzu ya saketa ina zatasa kanta yanzu...yan aikinta ta kira suka hada mata kayanta kaf bazata iya tuka mota ba saboda halin datake ciki direba tasa yakaita tasha ta hau mota sukuma su latifa taba kowannesu na mota tace su koma gida tareda albashi.

Sai yammah ta isa katsina dan adaidaita ya sauketa tabashi kudinsa mai gadi ta kwalama kira yazo ya jidan mata akwatuna yana kaiwa cikin gida Hajiya kari dake zaune afalo tana kallo taga ana shigowa da akwatuna saurin mikewa tayi tana fadin"Kai daga ina kuma..?

"Bai bata amsa ba Sakina ta sawo kai Falon sororo Hajiya kari tayi  tana binta da kallo da gudu Sakina ta isa ta fada jinkinta tana Fadin"Hajiya ya Sakeni wlh ya sakeni"Cikin karaji hajiya tace"Yame....."Sakina tace"ya sakeni hajiya safwan ya sakeni"

Ya sakeki kuma shine kika zomin gida"Muryan kwamishina ta katsesu wanda ke kofar falon yana takowa cikin bacin rai sakina da Hajiya suka kalli juna kafin hajiya tace"Haba Alhaji tanada inda yafi nan ne"Kai tsaye yace"Wannan ya rage  nata ammah na rantse bazanyi kaffara ba duk randa sakina ta kaso aurenta bawani dalili bazata zaunamin agida ba"Sakina ta sulale akasa tana Fadin"na shiga uku dady in ka koreni ina zani"Ya juyo ransa abace yace'"inda kika zaba sakina...Duk hakurin yaron nan sai da kika kuresa ko..?"girgiza kai tayi tace"Abbah hajiya da Anty lailane sukaje gidana suka na amshi  Adil ahannu Safeena wanda Safwan ya bata shi tana rikonsa"Hajya kari tace"Wata Hajiyar don ubanki"Tafada tana ballamata harara.

Sakina tace"Wlh Daddy susaka sani na aikata abunda har Safwan yasakeni"mirmishin takaichi yayi yana fadin"Very gud naji dadin haka kinga yanzu sai itama tabi ki....Sai ku nemi inda zaku"Hajiya kari tace cikin tashin hankali"In bita ina Alhaji...?Ya fara taka step kan ya waigo yace"Ki bita ku tafi koma ina ne Nima na sakeki Saki daya"Hajiya kari tasa ihu tana fadin"na shiga uku ni karima Alhaji ka sakeni fa kace"Yace idanunsa cike da kwallah"Eh....Haka nace  ba abunda zance miki sai Allah ya isa tsakani na dake karima aurena dake babu abunda na karu dashi sai tabarbarewan rayuwa kije duniya takoya miki hankali keda yarki.

Yana gama fadar haka ya haye sama yana share kwallan daya ziraromasa hannu akai Hajiya kari ta dora akai tana kwarma uhu tana fadin"Shikenan Sakina kinzo nima kin kashemin aure"Sakina dake gefe tana kuka tace"ni dakuka kashemin nawa fa hajiya"Hambari ta kai mata tana fadin "Don ubanki waya kashe miki aure kika dai kashema kanki...Ai sai ki tashi mu san nayi"

akwati daya Hajiya kari ta dauka sai Atm dinta suka rankaya suka fice cike da takaichi megadi na musu mgana sukayi banza dashi suna fita kwamishina ya kira Anty salma ya labarta mata komai kuma yace ko sun kira ta  zasu zo gidanta tace basunan sunyi tafiya Salma saboda bakinciki saida tayi kwallah ta amsa to ammh aranta tana so tasanya mizanin wata irin uwa Allah ya basu.

Sai da suka fita suka fara tunanin inda zasu yanke hukunci kiran Laila sukayi Sakina ta kirata take fadamata Abunda yafaru cikin razana laila tace"mun shiga uku Daddy yasaki Hajiya"Sakina tace"eh...Nima fa ai saki na Safwan yayi har Saki biyu"Anty laila tace"garin yaya sakina"Sakina tace cikin fusata"garin bin shawarar dakuka bani....Yanzu Daddy yace bazamu zauna mai agida ba to gamunan zuwa"Zuwa ina......Ta fada cikin firgici cikin mamaki Sakina tace"gidanki mana"Da sauri Laila tace"Kut...Wlh badani ba nima kuzo ku kashemin nawa aure tab...Ku tafi kankia gidansu hajiya zuwa goben ina tafe"daga haka ta kashe wayar sororo Sakina tayi da waya ahannunta tana kallon Hajiya kari dayake wayar a handfree ne taji komai.

laila ta rike baki tace"kutumar uba in barku kuzomin gida yadda mujaheed yake kume dani ai sai yace mu rankaya dukkanmu....Tab....Su karata chan nima ina lallaba rayuwatane

Sakina ta fashe da kuka tace"wlh bazan iya zama a kankia ba hajiya"Cikin bacin rai Hajiya kari tace"to don ubanki sai dai ki nemi gun zuwa domim banda nan bbu inda zamu a amshemu"Sakina batayi mgana ba ta kira Anty salma sai da tabata 2miss cll kana ta dauka cikin kuka take fada mata abunda ke Faruwa mirmishi mai kama da kuka salma tayi kan tace"Ayy bamu kasar mun tafi kasar turkey baban shahid yaje wani aiki ne"daga haka ta yanke wayar.

Basu da zabi illar zuwa tasha suka hau motar kankia sakina kuka taketa yi tana fadi  su suka kashe mata aure...Itakuma hajiya tana fadin ita ta kashe mata aure abu har yazaman musu fada amota sai kallonsu ake ana tirr dasu.

Sai bayan issha"i suka isa kanki koda suka isa gidansu Hajiya kari wanda daman iyayanta sun rasu  yayyintane agidan wanda ta gujesu sai tayi shekara bata leko ba sunyi mamakin ganinta matuka anan take fada musu karya da gaskiya basu yarda ba adaren sukama kwamishina waya yafada musu komai game da hallayar Karima suna ko jin haka suka ce babu ruwansu da ita sai da ta shiga wani yanayi ne zata nemesu to sukan babu ruwansu da ita gidane tazo ta zauna ga dakin mamansu chan data rasu su share kafa su zauna tunda zaman suka zaba.

Haka suka ja jiki asanyaye suka wuce koda suka shiga dakin sai da suka kusa kuka saboda yadda dakin ya lalace ga ruma tako'ina rufin dakin na azarane duk ya kusa ruftowa ga simintin duk ya banbare beraye na Safara ga gefe daya wasu buhuhunan kaikayi ne bbu ko katifa sakina kan akwatin ta ta haye tana kuka ita kuwa hajiya gyalenta ta shimfida ta zauna ga yunwa na addabansu rabonsu da Abinci tun na safe.

haka suka kwana Sakina kuka ta kwana yi hajiya ko da takaichi ya cika ta dunga durama sakinar zagi tana cewa"ki rufema mutane baki duk wayaja bake ba inda kinyi hakuri agidanki har yaushe za'a sako ki balle har kizo nima kashemin aure"Sakina tace cikin kuka"duk baku kuka kashemin auren ba wlh hajiya keda Anty laila ba abunda zence muku sai Allah ya isa"

Hajiya kari tace"Nima Allah ya isa tsakani da ke inda daya sakeki kin nufi wani wurin har yaushe Alhaji zai sakeni...Duk iya abunda nakemai baitama furta sake agareni sai akanki ni yakamata na miki Allah ya isa sakina"

_Hmmmm haka Rayuwa ta gada daman_

Haka suka kwana wanda Sakina dakyar taga Safe saboda cinnaku da beraye sun hanata sak,ita hajiya haka abun yake agurinta matan gidan kuwa ba wacce ta kallesu saboda daman tuni suka tsaneta domin ko gidanta kaje tadinga kyamatarka kenan.

Sakina gari na waye tafice mota ta hau tatafi banki tayi ciro kudi dubu dari tatafi kasuwa tayo musu siyayyah don tace baza ta iya rayuwa ahaka ba, komai ta siyo su kayan tea indomie macrooni complex kai katifa da fridge saboda bazata iya shan ruwa bbu sanyi ba ta siyo fanka komai da komai mota ta sauketa har kofar gida tasa aka shiga dashi matasan gidan tasa suka kwashe tarkachan daki suka gyara musu kana suka shiga mata da kayan ta biyasu,sai dai Hajiya kari ta ganta da kaya kawai aranta taji dadi domin daman ko ita da'aka haifa anan bazata iya irin rayuwarsu ba.










Commet
And
Share
Vote

*Shakira..*

NA TAFKA KUSKURE..!Where stories live. Discover now