b user: Khadeejaht Hydar Deejaht.
❤❤💋💋
IHSAN
❤❤💋💋(Romantic, Love,Sorrow)
❤❤💋💋✨✨Written By
Khadeejaht Hydar.
Young Novelist.✍🏻💫FAGEN MARUBUTA WRITERS ASSOCIATION💫
❤Gidan zaman lafiya,Aminci,Hadin_kai,da yardar juna insha Allah ❤
Dedicated to Sis🧕 Sarah(Afra).
✨48✨&✨49✨
Juyowa yayi don gaskanta abinda kunnu wansa suka ji, Babu tantama wannan Ihsan ce to amma meya fito da'ita har wannan abubuwan suka faru?.
Karasowa bakin gadon yayi yace" kanwata daman kece,Amma nakasa ganeki."
Tace" yaya nice randa za'a taho dani ma nagane ina hannun waenda kuke da alaka, amma bana iya magana alokacin."
Su mama dasuka tsaya kallon ikon Allah,suna zaune suna jinsu.
Mummy ce tace" Hisham daman kasantane? Yace" eh baki santaba amma mama ta santa."
Mama kallonshi tayi da mamaki tace" ni kuma aina nasan ta yace" Mama Ihsan din Deen ce fa."
Cikin rashin fahimta da mamaki da son tuno wacece Ihsan din Deen tace" Banganeba fa Hisham fahimtar dani."
Yace" Ihsan din damuke nema ce ai,Ihsan din Deen.
A razane mama ta mike tayi bakin gadon,don gasgata abinda taji.
Riko hannun Ihsan tayi wacce ke hawaye,mummy ma ta karaso mama tace" dagaske Ihsan kece."
Tace" Eh nice Mama,ikon Allah cewar mummy."
Nande tabasu labarin komai ta gama tana zubda hawaye,Hisham ne yace" Allah ya kyauta shima Deen din yana.."
Be karasaba mama ta masa alamun dayayi shiru ,Amma sun makaro don tunda ya ambaci Deen ta kafe shi da idanu,alokacin da mama ta masa alamun yayi shiru ma ta gani. "
Hankalinta inyayi dubu ya tashi,dan tasan ba lafiya ba tunda yana son fada mata wani Abu game da Deen Amma mama ta hanashi.
Hannun Hisham ta rike muryarta na kar_karwa tace" Dan Allah yaya kafadamin ko hankali na ze kwanta,in bakafadaminba bazan samu nutsuwa ba."
Shiru yayi yakasa magana,magana ta sake masa akaro na ✌tace" Dan Allah yaya kafadamin."
Mama tace ki kwantar da hankalinki," tace" mama hankalina bazai taba kwanciyaba harse naji abinda kuke boyewa saboda nasan yanada alaka da Yaya Deen.
Mama ce ta sauke ajiyar zuciya,sannan ta fada mata komai .
Jin yana asibitin da take cikine yasa ta kokarin tashi, muumyn Fahad ce tayi saurin riketa .
Hawaye ne ya sauka a kumatunta,jin duk rashin gatanta wani na kwance a gadon asibiti saboda ita.
To miye amfanin zamanta anan, sake yunkurin tashi tayi ,tana cewa Dan Allah Ku barni in duba shi wallahi in banjeba zan'iya mutuwa.
Hisham yace" to bara nakira likitan yacire miki karin ruwan, jin haka ne yasata komawa ta zauna."
A kofa sukaci karo da likitan,dawowa sukayi tare cikin dakin.
Likitan yace" to Alhamduliilah munsamu ya farfado amma yana ta kiran sunan Maman sa,don haka muna son ganin mamansa."
Hisham ne yace" mama kije ni saina tsaya anan,Ihsan tace"Mama nima zanje Dan Allah."

YOU ARE READING
IHSAN
RomanceROMANTIC LOVE STORY,IS ALL ABOUT AN ORPHAN WHO SUFFERED ALOT FROM HER STEP MUM,BUT LATER HAVE A BETTER LIFE WITH THE HELP OF 3 PEOPLE,,JUST READ ND FOUND OUT WHO THE 3 STARS ARE