page 1️⃣

587 14 12
                                    

🦚🦚🦚
*ISMAT?*
       🦚🦚🦚

(The young lady)

*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION*🌞

( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN  OUR READERS 💪)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P.W.A✍️


*STORY & WRITING*

*BY*

*SAFNAH ALIYU JAWABI*

1️⃣

*Life has a way of unfolding when you least expect it. You’ll be betrayed by those you trusted. You’ll fall out with so-called friends. Don’t despair. The Almighty is in full control. He knows who should go & who should stay. He will pave a way out for you. Keep going. Trust Him!*

*BISMILLAHI RAHAMANIR RAHIM*

,,,,,,Zaune take tayi shiru da alamu akwai abinda take tunani ,lokaci zuwa lokaci take duba fuskar wayar ta,can najiyo wani sauti Mai dadin sauraro Yana fitowa daga wayar,jiki na rawa ta dauki wayar ta makala akunnan ta,shiru tayi batare data farta komai ba tsawan dakika,can dai naji ta bude baki kamar tana tausayawa liɓenta tace"assalamun alaikum.

Bana iya jiyo abinda ake faɗa daga ɗayan bangaran saidai  alamu sun nuna tana farin ciki da duk Wanda take wayar.

Kusan mintina biyar ta dauka tana magana cikin wayar,sannan ta kashe ta,cikin sauri ta bude data,aikuwa nanfa saƙonni suka fara shigowa,wata number naga ta zaƙulo Wanda aka ajiyeta da wata suna Mai mahimmanci agunta, *muradin zuciya*

Sakon sane yafara shigowa kamar haka... Mahadin rayuwa.

Murmushi tayi har saida fararan hakoran ta suka baiyana,cikin sauri itama ta amsa masa...na'am muradin zuciya Kuma sanyin idaniya.

"Da fatan dai kina cikin ƙoshin lafiya??

"Alhamdullah kaifa?

"Nima haka,Amma kinsan babu yanda za'ayi farin ciki ya zauna atare Dani idan banji kiba?

Murmushi ta kuma yi tana Mai jin tsantsar kaunar sana bin duk wata jijiya na jikin ta.

"Nima haka, ka sani ko wani fitar numfashi na da soyayar ka take fita,nidai duk ba wannan ba,Don Allah yaushe zaka zona ganka habibi??

Gyara kwanciyar sa yayi yace,"karki damu in Sha Allah da akwai abinda nake jira ne, amma zanzo inganki kima ki gani,domin kuwa kallon hoton ki bazai taba wadatar da zuciya ta ba idan ba ganin ki nayi ba.

Haɗa fuska tayi kamar yana ganin ta tace," ba'ama gwanda niba tunda ka taba ganin hoto na,nifa haryau bansan kamanin kaba.

Shima murmushi yayi yace,"karki damu Inada nawa dalilin dayasa ban baiyana Miki fuska taba,nafi so ki ganni da idonki.

"Tom shikenan Allah ya nuna Mana lokaci.

"Ameen,Kinga bara nayi sallah Sai muce gaba kinji baby?

"To dama Nima aiki zanyi yanzu.

"Shikenan byee.

Sauke ajiyar zuciya yayi lokacin daya suks sauke wayar,dafe Shi haidar yayi yace,"nasan halinda kake ciki abokina kayi hakuri in Sha Allah zaka samu *ISMAT* matsayin mata, ka daina sawa kanka damuwa.

"Hmm haidar baka San yanda nake son wannan yarinyar bane, Wallahi ta tafi da duk wani tunani nawa,saidai ba anan gizo ke saka ba,kasan ko fuskata ta Bata'taba gani ba?

"Kai haba? To meeyasa baka tura mata da hoton kaba?

"Kawai ina jira lokaci yayi ne,nafi sota ganni da idanuwan ta.

"To idan Kuma tace bakayi mata bafa?

Dariya *AJMAL* yayi yace,"haba malam kaima fa kasan indai cikar zatine tofa duk inda ake niman namiji Kai kanka kasan nakai,mata nawa ke bina nayi burus dasu Saboda *ISMAT* ?

"Hmm haka ne,Amma kai ka taba ganin tane?

Hhhhh"sosai ma Wallahi hotonan ta acikin wayar Nan basa da adadi.

"Kai Gaye kace dai zazzaface?

"Kaima kasan *AJMAL* bazai taba faɗawa soyaya da mummuna ba.

"To anuna mana ita Mana.

Nandanan fuskar *AJMAL* ta canza,gabaki daya annurin fuskar sa ta ɗauke,"malam duk yanda muke dakai zamu samu matsala duk randa ka Kuma min irin wannan tambayar ,kan Mee zaka ga hoton ta?

"Yallabai Mee kuma abin fushi,idan takan hoto nee Allah yabaka hakuri bazan sake ba,batare da *AJMAL* ya Kuma bita kansa ba yayi ficewar sa.

*******

Ita kuwa *ISMAT* Koda ta rufe data tsurawa wayar ido tayi tana jin inama ta ganshi gabanta,tashi tayi ta shiga kitchen ta fara aiki.

Tana tsaye Mustafa kaninta ya shigo da gudu yana cewa,"aunty *ISMAT* Wai kizo.

Rike masa kunne tayi tace,"bana hanaka gudu ba.

Marairaice fuska yayi yace,"kiyi hakuri bazan sake ba.

"Yauwa to wake Kira na?

"Aunty Aisha ce tazo.

Ai *ISMAT* Bata tsaya jin zancan Saba ta nufi falo da gudu,binta da kallo yayi yace,"tace na daina gudu gashi ita ƙatuwa tana yi.

Da gudu suka rungume juna suna murna,kallon ta *ISMAT* tayi tace,"k
Ƙawar yaushe kika dawo?

"Sauka na kenan jakata kawai na ije nashigo.

"Aiyya zomu shiga ɗaki.

Hannun su sarƙe Dana juna suka shiga ɗakin *ISMAT*,bayan ta gabatar mata da abubuwan motsa baki  ta kalli aisha tace,"Kai kawar daga ganin bakin ki Yana dauke da magana menene faɗa min?

Aikuwa kamar  jira take ta fashe da kuka,lokaci daya *ISMAT* ta rikece tambayar ta take, amma Aisha kamar ana kara zuga ta,rike mata hannu *ISMAT* tayi tace,"ki taimaka ki faɗa min damuwar ki Aisha Don Allah.

Share hawayan ta aisha tayi tace,"*ISMAT* dana dauka masuyin soyaya mahaukata ne basa da aikin yine.

"Ashe ba haka yake ba,shiso Yana shigane batare da yayi shawara da kaiba, yake farraka zuciya ya samarwa kansa gurin zama,haka soyayar sa tayi min kamun kazar kuku,narasa inda zan saka Raina,kallo ɗaya nayi masa nasan shidin cikakkan namiji ne Ina sonsa *ISMAT*.

Da fuskar tausayi *ISMAT* ta kalle ta tace,"tabbas ko kadan bakiyi karya ba Aisha haka so take Bata da yare Kuma Bata sauranran ko wacce, Sai wanda ita kaɗai ke yinsa kuma take  jinsa,Nima haka na tsinci kaina bayan tafiyar ki da soyayar wanda muryar sa kawai nake iya ji,ban taba ganin saba,kullum ruramin wutar sonsa ake ,Amma kafin na baki labarin sa,ke kifara bani labarin naki.

Murmushi Aisha tayi tace,"lokacin da natafi kaduna Ina zaune agida kamar ance na fita bakin gite inazuwa idanuwa na sokamin gamu da Mai kyawun hallita, jingine jikin kofar wani gida Wanda yakasance kofar gidan sune.

"Kallon sa nake babu ko kifta ido, domin kuwa ya tafi da dukkan tunani na.

"Abin mamaki duk dadewar da nayi agurin Ina kallon sa,ko sau daya
Bai dauke idanuwan sa daga kan wayar saba,Sai murmushi yake Yana kara narkar minda zuciya.

"Haka na hakura na koma gida da tunanin sa cikin raina,haka kullum nake fitowa daidai lokacin da nasan yake fitowa waje,nayita daukar sa hoto batare da sanin saba,ana cikin haka wata Rana abokinsa ya kamani Ina daukar sa hoto,da gudu na tashi agurin da niyyar shigewa gida ,cikin sauri abokin ya tare Ni ,nanfa ya tambaya Ni dalilin daukar su hoto?batare da wani dogon tunani ba nafaɗa masa sirrin dake raina.

"Hakuri ya bani sannan, ya shaidda min lailai abokin sa yana da budurwar da yake so kamar ransa,Kuma abune Mai wuya ya amince da soyaya ta,Ni kuma jin haka yasa na tattara kayana na dawo,Saboda Wallahi idan harzan cigaba da kallon sa tofa babu shakka ciwon zuciya zai kashe Ni.

_

Tobe continue in Sha Allah_

ISMATWhere stories live. Discover now