5️⃣

49 4 2
                                    

🦚🦚🦚
*ISMAT?*
       🦚🦚🦚

(The young lady)

*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION*🌞

( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN  OUR READERS 💪)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P.W.A✍️

*STORY & WRITING*

*BY*

*SAFNAH ALIYU JAWABI*

5️⃣

*The best plan is  the one who knows what's ahead & what would happen. & there's only one who knows the unseen. That's Almighty. He's the best of the planners. Trust him & his plans. You don't know what's coming but he does. Have patience & you'll ace through all.*

,,,,, Haka lamarin yaci gaba da tafiya Soyayar *AJMAL* yana cigaba da ruruwa cikin zuciyar *ISMAT*, shima anashi bangaran haka abin yake, domin kuwa kullum da tunanin ta yake kwana yake tashi, sam bashi dawata buri daya wuce yaga *ISMAT* sa agaban sa....

Wani bangare kuma abinda ke ɗaga masa hankali bai wuce irin nacin kiran da aisha take masa ba.... Babu irin walakanci da  cin mutuncin da bai mata ba, amma san taƙi daina kiran sa, wannan abu yana mattuƙar damunsa...

******

Yauma kamar kullum aisha tana kwance, babu abinda take inba tunanin  *AJMAL* ba, sam zuciyar ta takasa hakura dashi..... A bangare guda kuma tana jin haushin kanta... Saboda irin kiran da take yawan yiwa *AJMAL*, wanda take ganin rashin dacewar sa.... Amma sam zuciyar ta takasa haƙuri... Koda tayi niyyar hakan sai taji ta kasa.

Janyo wayar ta tayi ta danna number sa, kira ɗaya ya ɗaga... Gabaki ɗayan su babu wanda yace da ɗan uwan sa komai... Can dai tayi ajiyar zuciya "tace, " kayi haƙuri nasan ina damun ka.... Amma don ALLAH  kamin wannan alfarmar koda sau ɗaya arana naji muryar ka sau ɗaya dan ALLAH.

"Sauke ajiyar zuciya yayi yace," menene acikin muryar tawa da kike son ji?

Cikin sauri aisha ta tashi ta zauna, ɗaukar filo tayi ta rungume  haɗe da lumshe idanuwan ta.... Tana jin wani irin natsuwa yana shigarta, tako ina...

"Malama kinyi shiru zan kashe wayata....

"Kayi haƙuri...

"Malama ba haƙuri nace ki bani ba, kawai ki faɗa min dalilinki...

"Ni kaina basan dalili ba, saidai kawai nasan muryar ka tana saukar min da natsuwa da kuma ɗebemin ƙewar masoye na...

"Meya same masoyin naki?

"Hmmm babu abinda yasame shi... Kawai dai shi kansa baisan inason sa bane, kuma sam nakasa mancewa dashi, ina mai tabbatar maka bazan taba iya rayuwa babu shiba....

Haka kawai *AJMAL* ya tsanci kansa da son jin labarin aisha, sosai ta bashi tausayi....

Itama taji daɗin yanda ya saki jiki da ita.... Koda babu komai kaso ɗari cikin damuwar ta hamsin ya ragu....

Hakanan sukayi sallama da alkawarin kullum rana zata kira shi sau ɗaya....

Koda suka gama waya, tsalle aisha tayi tace, "in sha ALLAH daga lokacin da abba ya bari na koma kaduna nayi alkawarin  ganin na shawo kan masoyina.... Tunda gashi duk taurin kan *AJMAL* na shawo kansa.... Don haka inada tabbacin masoyina ma bazaiyi wahala ba, daga nan sai na daina kiran saurayin *ISMAT*.....

*****

*ISMAT*kuwa kullum cikin kallon hoton *AJMAL* take.... Wani abu mai karfi ke fisgarta game da mutumin hoton.... Haka kawai take jin akwai wani halaƙa mai girma daya shafi rayuwar  ta..... A tattare da mutumin cikin wannan hoton....

Tana cikin kallo kiran *AJMAL* ya shigo wayar ta, jiki na rawa ta ɗaga, ajiyar zuciya mai karfin  ya sake yace, "sanyin idaniya...

"Na'am muradin zuciya.

"Don allah meyasa soyaya bata da adalci ne?

"Wani rashin adalci soyaya tayi maka bayan kana dani?

"Hmmm kedai ki bari, babu bata lokaci *AJMAL* yashiga bata labarin yadda sukayi da aisha..... Sosai itam ta tausayawa  yarinyar da yake magana akanta, muryar ta har rawa yake tace, "gaskiya na tausaya mata, allah yasa yasota koda baikai yadda take masa ba.....

"Ameen ameen.

"Amma ita bata san koda sunan saba?

"To sarkin son labari.... Nifa iyakar abinda ta faɗa min shine baisan tana sonsa ba,... Daga haka bata faɗi komai ba...

"Ikon allah.

"Ke malama mubar maganar  ƴar soyayar can.... Nidai ya soyaya ta?

"Soyayar ka tana nan kullum tana ƙara ruruwa...

"Lailai da saura tunda har yanzu  batayi gobara ba....

Dariya *ISMAT* tayi tace,"yauwa gaskiya dama inaso muyi magana ta fahimta dakai muradin zuciya ta.

Gyara zama *AJMAL* yayi yace, "ina jinki sanyin idaniya....

"Gaskiya abba yamin maganar fitar da mijin da zan aura jiya....

"Daya tambaye ki mekika ce masa?

"Ce manayi inada wanda nake so....

Sauke ajiyar zuciya *AJMAL* yayi yace, "alhamdullah...

"Da mekake tunani?

"Aa babu komai... Yanzu yakike so ayi?

"Duk yadda kace?

" *ISMAT* nidai ki sani ke nake so... Kuma ina fatan karasa rayuwa ta dake... Amma bansan taya zan fara shaidawa iyaye na wannan batun ba...

"Da mamakin jin furucin sa tace, "bangane ba.

"Marairaice murya yayi yace, "gaskiya *ISMAT* iyaye na bazasu bari nayi aure yanzu  ba, alhalin bangama makaranta ba, kuma bana da aikin yi.... Kina ganin mahaifinki zai yarda ya bayar da ƴarsa ga wanda ko aiki  baya baya dashi?

Wani irin zazzafar hawaye ke zarya a kuncin *ISMAT*,... Me hakan ke nufi???  *AJMAL* yana nufin bazai aure niba kome????

Jin shirun yayi yawa yasa *AJMAL* yayi gyarar murya yace, "baby kina jina?

"Share hawayan ta tayi tace, "ina jinka...

"Meyasa kikayi shiru kuma kina jina??

Kuka mai karfi *ISMAT* ta fashe dashi tana cewa,"yanzu dama yaudara ta zakayi?... Duk tsananin sonda kake ikrarin kana min?

Dariya *AJMAL*  ya kece da ita yana cewa, "ke wasa fa nake miki... Taya zance haka bayan nida kaina wannan rana nake jira....

Aikuwa baikai karshan zancan saba  ta kashe wayar gabaki ɗaya, kwanciya tayi saman gado tana cewa, "meeyasa zaka min haka muradin zuciya? ....

Baya kasan bazan iya jurar rashinka akusa dani ba??

Haka *ISMAT* ta yita sambatu ita ɗaya har barci yatafi da ita...

******

Shikuma *AJMAL* gabaki ɗaya hankalin sa idan yayi dubu ya tashi, kiran wayarta yake babu ƙaƙƙautawa, amma babu amsa,  kiran haidar yayi hankali atashe, jin irin kiran yasa haidar ya fahimci babu lafiya.... Cikin ƙanƙanin lokaci ya iso gidan su.

Labarta masa yadda sukayi yayi,.... Yana mai dana sanin abinda yayi.

Ƙwantar masa da hankali yayi yace...

""Yanzu ina mafita?

"Gaskiya dole gobe na tafi abuja... Wallahi baxan iya rayuwa ba haidar idan har *ISMAT* ta auri wani bani ba....

Murmushi haidar yayi yace, "kaji ta ambaci hakan cikin maganar tane?

"Malam kaga kaje ka shirya in sha ALLAH gobe zamu tafi abuja... Yana gama faɗan haka ya ɗauki wayar sa yafita daga ɗakin...

Girgiza kai haidar yayi yace, "ALLAH yakai mu goben....

.
*Muje zuwa*

ISMATWhere stories live. Discover now