1️⃣1️⃣

43 3 8
                                    

🦚🦚🦚
*ISMAT?*
       🦚🦚🦚

(The young lady)

*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION*🌞

( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN  OUR READERS 💪)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P.W.A✍️

*STORY & WRITING*

*BY*

*SAFNAH ALIYU JAWABI*

1️⃣1️⃣

*Dear Almighty. You have always been wonderful and merciful towords my future husband and I. Keep protecting my dear future husband and evil that men do which will surely leave after them. I believe in the oneness of the almighty and his judgement. You are the best of the judges . And let my enemies leave long and see what the future holds for me. Gdmorning every well wishers*


________Tashi yayi ya nufi ɗakin sa yana ƙara maimaita kiran layin A'isha wanda a yanzu ya kira babu adadi....

******
Sosai jikin A'isha yayi tsanani ta yanda saida aka dangana da asibiti.sosai take jin jiki duk wani ƙoƙari da Dr zasuyi sunyi amma jiki kullum gaba yake ..kuma duk yanda akayi ta faɗi abinda ke damun ta abu ɗaya take maimaitawa shine babu komai.

Tun abin baya damun Hajiya har abin ya fara damun ta.koda * ISMAT* ta samu labarin jikin aisha sosai ta shiga damuwa domin kuwa tasan cewar soyayyar *AJMAL* bazai taɓa barinta ta rayu cikin salama ba..
Koda ta isa asibitin kallo ɗaya ta yiwa A'isha taji wani irin tausayin ta ya lulluɓe ta..

Murmushin jin daɗi A'isha tayi tace,"Aminiya sai yau zaki zo duba aminiyar ki?

Kuka *ISMAT* ta fashe dashi tace,"abinda kike kina ganin shine daidai ko A'isha? "Yanzu A'isha kina ganin zan zuba ido naga kin mutu saboda son *AJMAL*?

"Wallahi aisha baki isa ba."babu abinda zaisa na yarda da wannan shawarar taki.

Fita zatayi cikin sauri A'isha ta janyo ta rungume ta tayi tace,"shikenan na yarda kiyi duk yanda kike so .amma kafin nan ki faɗa min abinda yin hakan zai haifar min.
"Karki mance *AJMAL* bani yake so ba .kuma baisan ina shan wahala saboda son sa ba.shin kin taɓa ganin inda akayi wa namiji dole ?

Girgiza kai *ISMAT* tayi hawaye na Zarya a kuncin ta.tashi tayi ta fice daga ɗakin..

Murmushi kawai A'isha tayi ta koma ta ƙwanta.

Washa gari Hajiya tayi mattukar mamaki ganin A'isha ta shirya tsaf kamar ba mara lafiya ba.  Tayi kyau sosai abinta.murmushi tayi tace,"Hajiya na warke Kinga babu abinda yake damuna yanzu.

Kallon ta Hajiya tayi cikin nuna farin ciki tace,"alhamdullahi alhamdullahi ALLAH na Nagode maka yanzu shikenan sai gida?

Nod dakai kawai tayi ta cigaba da shirya kayan ta..koda Dr yazo shima sosai yayi mamakin ganin A'isha ta warke.hamdala kawai yayi ya sallame su .duk da kuwa zuciyar sa tana cike da soda ƙaunar aisha.

****

Suna komawa gida bayan sun huta sunci abinci A'isha ta riƙe hannun Hajiya cikin nuna tsantsar biyyaya tace,"Hajiya wata alfarma nazo nima a gunki kuma don ALLAH Karki hanani kuma Karki tambaye Ni dalili, Amma ki sani amincewar ki shine kawai zai samar da farin ciki a cikin rayuwa ta.

Kallon ta Hajiya take cike da mamaki tace," shi wannan alfarmar da kike nima aisha ta Mecece?

Gyara zama tayi tace,"Hajiya inaso in koma makaranta, sannan ba ana nake son karasawa ba,so nake ki turani Jigawa gurin inna larai .kuma bana so kowa yasan inda nake duk wanda ya tambaya ni  kice masa na tafi garin su Abba .

Da mamaki take kallon ta buɗe baki tayi da niyyar tambayar ta..cikin sauri tace,"Hajiya munyi alƙawarin bazaki tambaye Ni dalili ba.

Shiru Hajiya tayi,can tace,"shikenan ALLAH yasa haka shine mafi alkairi.

Cike da murna A'isha ta rungume Hajiya.. washa gari tunda sanyin safiya A'isha ta bar garin Abuja..

Sosai hakan yasa taji damuwar ta kashe ɗari talatin ya ragu.

Koda ta tafi can dama babu waya a hannun ta.siya tayi ta canza layi ta kira Hajiya dashi..

*******

*AJMAL* kuwa samun ummin sa yayi ya faɗa mata yana son zuwa Kaduna domin duba jikin mahaifin haidar.jinjina lamarin tayi domin kuwa tasan  babu inda abban sa ya tsana ya tafi irin Kaduna .duk da kuwa akwai danginsa agarin..

Kallon sa tayi tace,"amma kaima kasan abban ka ba yarda zai yi bako? Shiru yayi can ya ɗago kai yace,"ummi nasan cewar Abba bazai yarda ba.saidai abinda kowa ya sani ne,babu yanda za'ayi a kunna fitila saidai maƙunni .saboda haka a gare Ni kece maƙunni Abba.don ALLAH ummi kiyi masa magana...

Murmushi tayi tace,"Tom  zanyi masa magana amma idan ka tafi ka daɗe wallahi duk abinda yayi maka babu ruwa na. Murmushi yayi yace,"in Sha ALLAH.

Sake kallon sa tayi tace,"ƴauwa dama kuwa inaso muyi magana.

Gyara zama *AJMAL* yayi yace,"ina sauraron ki ummi.

"Shin yarinyar daka tura a nima maka auran ta tun yaushe kuka haɗu Ni bansani ba?

Murmushi yayi yace,"naso na faɗa miki ummi amma nayi shiru ganin lokacin bamu gama fahimtar juna koba.

"Ita ɗin ƴar asalin inace?

"Su ƴan asalin garin Yola ne.aiki yakai mahaifinta Abuja .

"Shin ka yarda da tarbiyyar tane?

Sunkuyar da kansa ƙasa yayi yace,"na yarda da tarbiyyar ta ummi domin kuwa hakan nema yasa na zaɓe ta cikin daruruwan matan dake bibiya ta. Wannan nida kaina na ganta,sosai nake sonta ummi.

Ƙaramar pillow dake hannun ta ta jefe shi dashi cikin wasa tana cewa,"kaji ja'irin yaro nina tambaye ka wannan ne?

Dariya yayi yace,"ameen afuwa ummi..tashi yayi ya nufi ɓangaren sa cike da farin ciki.

*******
Hajiya ce zaune gabaki ɗaya kewar A'isha ke cinta,sallamar da *ISMAT* tayi shiya dawo da ita daga duniyar tunanin ƴarta data shilla.

Da fara'a Hajiya ta amsa mata bayan sun gaisa take tambayar ta aisha. Da mamaki Hajiya tace ,"wai bata faɗa miki zatayi tafiya ba? Girgiza kai *ISMAT* tayi alamar a a." Amma dai kam nayi mamaki ai..tunawa da alƙawarin da tayi wa A'isha yasa ta canza akalar zancan tace,"ai kuwa dai babu zato babu tsammani dangin mahaifinta suka ce suna da ɓuƙatar tazo tayi musu ɗan watanni saboda a saba da juna da sauran yaran .kinsan tunda mahaifinta ya rasu sau biyu kawai ta tafi can.

Wani irin yanayi *ISMAT* taji ya ziyarce ta tabbas tana son yarda da maganar Hajiya saidai kuma wani bangare yana nuna rashin yarda da zancan.kwata kwata yaushe aka sallami A'isha daga asibiti har ace ta tafi..ɗago kai tayi tace,"Hajiya wani gari ta tafi. Haka nan kawai Hajiya ta tsance kanta da cewa jos.da mamaki take kallon ta don kuwa tasan A'isha basa da wani dangi a jos.."Hajiya ki bani number da kuke waya wanda nake dashi sam bata zuwa.

Muskutawa Hajiya tayi tace,"ƴannan tunda A'isha tabar garin nan har yanzu nida ita ba  muyi  waya ba.saboda wayar ta ta samu Matsala.kuma kin san yanda al'adar Fulani take sam bana da ƴancin kiran ɗaya daga cikin su nace a bawa A'isha waya.amma in Sha ALLAH nasan tana siyan wani wayan zata kira ni dashi.ni kuma zan tura miki dashi ko kuma nasa ita ta kira ki.

Wasu irin hawaye Masu zafin gaske ne suka shiga zarya a kuncin ta.shikenan hasashan da take ya tabbata.shikenan A'isha tayi nisa da ita ,share hawayen ta tayi tace,"shikenan Hajiya ina sauraron ki .

"Tom madalla ki gaida umman taku.

"Zataji in Sha ALLAH.

Haka ta fita daga gidan tana jin wani irin jiri na ɗiban ta. ....

******
A'isha kuwa kuda Hajiya ta faɗa mata yanda sukayi da *ISMAT* sosai taji babu daɗi saidai sanin cewar wannan hanyar itace kawai mafita yasa ta share batun, kuma ta kara jaddadawa Hajiya kin bawa *ISMAT* number ta

*Wai Ni kuwa me A'isha take shirin aikatawa ne? "Shin menene dalilin daya sa daddy baya so *AJMAL* ya rinƙa zuwa Kaduna? Ku biyu Ni domin jin yanda zata kasance*

ISMATWhere stories live. Discover now