Page 33 and 34

2.6K 101 27
                                    

*💫SHINNING STARS WRITERS ASSOCIATION*

'''The more we shine bright the more we educate and enlighten our readers.'''

https://m.facebook.com/110896360504039/photos/a.110896457170696/110898470503828/?type=3&source=45

🍇🍇🍇 *UNCLE DATTI*🍇🍇🍇.
                 '''JIKINA YAKE SO!'''
         

               *WRITER OF*
*1.MAGANIN MATA(DAMUWA)*
*2.WAYE MACUCI?*
*3.RAYUWAR SUMAYYA*
*4.UNCLE DATTI(JIKINA YAKE SO)!*
             
                            ©
                      *eedatou✍🏻*
'''Follow and ✅ote me on Wattpad''': *eedatou*   

~Comments d'inku na jiya sun rikirkitana ni, wannan page kyauta ne na ware ma dukkan masoyana💘💘~

                     3️⃣3️⃣—3️⃣4️⃣

Tana cikin wannan tunanin taji an dafata kafad'an ta ta baya, ko ba'a a fad'a mata ba ta san cewa Inna ce, fuskarta tafffffff da hawaye ta juyo tana kallon ta, hanken da ke gauraye da illahirin parlourn ne ya Inna ta fahimci halin da take ciki".
          Girgiza mata kai Inna tayi alamar kar tayi kuka amma ina kuka ya kwace mata ta shige jikin Inna tana sheshek'ar kuka". Ummana Inna, ina so na ganta na san a duk inda take hankalin ta a matuk'ar tashe yake, idan zanyi fushi da kowa bazan iya yi da ita ba".
            Bayan ta Inna ta hau bugawa cikin hikima tana zancen zuci, ita kanta zata so ace an sada yarinyar nan da mahaifan ta amma ganin yanda Ammjntacce ya fice da kuma yanayin Nana ya tabbatar mata da cewa bai ammince da bukatar Nanar ba".
         "Kiyi hakuri kici gaba da zama damu Nana Allah shi yasan nufin hakan, idan da rabo wata rana zaki koma ga iyayen ki".
            Sai da ta ci kuka son ranta kafin ta share hawaye ta dubi inna cikin kuncin zuciya tace" Don Allah a wani gari nake yanzu? "Hmmm Nana ba hurumi na bane na fad'a miki garin da kike, ni dai aikina a nan na baki dukkan kulawan da kike bukata".
         Zata kuma yin wata tambayar Inna ta ja hannun ta da sauri muje ki kwanta dare ya fara nisa", ba dan ranta ya so ba tabi bayan ta suka shige d'akin ta.
         Makeken gadon ta ta hau ta kwanta Inna ta d'auko bargo ta rufa ta dashi kasancewar hunturu ne ana sanyi sosai  yasa tayi hakan cuz bata son sanyi ya cutar da lafiyan ta", ta koma ta zaune a gefen gadon tana mata hira can kuma  barci ya fara d'aukan ta tana gyangyad'i
          Sai tausayin ta ya kama Nana ta san cewa duk dan tsaron lafiyar ta take yi, cikin hikima ta lumshe idanuwan kamar mai barci komai ne yasa ta hakan ba sai dai dan ta ba ma Inna damar da zata je ta kwanta tayi barci, bayan haka itama kanta Nanar tana bukatar kad'aici".
              Inna dai na nan a haka idan ta gyangyad'a sai ta bud'e ido, da dai taga alamar barci ya d'auke Nanar tayi mata addu'ar barci ta fita tare da rufa mata k'ofa, ta nufi d'akin ta ta kwanta ta hau sharara barci abin ta.
       B'angaren Nana tana ganin Inna ta bar d'akin ta mik'e a hankali ta zira k'afarta ta a k'asa ta taso a hankali tana takawa taje jikin tagar d'akin tana lek'awa, dan k'arfin hali duk da tana jin sanyi na ratsa ta, jikin ta na  rawar sanyi  kattt katttt katttt bata yi yunk'urin kare kanta ba ko tsoron dare bata ji ba balle taji darrrrr a ziciyan ta ta fara tunanin kar tayi gamo......ance tsananin bakin ciki na cire tsoro idan mutum yaji tsoro to bai had'u da bakin ciki bane tabass hakan ya faru ga Nana a wannan lokacin."
           Hawaye ne masu uban dumi suka hau zubowa ta kasa tsaida su  zuciyan ta falllll cike take da tunanin........tayi dana sani mai tarin yawa na ba ma Datti kanta da tayi, duk da dai ta san cewa a lokacin bata da wata cikakkiyar wayo amma duk da hakan sai da taji haushi da zafin  kanta na sakin jiki da tayi da tayi da shi sosai, ta bashi damar da zai sarrafa ta ya driving d'inta to his test".
           Tsiraren hawaye suka sake yankoma mata da ta tuna da Auntyn ta Aina, wata k'ila alhakin ta cin amanar da tayi mata ne yake binta gashi nan an killace ta a gida da bata san ko na wanene ba bata da damar fita". Kaiiiiii ba zai yihu ba ko ta halin yaya sai ta nemo hanyar guduwa baza ta ci gaba da zama a gidan shi ba cuz bata san wani irin buri yake so ya cimma akanta ba".
          Wannan dare ko runtsawa Nana bata yi ba banda aikin kuka babu abunda take yi har sai da taji kanta ya fara yi mata ciwo kafin nan ta hak'ura ta koma ta kwanta.
          Da safe bayan ta idar da sallah ta nufi d'akin Inna har kasa ta tsuguna ta gaishe ta ta amsa mata".
          Tana lura da yanda fuskar Nanar yayi luhu-luhu alamar taci kuka sosai daren jira, Inna ta d'an had'e rai tace wato baza ki hakura ki saka wa kan ki salama ba? Yanzu haka kike so ki ta zama kina kuka? Gaskiya idan kina haka baza mu shirya ba tsammm banji dad'in haka ba sai ki saka na fara zargin cewa da wani abu da nake miki wanda bakya so amma kin kasa fad'a".
           "Ganin yanda ranta ya fara baci ta hau fad'a sai ta hau bata hak'uri tare da yi mata alkawarin baza ta sake yin kukan ba".

UNCLE DATTIWhere stories live. Discover now