Page 37 and 38

2.3K 76 14
                                    

*💫SHINNING STARS WRITERS ASSOCIATION*

'''The more we shine bright the more we educate and enlighten our readers.'''

https://m.facebook.com/110896360504039/photos/a.110896457170696/110898470503828/?type=3&source=45

🍇🍇🍇 *UNCLE DATTI*🍇🍇🍇.
                 '''JIKINA YAKE SO!'''
         

               *WRITER OF*
*1.MAGANIN MATA(DAMUWA)*
*2.WAYE MACUCI?*
*3.RAYUWAR SUMAYYA*
*4.UNCLE DATTI(JIKINA YAKE SO)!*
             
                            ©
                      *eedatou✍🏻*
'''Follow and ✅ote me on Wattpad''': *eedatou*   

                     3️⃣7️⃣—3️⃣8️⃣

Juyowan da zaiyi tayi ido hud'u da shi.......ido waje ta zaro dan ganin wannan mutumin ne amma samm zuciyar ta ta kasa yarda da shi............., sai ido take bin shi da shi ba tare da tace komai ba, kamar kullum murmushi ya sakar mata tare da k'awar da kanshi suka ci gaba da hira da Inna.
         "Hawaye ne ya cicciko mata a idanuwan ta.........menene kuddurin da yake da shi akan ta da zai tsare ta na, juyowa tayi da sauri zata bar wajen Inna tace" ina kuma zaki y'ata koma ki zauna ".
         Bata son da da ita ba shiri ta samo guri ta zauna ta k'asan ido take fuskar shi, tana so ta gano wani abu game da shi.
           Sai take ganin kamar da ban-banci tsakanin fuskar da take gani a duhu..........lallai Amintacce yana wahalar da zuciyan ta wajen gano ko shi d'in wanene and she can't tress him.
          Da wanan tunan har ya bar gidan ba tare da ta sani ba.
          Inna na zaune taji barci ya fara d'aukan ta tace wa Nana ta taso suje su kwanta, sai a sannan ne ta dawo daga rakiyar tunanin da take, jiki a sanyaye ta shige d'aki ta kwanta itama Inna tayi nata d'akin.
           B'angaren Inna tana shigowa d'akin taji wayan ta na ringing a samar drawer tayi sauri ta picking ta manna wayar a kunnen ta, suka gaisa da juna".
         " Yaya amanata Inna da fatan kina kular min da ita? 
       "Ehhhh gwargwadon iyawata ina yi sai dai fa yarinyar har yanzu bata hak'ura da batunta na komawa gida ba, baka ganin ya dace ace ta koma gida?
            " Uhmmmmmm ya fad'a cikin muryar shi mai dad'in sauraro, har yanzu ba'a kai matakin da zata koma ba........burin nawa bai gama cika ba amma saura k'iris".
        D'oguwar ajiyar zuciya taja ta sauk'e a hankali............to amma ya kamata ace ka bayyana mata kanka......ina tunanin ta fara zargin wani abu...........,ka san bana ta tashi hankalin ta saboda kar abun ya shafi juna biyun ta...........
            "Wani irin abu yaji ya daki zuciyan shi mai kama da mashi dan jin ta ambaci sunan ciki..........shikenan Inna zan duba na gani ki d'an bani lokaci kad'an kafin nan na gama cimma burina".
         " Uhmmm, shikenan tunda kace haka......Allah ya taimaka ya bada sa'a ina yi maka addu'ar cimma burin ka".
         "Ameen, Ameen inna na gode, daga nan suka yi sallama ya kashe wayan.
        
            Tunani ya dumiya a ciki she ma kanshi bashi da piece of mind akan killace ta da yayi but bai da option than yayi hakan..........., waya ya d'auka ya dailing wata number ya manna a kunnen shi daga d'ayan b'angaren aka d'aga."
         "Har yanzu baka kai gida bane naji kamar kana tuk'i ne?
       " Yeah of course amma saura kirissss.
      "Owk..... Owk.....to yaya mission d'in?
        "Dariya yayi a dai-dai lokacin da ya k'arya steering motar ya shawo kwana," gaskiya mutumina kwakwalwar ka na jaaaaa ban yi zaton yarinyar nan zata yi saurin gano wani abu ba sai yanzu.........., ya bashi labarin yanda ta tarar da shi a parlour ".
           " Ajiyar zuciya mai nauyi ya sauk'e tare da gyara kwanciyar shi a kujerar da ke babban parlourn gidan su yace" dama na san dole za'a rina shi yasa tun farko na shirya hakan".
           Basu wani dad'e da wayan ba suka yi sallama da juna........., daren ranar da tunanin yarinyar ya kwana ga uban zafi da ranshi ke yi mishi........, abubuwa da yawa sun saka shi a gaba sun hana zuciyan shi sakat.
          B'angaren Inna kuwa bayan ta gama waya da mutumin taji an bud'e k'ofa an shigo........, Nana ce ta tsaya daga bakin k'ofa ta jingina bayan ta da jikin k'ofan hawaye na bin bayan fuskar ta d'aya bayan d'aya, da alama taji duk abunda suke fad'a cuz a hansfree wayar take.
       Jikin ta ne yayi mugun sanyi ta taso da sauri tayi wurin ta zata lallashe ta Nana ta ja jikin ta da sauri cikin kuka tace" Irin zamar da zamuyi da ke kenan? Ashe dama kina sane da komai kike b'oye min.........da na d'auka ke mai tausayina ne amma yanzu na gano cewa da had'in bakin ki ake so a cimma buri a kaina........kuka ne ya ci k'arfin ta tayi shiru tana sheshshekar kuka.......laifin ta ne da ta yarda da da ita tun farkon zuwan ta gidan har take bata girma ta d'auke ta a matsayin dangin ta duk da dai ta san cewa bata tab'a ganin ta ba sai a gidan amma haka ta ammince da ita.
         Zuciyar Inna ya karaya sosai da jin kalaman yarinyar" Ba cutar da ke zamu yi ba ki yarda da dukkanin abubuwan da nake fad'a miki..........,
            Cike da takaicin maganar Nana ta juyo ta dube ta" ta yaya zan k'ara yarda da ke bayan da had'in bakin ki aka b'oye min ainihin fuskar Ammintacce da kuma hujjar zamana a gidan nan tare da ku?
          "Na sani ni mai laifi ne a gare ki amma ki daura ki dubi magana ta da fuskar fahimta.........
       Ba zan tab'a fahimtar ku ba har a bada........., barin d'akin tayi ta koma nata da sauri ta fad'a saman bed ta shiga rusar kuka kamar ranta zai fita............, abu ta tuno da sauri ta mik'e da sauri ta d'ago rigar ta tana shafa cikin ta...........da gaske ne baby ne a ciki d'ina?
        Is it true that baby d'in nan na Uncle d'ina bai zube be?
        " me yasa Inna bata fad'a mata cewa cikin ta bai zube ba bayan ta sani.............
           Kuka ne mai tsananin k'arfin gaske ya kwace mata na tunawa da rayuwar da suka yi da Datti" ya treating d'inta kamar k'are, ya maida ta kamar jujin shi, ya maida ta tamk'ar rigiya a duk sanda yake bukatar ruwa ya zira gugan shi ciki ya d'iba............, at the end da ya d'irka mata ciki sai ya manta da irin rayuwar da suka yi a baya, at yayi yunkurin zubar mata da cikin............, hawaye mai uban d'umi ta ya sake bin kyakkyawar fuskar ta tana shafa cikin tace" baby d'ina dady d'inka baya son mu? Ya maida mu useless, he tried to murder us.
          Idan na haifo ka ka fito duniya kar ka d'auki irin halin mahaifin ka.........,kar ka kasance cikin jintsin maza marasa sha'awan mata like daddy d'inka...........bana son halin mahaifin ka ya shafe ka..............bana so ka taso da halin akuyanci irin na mahaifin ka............cuz idan ka taso da hakan zaka zamo mutum mugu mai son kanshi..........zaka yi cuta irin na mahaifin ka..........., promise me cewa idan ka fito duniya ka zamo mutum kamar kowa baza ka aikata abunda mahaifin ka ya aikata ba.............,abun da ke cikin ne ya fara motsawa kamar yana jin ta.........murmushin mai d'auke da hawaye ya subuce mata ta ta sauk'e rigar ta koma ta kwanta..........tana mai ci gaba da kukan ta.......ta ko ina bata da sauki ga matsalar da Datti ya jefa ta a ciki ga kuma Ammintacce da saboda bakar kudurin shi ya ki barin ta ta tafi gida.
         Cikin kwanakin ta d'aga hankalin ta sosai kullum cikin d'aki take bata saukowa sai idan yunwa ya addabe ta kafin nan ta nemo abinci taci ta koma. Inna ta damu sosai da wannan sauyi na ta sammm bata jin dad'in hakan domin Nanar bata tab'a bari su had'u ko da kuwa sun had'u bata bata mata maganar har ta gama abunda ya kawo ta ta koma d'aki.
            A lokacin tsananin kewan gida na kama ta idan ta tuna sai tayi ta shafar cikin ta tana kuka shine kad'ai abunda yake saka ta jin sauki a halin yanzu.
          Shima kanshi Amintacce bai ji dad'in hukumcin da Nana ta d'auka ba.........,hakan ya sa ya gane cewa duk rubutun da yake bata bata karantawa........., da ace tana karantawa da ba zata d'aga hankalin ta ba........da zata fahimci asalin kuddurin shi na yi hakan......cuz yayi rubutun ne ta yanda zata gane ko waye shi da kuma kuddurin da da dalilin kin bayyana mata fuskar shi da yayi........
          Wata rana da ya shigo gidan da rana ya haye sama daga bakin k'ofa ya tsaya yana mata magana da tattausar muryar shi wanda kusan kullum kamar ana k'ara mishi zaki yace" ko da sau d'aya kin yi tunanin bud'e takardun nan da na baki kin karanta?
         "Ko wace takarda da dalilin rubuto ta me yasa baki bud'e kin ji hojjojin da na rubuto ciki ba.......,
         " Sheshekar kukan ta ya jiyo ba shiri ya runtse ido, da ta san me yake ji a ranshi da ta hak'ura da kukan nata".
       Mik'ewa tayi daga kwancen da take ta tako har bakin k'ofa ta tsaya........baka da wani hujjar da zaka ajiye ni a nan, idan har zaka iya rubuto min takarda kamar yanda ka fad'a na tabbata babu abunda zai hana ka bayyana min kanka".
         Bana bukatar karanta komai ka rik'e hujjarka kuma ka ci gaba da b'oye kanka, sai ta durgusa a k'asa tare da jingina bayan ta a jikin murfin k'ofa ta saki wani irin malalacin kuka mai tsuma rai.
        Wani irin kuka yaji ya kwato mishi ya hau rerawa ya hau bugun k'ofan, muryar shi na breaking yace" kar kiyi saurin yanke hukunci akan akan abunda baki sani ba..........takardar nan shine sirrin duk wani abunda kike so ki sani game da ni...........
             "Dakata malam ba zan bud'e ba nace.....ka barni na tafi gida na gaji da wahalar da ni da kake yi. Suna cikin hakan ne yaji an dago shi ta baya..........Inna ce ta fito daga d'aki zata lek'a ko Nana ta fito parlour sai taji muryar Amintacce na kuka........., shine ta hauro taji menene ya faru.........
          Jikin ta ya mutu sosai da ta ga shi a hakan abune mai matukar wahala ka ga namiji yana kuka wi-wi da hawayen shi sai gaji Amintacce yana yi.
          "Muryar shi taji tana cewa" Inna kin gani kuka take yi kice mata ta daina bana so?
           Takardar da na rubuto mata ma tace baza ta karanta ba yaya tace so na saka raina?
         "Ni na fita jin zafin killace ta dani amma dole ce ta sa babu yanda na iya............
             " Shiru Inna tayi sunyi matuk'ar bata tausayi sosai daga shi har ita Nanar..........
         "Ban ga laifin ta ba dan tak'i bud'ewa kamata ka janye maganar burin da kake son cikawa ka fito mata ido da ido ta san komai game da kaiiiii.
           "Hawaye mai uban d'umi ya matsa" Shikenan  Inna yanzun nan zata san ko ni waye kuma a yau d'in nan zan zata koma ga iyayen ta ko da kuwa burina bai gama cika ba amma Alhamdulillah ko a haka ma ya wadatar..........bud'e ki ganni a yau zan bayyana miki kaina.
         Tana jin su kuka yaci k'arfin ta she cried bitterly, da dishashshiyar muryar ta tace" bana son ganin fake fuskar ka da a kullum kake yaudara na dashi cewa fuskar Amintacce ne bayan ba hakan bane............,
          "I hate to see your face........na gaji da yaudara da zulumin da kake barina da shi a duk lokacin da nayi arba da fuskar ka............., kuka ta kuma sakewa har tana shid'ewa.
          "Billahil Azeen nine Amintacce ba da fuskar da kika saba ganina zaki ganni ba........i bet you yau na shirya bayyana miki furkar da ya dad'e yana b'oye miki.......bud'e ki gani nana nine...........,
         "Enough please!!! tayi sarin katse shi cikin kuka,  na gaji da jin yaudarar ka please let me be.........duk ka bi ka hana zuciya ta sakattttt ko da yaushe cikin fargaba take, i don't want to see you.......i hate you most.
          Maganar ta ta k'arshe yayi mishi zafi da yawa........ba tare da ya furta komai ba ya sa kai ya fita daga gidan Inna har waje ta bishi tana kwala mishi k'ira amma ko tsayawa bai yi ba.
         Mota ya shiga da uban gudu ya ke jan ta kamar zai tashi sama sai da yayi tafiya mai nisa kafin ya parking ba tare da ya fito ba ya fiddo dawa ya dailing wani number.........daga d'aya b'angaren aka d'aga tare da sallama", maimakon yaji an amsa mishi sai ma jin sautin sheshshek'ar kukan shi, da mugun mamaki yace" Subahanalillah! Me ya same ka kake kuka? Waittttt tell me please, duk a rikice yake maganar".
         "Ina son mission d'in nan ya k'are daga yau.......daga yau, yarinyar tana bani matsala sosai ban jin zamu d'ore a hakan".
       Doguwar ajiyar zuciya ya saki yana sauraran shi har sai da ya gama kafin nan yace" tun farko sai da na warning d'inka akan wannan plan d'in, ni ban ga dalilin da yasa baka so ka yi ido hud'u da ita ba...........yanzu yaya kake ganin za'a ending mission d'in?
          "I really don't know, har yanzu burina bai gama cika ba........, ka san for how long na d'auka nake neman hanyar da zan cika burina?
      Ya gyad'a kai kamar dama yana ganin shi.
       " You won't know ni kad'ai na san irin adadin lokacin da na d'auna ana zaman jira.
          "Ka ending wannan plan d'inka please ni kaina wallahi k'arfin hali kawai nake yi a duk sanda na je mata a matsayin kaine, sometimes tausayin ta har kusan saka ni kuka yake yi, tana narkar min da zuciya musamman da cikin ta ya fara tsufa d'in nan".
          Da haka suka yi sallama ya koma gida ya kwanta da tunanin kala-kala a ranshi....that night he cried bitterly har sai da hawaye suka k'afe mishi a ido".
         Bayan kwana biyu abubuwa sun dad'e cunkushewa wa Amintacce duk sanda ya so ya so ya shawo kan matsalar abu ya ci tura, a duk sanda ya shigo digan sai ya haura d'akin Nana ta bud'e amma ta k'i bud'ewa hakan zai koma cikin k'unan rai. Inna ma tayi nata iyakan k'ok'arin amma duk da haka still Nana tana nan akan bakan ta........, yanzu kam ma idan zata sauk'o sai ta tabbatar babu kowa a parlourn kafin ta fito tana gama abunda zata yi ta koma ciki........., haka zata zauna ta saka cikin a gaba tana kuka she knows that babu k'ofan guduwa daga gidan cuz akwai tsaro na musamman da aka yi ma duka k'ofofin gidan.
        Yau ma kamar kullum tana d'aki tana kwance taji haka kawai tana so ta watsa ruwa rabuwan ta da wanka har ta manta, mik'ewa tayi ta sauko ta nufi ban d'aki ta had'a ruwan wanka ta tayi tana gamawa ta fito ta d'au rigar ta zata saka taji yak'i shiga........kusan kala goma ta duba duk sun ki shigan ta kawai sai ta sa kuka..........ta hau dube-dube ko zata yi sa'a ta samo wanda zai yi mata dai-dai bata samu ba haka ta hak'ura ta maida wanda ta cire sai hawaye take yi cuz kayan sosai yake tashi da tsami.
        Tunanin yanda rayuwa ta sauya mata.....da dai yar gata ce ummin ta na ji da ita haka Uncle d'inta Datti daga baya komai ya cakude mata ta fad'a k'azamar rayuwa.
          Datti ya cuce ta da ya jefa ta cikin tsaka mai wuya Amintacce kuma ya zalumce ta da ya killace ta a guri d'aya ya barta tana azaftuwa da rashin iyayen ta. Ta sani sune silar jefa ta cikin wannan halin amma duk da haka tana jin son su a ranta she knows that suma sunyi kewan ta da yawa kamar yanda ta ke jin nasu.
          B'angaren Datti kuwa yana nan a sume a wajen bai kuma sanin inda kanshi yake ba sai wajen goma da rabi na dare shi d'in ma uban sanyin hunturu da ke busowa cikin d'akin ne ya dawo da shi cikin hayyacin shi.
          A hankali ya bud'e ido yana gama bud'ewa ya ga jikin shi ko kaya babu sai a sannan ne ya mik'e ya lalumi kayan shi ya saka........cikin ta d'an fad'a mishi ba laifi tunda har yana iya takawa.
        Amma ba wai ya daina jin feelings d'in bane kwata-kwata.
           Komawa yayi ya kwanta kwanta.........sai yaji gaban shi kamar an sa mishi peper ya zaro shi da sauri yana matse ido yayin da zafi ke ratsa shi a take jikin shi yayi zafi rad'au.
        Hankalin shi yayi matuk'ar tashi na ganin yanda wurin ya koma, shi dai ya gamu da jarrabawar rayuwa yana tunanin ya fita daga wannan sai ga wani kuma ya dawo, hawaye ne ya gangaro mishi mai uban d'umi duk muguwar jarabar shi ce ta jawo mishi hakan. Maida bananar shi yayi cikin wando yana maida kwallar azabar raddin zafi.......yayin da hawaye sabobbi suka hau bin fuskar shi............., cikin daren ya k'ira mumber d'in Usman ya hau jero mishi abun da ke faruwa cikin kuka mai tsanani.
          Shima kan shi Usman d'in ya tsorata matuk'a da lamarin Datti........, bai k'ara tsorata ba har sai da ya shigo gidan cikin sa'a kuwa Fu'ad na maib parlour a kwance yana jin muryar Usman ne ya taso ya bud'e mishi............, ko tsayawa baiyi ba ya haura site d'in Fu'ad da sauri,  shima Fu'ad na ganin haka yayi saurin komawa ya kwanta.......a yanayin Usman d'in ya shigo gida ya tabbatar mishi ba lafiya.......dole da akwai abunda yake faruwa da Datti.........to ko yaje ya duba shi ne.....ko ma dai menene yayi d'an uwan shi ne..........ba da son rashin bane yake keeping malice da shi.
          Mik'ewa yayi ranshi babu dad'i hayi hanyar d'akin da sauri........., da ya tuna cewa ba lallai ne su bari ya san abubuwan da suke b'oye mishi ba yana  kaiwa bakin k'ofan sai ya ja ya tsaya yana tunanin ya shiga ne ko karya shiga ..........
          B'angaren Usman bayan ya shigo d'akin sai ya tarar da abun da ya mugun d'aga mishi hankali.......a yanda ya zata ba hakan ya tarar ba  domin da ya bud'e dan ya duba sai ya gaban Datti yanda ka san sab'ule haka ya koma.
          "Salati ya doka a rikice yayi saurin rufewa yana maida kai gefe ya rutse ido da k'arfi he never expect cewa haka abun yayi tsananin...........ya dube shi" yace garin yaya hakan ta faru.......? Me kayi dick d'inka ya koma haka?........., Datti dai sai ido yake ta bin shi da shi hawaye na zubo mishi ya kasa controlling d'in su, hannu ya kai yana dungurar pillow d'in dashi Usman ya bi bayan shi da kallo to his greatest surprise sai ya ga k'atuwar rami fad'in shi ya kai k'aurin dick d'in Datti a jikin pillow, da mugun mamaki ya gwalala ido yana kallon Datti? Pillow ka ci?, gyad'a kai yayi alamar eehhhh.
          "Shiru Usman yayi yana tunani" wani irin caccaka yayi ma pillown da har dick d'in shi zai sauya halittan dick d'in shi..........
            Jikin dagon ya bi da kallo ya ga stain d'in jini ashe garin caccakar pillown dan jaraba  bai sani ba a lokacin har yana had'awa da jikin gado, shi dai a lokacin idanuwan shi a rufe suke bai da burin da ya wuce ya rabu da feelings d'in da ke damun shi.
           "Sai hawaye ya k'aryo ma Usman na tsananin tausayin abokin na shi........cuz he knows that he was suffering a lot.  Treating na wajen yayi yana ma mishi fad'a sosai ya dinga bin abun a hankali idan ba haka ba zai iya rasa ranshi......, Allah friend idan baka controlling kanka wata rana sai dai a tsinci gawan ka a d'aki........., k'arya murya yayi irin na wanda take cikin azaba yace" to yaya kake so nayi bacin baby ta tafi ta barni........?  Maganar sai ya bama  Usman tausayi  yace" daurewa zaka yi ka cire sha'awar nan a ranka........., sannan ka dinga azumi akai-akai shine dai shawara ta gare ka".............,
         *Usman don Allah kaci gaba da rik'e min sirrina..........bana son kowa ya sani.......daga ni sai kai sai Allahn da ya halicce mu.
         "Huci mai zafin gaske ya sake" gana ganin binne sirrin da muke yi shine solution na problems d'inga? Wallahi Datti na fara karaya da lamarin ka.............bana jin zan iya rik'e maka sirri".
         "Miyau mai d'aci ya had'iye zuciyan shi na mishi suya uba uba ga pain na dick d'in shi ya dame shi.........Usman ko mutuwa nayi bana kaunar su baba Babba su san abunda na aikata.........., jikina na bani rayuwana ba mai tsawo bane.........ko da bayan raina idan baby ta dawo kace ta yafe min abunda nayi mata.........,ba laifina bane da na kasance mai tsananin son na kusance ta............., zan mutu ne da ciwon son baba......., k'asa jurewa yayi da sauri ya rufe bakin shi yace" baza ka mutu ba.......da yardar Allah Nana zata dawo cikin rayuwar ka..........,
        Datti kam sai girgiza kai yake yi a zuciyan shi yana cewa" kayya!!!!!! bana jin zan kai har zuwa wannan lokacin da zanga baby ta dawo..........
          Bayan Usman ya gama dressing na wajen ya duba wristwatch d'in shi ya ga karfe goma sha d'aya na dare yayi saurin sallama da shi ya bar d'akin tare da tabbatar mishi cewa gobe idan zai dawo".
        Bud'e k'ofan da zaiyi ya ga Fu'ad tsaye a gurin hawaye na rolling a fuskar shi hakan ya sa ya tabbatar da cewa ya ji abunda suka fad'a........."
        From head to toe ya watsa mishi muguwar harara zuciyar na bashi kamar ya nemo wuk'a ya dab'a mishi.........amma sai ya dake yace" Usman  kai ba mosoyin Datti bane.......kai kububuwan macijine........., da ace kai aminine na kwaraiiii maimakon da ka jefa shi cikin wani hali hanya ya kama ta ka nemo yanda zaka yi ka ceto shi daga ramin da ka bada gudumawan ya fad'a ciki..........., kana ganin kayi mishi aldalci, kayi ma iyayen mu adalcin b'oye musu gaskiyar lamari?
          Kai butulu ne........kaci amanar amminci da abota.......kuma Allah ba zai barka ba.........., yana gama fad'a ya bangaji kafad'an shi ya wuce ya barshi tsaye baki bud'e galala yana bin bayan shi da kallo, da k'ar ya ja tsummokaran kafafuwan shi yayi gaba.
            B'angaren Fu'ad har inda Datti yake kwance ya tsaya a kan shi har yanzu hakayen basu d'aina saukowa akan fuskar shi ba shi hawaye Datti hawaye, k'arfin hali yayi yace" kai d'an uwana duk abunda kayi ba zan so ka kasance a hakan ba amma sai dai ka kasance mai kunnen kashi.......me ribar boye musu gaskiyan da kake yi?
            Datti ka rubuta ka ajiye zuma sai da wuta..........., yana gama fad'a ya koma parlour ya bar Datti da zancen zuci yana maimata k'almar "Zuma sai da wuta". K'almar ta tsaya mishi a rai sosai.
          Washe gari kamar yanda Usman yayi alkawari hakan ta kasance sai da ya biya ta gidan ya duba lafiyar shi kafin nan ya koma Office ya hau duba files d'in da ya tarar nurse ta kawo mishi baya ta aje saman table. Tun yana bud'ewa yana fahimtar me files d'in ke d'auke da shi tunanin maganganun da Fu'ad ya fad'a mishi daren jiya ya hau yawo a kan shi yana birkita mishi tunani.........daga  k'arshe ma kasa fahimtar komai yayi ba shiri ya rufe gaba d'ayan su ya maida inda ya d'auko su kana ya dunkula hannun shi yana tunani".
         "Gaskiyar Fu'ad ne bai rike abota da hannun biyu ba........babu abokin da zai yarda ya jefa abokin shi cikin rami maimakon ya samo shi ya fidda shi cikin ramin sai ma ya hau hakar kasa yana watsawa domin ya ciki ramin da yake ciki.........,
          Duk irin uban sanyin A\Cn da ke ratsa shi bai hana zufa ya k'aryo mishi ba ya ciro hanky a aljihun wandon shi yana gogewa.
         " Datti bai cancanci hakan daga gare shi ba........bayyanar sirrin shine iya adalcin da zai mishi ko da kuwa baya so , kuma ko da kuwa zai zamo k'arshen abotan su da shi kenan.
          Da wannan tunanin ya wuni a Office yana yi.

UNCLE DATTIWhere stories live. Discover now