[8/13, 4:18 PM] Nuceey luv😘: ® *OMAR* *KO* *FAROOQ* ❓
1_5
"Omar ko farooq samari kenan masu ji da kai, hade da bugun abujaa. 'Yan biyu ne wajen Alhaji Basheer da mummy'n su Hajia zainab. "Sun taso cikin gata da soyayyar mahaifan su, babu abinda suka nema suka rasa, saidai a kwaisu da rashin mutunci wulakan ta dan Adam a wajen su ba karamin Abu bane. "Tabbas wannan hali nasu yana damun mummy idan tayi magana daddyn su zaice ai yarane a barsu, a haka har suka sangarce, "idan akace batun kamanni mutun duk kwakwar sa bazai iya banbance su ba, wannan su ake kira da identical twins. Shiyasa idan daya yyi laifi toh da wuya a kama su, saidai duk a hadasu ayi maganin su wannan kuma abu ne me wahala sbd daddyn su ya tsaya mu, idan an tambayi daya zaice bashi bane haka nan dayan baka d wani shaida d zaka tabbatar da hakan.
"Idan muka koma bangaren kyau, tofah saidai ace masha Allah dogaye ne masu fadin qirji da fuskar su a kewaye Wanda yyi daidai da dara-daran idanun su masu matukar kyau tamkar masu jin bacci, hancin su kuwa dogo ne yyinda kasan sa akwai kewayeyyen pink lips. Sumar Kansu kuwa akwance take har wani sheki take habawa taji gyara. Omar shine babba yyinda farooq shine karami ma'ana hasan da hussaini.
Idan akace 'yan mata ba'a mgn toh tanan zaka iya banbantasu domin farooq akwai son 'yan mata yana chilling life dinsa, yyinda omar baima da lkcin ko wacce kucaka. Dariya bata damesu ba, dukda farooq yana kula 'yan mata bawai ko wacce jik and jak yake kulawa ba aa sai me class sanna su suke biyoshi bawai shike binsu ba.
"Yau kwana daya kenan da dawowar su daga india bayan kammala karatun su da sukayi, inda omar ya kanci harkar likitanci fannin operation, yyinda farooq ya dauki fannin duba matsalar data shafi mata (Gynecologist).
"Sai wajajen 11 suka shigo side din iyayen nasu, dake jiransu danyin breakfast. "Bayan sun gaisa daddy ya kallesu cike da murmushi. Mummy ma haka ganin twins dinta sun gama kr2. "Bayan sun kammala cin abincin daddy yyi gyaran murya kowa yyi shiru yana sauraren abinda zai ce....Nuceey luv😘
[8/13, 4:18 PM] Nuceey luv😘: ® *OMAR* *KO* *FAROOQ* ❓6-10
"Daddy yace toh Alhamdulillah tunda Allah ya kawo mu wannan lkcn da muka dade muna jira. "Abu na farko shine na Gina muku hospital naku me suna *OMAR* *FAROOQ* *SPECIALIST* *HOSPITAL* a tare twins din sukayi murmushi hakan ya tabbatar wa iyayen nasu sunji dadi kenan. "Daddy yace bayan nan kowa na Gina masa gida nan ma murmushin sukayi, "abu na karshe shine kowa inaso ya fito da Matar da zai aura, Amman Ku sani a tsarina banason Ku kwaso 'ya'yan talakawa hop kun gane....mummy tayi saurin kallon daddy bude baki tayi tace haba alhji talaka da me kudi duka mutum daya yyi su ai, kuma...daddy ya daga mata hannu enough plss, mummy na ganin haka taja bakin ta tayi shiru dan batason ja in ja da alhji gaban yaransu dan a ganin ta be dace ka dinga CeCe kuce a gaban yara ba.
"Daddy ya kalli twins yace hop kun gane, gaba1 suka gyada Kansu. "Ana suka tashi dan komawa side dinsu. "A hanya farooq yyi 'Yar dariya hakan yasa omar ya kalle shi yace lpy? "Farooq yace wai daddy ke zancen aure, omar yaja tsaki yace ai ko beyi ba kaikam kana bukatar aure, "farooq ya zaro ido yace haba bro. Nayi karami dayawa. "Omar ya tabe baki yace shi yasa kuma kke chilling da enmata koh, farooq ya Sosa qeya batare d yace komai ba, nan kowa ya shige dakinsa.
"Omar kwance kan gado yana tunanin abinda daddy yace shidai mgnr gsky be shirya aure yanxu ba, hasalima mata basa gaban sa shi a nasa tunanin bega abin burgewa a aure ba, dukda yanada enmatan dake nuna so gare hakan be tabajin a zuciyar sa mace ta birge shi ba, wasu ma zaton su ko farooq ne Amman d sunga ba fuska zasu gane omar ne, ajiyar zuciya ya saki yyinda ya tuno cewa daddy yace bayason su auri 'yan talaka wato kwarya tabi kwarya, murmushin yake yayi toh shi ko zaiyi aure ya rasa wacce zaiso sai masu warin kodaddan kaya?,god forbid masu kudin ma sai a slow, shi yasa Sam baya son dawowa naija sbd wannan mgnr auren yasan dole sai sunyi musu. Da wannan tunanin bacci ya sace shi.Nuceey luv😘
[8/13, 11:18 PM] Nuceey luv😘: ® *OMAR* *KO* *FAROOQ* ❓11_15
YOU ARE READING
OMAR KO FAROOQ?
General FictionOMAR KO FAROOQ? Dukkansu 'yan biyu ne masu matukar Kama daya Wanda ake Kira da identical twins, Kowanne su yanaji da matukar Izza da ji da kai tamkar wasu jinin sarauta, Sun taso ne cikin gata Wanda mafi rayuwar su sunyita ne a kasashen turai Hakan...