® *OMAR* *KO* *FAROO* ❓
76_77
"Omar kuwa yana fitowa a dakin daddy ya samu imaan a main falo tana kallon wani Indian film. Omar har zai wuce sai kuma ya dawo da baya ya rankwashi kan imaan, "imaan ba zato ba tsammani taji rankwashin har tsakiyar kanta. A razane ta juya tana kallon sa idon sa duk ya ciko d kwallah, "yah omar menayi maka dan Allah? Omar yace ban hanaki kallon Indian film ba? Imaan tace toh dannan kalla meye aciki? Omar ya zaro ido oh wato tmbyta kike miye aciki koh? Imaan tayi shiru, omar yace shikenan zan fadawa mummy kina koyon yanda kiss dan kiyi wa gateman, imaan ta zaro ido tace na shiga uku ya omar yaushe nace maka haka? Omar ya daga gira yana murmushi burinsa ya cika tunda ya sata kuka. "Imaan kuwa tashi tayi daga zaman da take ta kama rigar shi tace dan Allah ya omar karka Sanar wa mummy ni wlhy ban taba yima kowa kiss ba. "Omar yace kinaso na yadda? Imaan ta gyada kai, omar yace ohk biyoni, imaan tace toh. Haka tabishi kamar jela, side dinsa suka nufa, bayan sun shiga falon sa, yace jeki dakina ki gyara ki wanke toilet sannan kizo kiyi mopping, imaan ta kwalalo ido tace haba ya omar banyi maka komai ba fa, kawai ma shrrin k...da sauri omar ya kalleta yace sharri na miki. Tayi saurin girgiza kai, omar ya daka mata tsawa oya je kiyi abinda nace or na je na sanar mata, jiki a sabule ta tafi dakinsa tana mgn ciki2 Allah wannan yah omar din mugune, omar yace kikace me? Da sauri imaan ta qara saurin tafiyar ta fatan ta Allah yasa beji abinda tace ba. Shikuwa omar kallo ya kunna yana ganin news, "saida tasha wuya sosai kafin ta iya gyara gadon omar dan ma Allah ya sota, mummy tana koya mata badan haka ba ai da wuyar saitafi haka. "Saidai ta gama sannan ta komai toilet dinsa, komai tsaf2 yake a zuciyar ta tace mutum har mutum Amman sai mugunta data cika masa kwanya fisabilillahi meye abin gyara anan? Haka imaan ta cika kunfa a katon boket, sannan ta kwara duka toilet din, sannan ta Debi wani ruwan ta kwara haka tayi tayi har kumfan ya tafi, ganin haka ta lall6a ta fito a toilet din kadan ma ya rage santsi ya kwashe ta. "Falo ta tana haki, omar ta samu ya fara bcci, hamdala tayi sannan ta la6a6a tabar falon, tana fitowa ta tafi side din mummy a guje.
*****
Daddy ne ya tara su a falo yake sanar musu sun gama mgn d Abban amira zuwa nan d 2weeks za'a daura aure, mummy tace da wurwuri haka? Daddy yace toh me za'a jira ai idan akwai kudi sai ayi komai akan lkci basai an ja ba. Mummy tace Allah ya sanya Alkhairi daddy yace haka nakeson ji, "farooq dai yyi murna abinsa, shi kansa omar ya taya dan uwansa murna. Haka sukaci gaba da hirar su har farooq ya mike da nufin tafiya side dinsa dan kiran mutuniyar sa, Imaan CE ta tashi tabi bayansa, omar ma tashin yyi. "Lkcn da duk suka fita, mummy ta kalli daddy, tace alhji yanxu ya mgnr da mukayi ranar? Daddy ya hade girar sama data qasa yace zainab abinda ya Dade be kira ba kenan, yace tun muna shaida juna kada ki sake min wannan mgnr Sam banji zan iya ba, mummy ta sunkuyar da kanta tace Allah ya huci xuciyar ka banyi hakan dan 6ata maka raiba, Amman INA rokon ka da kasake tunani akai dan Allah, daddy ya 6ata rai batare d yace komai ba.
"Imaan har falon farooq ta nufa, saida suka zauna farooq yace my sisi yadai? Imaan ta 6ata rai tayi shiru. "Farooq da damuwa yace imaan yimin mgn mana. "Imaan ta fashe da kuka a rikice yace ya salam wani Abu aka miki? Imaan ta daga kai. Farooq yace waye? A hankali tace kaine ya farooq. "Farooq ya zaro ido yace ya salam menamiki? Imaan tace yah farooq ka daina sona gashi nan daddy yana mgnr auren ka da wata Amman bakace dani zakayi ba. "Dariya, mamaki, tausayi sukayi masa durar makiyiya a lkci daya, kwantar da murya yyi yace sorry my sis ba nufina haka ba, kinga yanzu kina Ss1 going to ss2 yaushe kika gama skul kikayi university kafin muyi aure? Ai kinada lbrin yanda daddy yace dole mu kawo mata a yanxu ko. "Imaan ta girgiza kai. "Farooq yace toh kiyi hakuri idan kika gama skul, a shekarar zamuyi aure, d gske? Ta tmbyeshi farooq yace yes, imaan sai alkcn ta saki ranta tana murmushi. "Shima farooq murmushin yyi yana me
YOU ARE READING
OMAR KO FAROOQ?
General FictionOMAR KO FAROOQ? Dukkansu 'yan biyu ne masu matukar Kama daya Wanda ake Kira da identical twins, Kowanne su yanaji da matukar Izza da ji da kai tamkar wasu jinin sarauta, Sun taso ne cikin gata Wanda mafi rayuwar su sunyita ne a kasashen turai Hakan...