® *OMAR* *KO* *FAROOQ* ❓
60_61
"Imaan ta 6ata rai sannan suka fara cin abinci.
"Omar yana wanka bayan ya gama ya fito, yana sa kafar sa a waje sai ji yyi suuuu ya zame, auchhh... Ya furta sosai ya bugu a qugu, rarrafa yyi bakin gado, cike da wuyar faduwar d yyi, duba wajen d ya zame yyi, ga mamakin sa sai yaga 6awon ayaba, sosai y shiga tunanin ta yanda akayi 6awon ayaba yazo har dakinsa. Shidai yasan ko cin ayaba baiyi ba, can ya shiga duniyar tunani, duk iya tunanin sa ya rasa ya akai 6awon ayaba yazo dakinsa, tunanin sa ya fara ga 'yan gidan duk Wanda ya tunano yasan bazai aikata ba, tunda yasan ko kusa farooq bazai sa masa ba toh aknme zai sa masa? Nan ya koma kan imaan, mwtss yaja tsaki har yaushe ya sakar mata fuska da zata shigo dakinsa? Harma tayi tunanin sa masa ayaba? Anan ya mike da kyar ya isa gaban mirror dake dakin sai kace mace sannan ya fara shiryawa har lkcn bai daina tunani ba ga azaba da qugun sa yake, shidai yasan ko mage basuda ita a gidan. Haka ya fito zuwa falon sa, mamaki ne ya isheshi ganin falon a bude ba kamar yanda ya barshi ba, tunanin sa ya tsaya cakk ko shakka babu lkcn da yake wanka yaji sallamar imaan, kenan itace tasa maka 6awon? Wata zuciyar ta tambaye shi a fili ya furta yesss yana me furzar da iska cike da 6acin rai tamkar yana magana d wani. Zuciyar sa CE ta fara zafi dan haka ya fice a falon ya isa side din mummy.
"Imaan ya tarad a dining tana tattare plate harsun gama cin abinci, tana ganin sa tayi saurin sunkuyar d kanta alamun rashin gsky ya tattara a wajen ta. "Hakan ya tabbatar wa omar abunda yake zargi. "Imaan baki na rawa tunda ta kalleshi sau daya ta tabbatar wa kanta tarkon ta ya danu. Tace good morning ya omar, ya omar yace mrng. A takaice., sannan yace ki kawo min abinci na falona, imaan tayi saurin dago kanta ta zaro ido a xuciyar ta tace kaddai ya gane nice nasa masa? Oh ya rabbi help me 🙄., omar yana ganin yanda kamannun ta suka canja yyi murmushin gefen baki Wanda d alama na mugunta ne, a zuciyar sa yace ashedai karamar marar kunya CE ke., batare d yace mata komai ba ya juya wajen mummy dake kallo ya gaishe ta a tsaitsaye suka gaisa d farooq a tsaitsaye sannan ya koma side dinsu.
"Imaan jiki ba kwari ta tattari abinda ya kamata ta jerasu cikin faranti sannan ta wuce side din omar. "A falo ta tarad shi yana kallon kwallo. "Tana shigowa omar ya mike ya sawa kofar key. Sannan ya dawo ya zauna duk abinda yake fuskar sa a tamke babu alamar wasa. "Imaan qirjinta ya bada damm, jiki na rawa tace gashi, bece mata kala ba, ganin haka ta mike da zummar tafiya, dagowa yyi ya watso mata wani kallo, take cikin imaan ya bada kulululuuuu ai batasan lkcn data zube a kasa ba. "Cikin dakilewar murya kamar bayason magana, yace ki zuba ruwan zafi a jug sannan kisa Lipton guda goma a ciki, imaan tace toh. "Bayan ta gama abinda yace, omar yace tashi kiyi kneel down. "Imaan ta zaro ido tace ya omar menayi kuma? "Omar yace tambaya ta kike? Tace eh menayi? Omar ya mike yace ohk bari kiga me kikayi, kunnen ta ya kama ya murda sosaiii har Sanda tayi kara Amman baiyi kokarin saki ba, imaan cikin kuka tace yi hakuri zanyi yanda kace, omar yyi murmushin mugunta sannan ya sake mata kanta. "Imaan tashi tayi sannan tayi kneeling, "bayan like 15mins suna zaman kurma, can omar yace dauko min wancan ruwan Lipton din, imaan ta mike da kyar dan kafafun ta sun fara tsami sannan ta dauko, omar yace toh shanye, "imaan a kidime tace yah omar kallifa babu sugar ga Lipton har goma ai yyi daci. "Omar ya sake hade rai batare d ya kalleta ba yace zakyi abinda nace ko saina tashi? "Imaan ta kafa bakinta kur6a daya tayi saurin cire kanta, tsabar daci ta kasa hadiyewa, tashi tayi da nufin zubar wa omar batare d ya kalleta ba yace zauna, imaan ta zauna, sannan yace hadiye abinda ke bakin ki. Imaan kamar tayi kuka ta runtse idon ta tafara hadiyewa, omar duk yana kallon ta ta gefen ido sai murmushin mugunta yake, "da kadan kadan saida yasa imaan ta shanye tasss cikin ta kamar zai fashe haka takeji. "Sai nishi take, omar yace tashi ki sakeyin kneeling, imaan na hawaye tayi abinda yace. Can yace ki daga hannun ki sama ki rufe idon ki, sannan ki bude bakin ki. Imaan tace dan Allah ya omar kayi hakuri. Omar yace hakuri? Ai bakiga komai ba tukun tunda ke Allah y yi ki muguwa, wannan duk mijin daya aureki ya auri azzaluma. Gaki karama dake Amman kinsan takan mugunta. "Imaan tace nidai dan Allah kayi hakuri bazan sake ba. "Omar yace kina bukatar wani ruwan Lipton din kenan. "Imaan ta jijjiga kai. "Omar yace toh kiyi abinda nace banason bata lkci. "Imaan na kuka tayi abinda omar ya sata.
"Omar tashi yyi daga inda yake zaune sannan shima ya 6allo ayaba daya ya cinye, sannan yasa a daidai bakin kofar fita. Dawowa yyi ya zauna abinsa ziciyar sa fari kall sa6anin da da yake a 6ace. "Saida imaan tayi kusan 20mins a haka sannan yace tashi. "Bayan ta tashi d kyar yace fice kiban waje. Dadi ya cika imaan ganin ya barta zata tafi harda cewa thank you. "Omar ya girgiza kai yana me cike da murmushin mugunta. "Imaan kuwa garin sauri taje bakin kofa kenan sai jinta tayi suuuuuuu.....Nuceey luv😘
YOU ARE READING
OMAR KO FAROOQ?
General FictionOMAR KO FAROOQ? Dukkansu 'yan biyu ne masu matukar Kama daya Wanda ake Kira da identical twins, Kowanne su yanaji da matukar Izza da ji da kai tamkar wasu jinin sarauta, Sun taso ne cikin gata Wanda mafi rayuwar su sunyita ne a kasashen turai Hakan...