® *OMAR KO FAROOQ* ❓
36_40
"Imaan tace, sunana Fatima abubakar, INA zaune a nan kano unguwar rijiyar lemo, mahaifina malam abubakar da umma ta Sadiya sunyi auren so da kauna asalin su 'yan Maiduguri ne wannan tashe tashen bom din yasa sukayi hijira suka dawo garin Kano da zama, inda mahaifina ya sai dan madaidaicin gida da sauran kudin dake gareshi, daga nan ya fara sana'ar saida kaji, da wannnan muke cikin rufin asiri, tun INA shekara 5 a duniya Allah yyi masa rasuwa, sosai ummata ta shiga wani hali na tashin hankali kasancewar ba kowa suke dashi a garin kano ba, haka dai ta fara sana'ar wankau makota su kawo mata ta wanke a haka take ci damu, nayi makaranta ta INA js3 yanxu haka kasancewar halin yau dukda ta gwamnati CE dole za'a bukaci wasu kudi a wajen mu dan zana takar dar j.s.c.e. "tun lkcin muke ta fafutuka Allah be bamu ikon hada kudin ba, bangaren islamiyya kam Alhamdulillah na kammala sauka ta, sai hadda da wasu littafai da nake yanxu... "Labarina na karshe shine mafi muni da rashin dadin ji, nan taja numfashi tare da matse hawayen da suka cika mata ido tun dazu. "Sannan tace, jiya INA wanke wanke..... Tass ta zayyane wa mummy abinda ya faru da ita jiya, da rashin mahaifiyar ta da tayi.
"Allah sarki mummy tace cike da tausayin imaan, tace gsky na tausaya miki sosai dukda mummy ta fahimci a hospital na yaranta abun ya faru, saidai taja bakinta tayi shiru. "Ta kalleta tace Imaan, imaan tace na'am. Mummy tace kin amince na maye miki gurbin Wanda kika rasa? Imaan ta zaro ido waje dan Abin mamaki ya bata tace ni kuma?, mummy tace eh, Imaan tayi kasa d kanta tana wasa d 'yan yatsun ta. "Mummy tayi murmushi tace tun lkcn Dana ganki sai naji hankali na ya kwanta d ke, tunda nake yarana biyu, gashi inason 'ya mace a rayuwa wa. Koda ace akwai iyayen ki a Raye daman zan nemi alfarmarsu su bani ke, Amman cikin ikon Allah saiga yarinya tazo har gida na. "Imaan tayi murmushi kawai. "Mummy tace daga yau mummy zaki dinga kirana ba baiwar Allah ba.. Ta karasa fada tana murmushi. "Imaan itama murmushin tayi kasan zuciyar ta cike da farinciki dan koda ta koma gida bata fa kowa, gashi batasan ma inane hanyar Maiduguri ba. "Kallon mummy tayi da murmushi tace banda bakin da zan gode miki mummy saidai nace Allah ya saka da Alkhairi. "Mummy tace ameen. Tashi kiyi sallolin da ake binki, imaan tace toh.
"Bayan ta idar ta koma jikin mirror nan ta sake fesa turare da simple make up, sannan ta fito waje kamar yanda mummy tace mata. "A falo ta tarad da mummy zaune tana kallo. Itama zama tayi a kasa. Mummy tace haba imaan tashi daga nan ki dawo nan. "Imaan ta mike ta koma inda mummy ta nuna mata kusa da ita. Ahaka suna hira jefi-jefi, can sukaji An bude kofar falon tare da sallama.
"Mummy ta kalle sa da murmushi tace tofah yau Kaine ka dawo da wuri haka? Farooq yyi murmushi yace kinsan nabar patient a gida ya kamata na duba ta. Mummy tace hakane, imaan na jinsu saidai hankalin ta na kan film din da take kallo. "Nan farooq yace mummy INA take? Mummy tayi masa nuni da ita, oh abinda ya fada kenan danshi tunda ya shigo hankalin sa be kai gareta ba. "Matso yyi kusa da ita,.. Yaga hankalin ta na kan Kallo yadan buga kujeran yana kallon ta. "Da sauri ta jiyo gareshi. "Tana ganin sa ta hade girar sama data kasa dan har abada bazata manta fuskar nan ba, fuskar da tayi sanadin mutuwar umman ta. "Take ta maida kallon ta wajen Mummy, mummy tana ganin haka ta kauda kai, tasan za a rina, haka ta fada a zuciyar ta.
"Imaan zata sunkuyar da kanta kenan sai sukaji an sake bude kofa, daga kanta tayi, tasss ta sauke manyan idanun ta cikin nasa bala-balan idon, a razane ta maida kallon ta ga farooq Wanda shima ya hade rai kamar yanda omar yyi sbd yaga yyi mata mgn tayi banza dashi shine ransa ya fara baci. "Ido imaan ta zaro ganin fuskoki masu kama daya, Wanda duk kwakwarta ta kasa tantance waye omar daga cikin su. "A zuciyar ta tace *OMAR KO FAROOQ*??? Wanne ne a cikin su yyi mata rashin mutunci???Nuceey luv😘
YOU ARE READING
OMAR KO FAROOQ?
Ficción GeneralOMAR KO FAROOQ? Dukkansu 'yan biyu ne masu matukar Kama daya Wanda ake Kira da identical twins, Kowanne su yanaji da matukar Izza da ji da kai tamkar wasu jinin sarauta, Sun taso ne cikin gata Wanda mafi rayuwar su sunyita ne a kasashen turai Hakan...