® *OMAR* *KO* *FAROOQ* ❓
74_75"Duk wani tunanin sa yarasa menene mafita. Qarshe tashi yyi daga kwanciyar side din omar ya nufa. "A falo ya tarad dashi. "Omar yana zaune kan kujera yana kallo. "Farooq ya qarasa da sallama sannan shima ya zauna yana kallo suna hirar su jefi2, can farooq yace bro wata shawara nakeson ka bani, omar ya tattara nutsuwar sa ga farooq yace INA jinka. "Faroiq yace kasan daddy ya matsa mana da zancen auren nan ko? Omar yace eh, farooq yace hala ka samu matar da zaka aura? Omar ya tabe baki yace kyale dadday ni ban shirya yanxu ba, farooq ya zaro ido yace sai yaushe kenan? Omar yace sai lkcn da nayi niyya. "Farooq ya girgiza kai yace kasan halin daddy fah kada ya kawo mana wasu matan Wanda ra'ayin mu baya wajen su. "Omar yace kaga malam idan auren nan zakayi kaje kayi danni ban shirya ba., bayan haka kaida kacemin na baka shawara meya kawo wannan zancen auren? Farooq yyi murmushi yace kwantar da hankalin ka, kasan shawarar da zaka bani? Omar yace saika fada. Yyi mgnr a takaice dan ya kosa yaji abinda zaice. "Farooq yace inason na auri _Imaan_ shin meka gani a kai? Whatttt.....ido wuru wuru omar ya zaro yana me kallon dan uwansa, can kuma ya kwashe da dariya yana nunashi da yatsa yace ah lallema bro, shin INA dukkannin 'yan matan ka suke? Masu ji da class? Manya dasu? Ka rasa wacce tunanin ka zai qare sai kan wannan tatsitsiyar yarinyar? Yaushe aka gama tsigeta daga shan nono?.... Farooq ya katse shi d fadin haba bro shawara nace ka bani bawai ka tsaya muzanta imaaa ba, omar da kyar ya tsaida dariyar d yake yace, kasan Allah wallahi ka cire zancen imaan a ranka dan Sam yarinyar nan ba class dinka bace, haba karka bamu kunya mana, kuma kasanme? Daddy bazai aminta da auren Ku ba kwatakwata sbd asalinsu bamasu hali bane, kaifa da kanka kke bani lbrin da kyar daddy ya amince da zaman yarinyar nan a gidan nan fah? Wallahi tun da sauran mutuncin ka wajen daddy ka janye wannan zancen inaga shawarar da zan baka kenan. "Farooq yyi shiru d alama zancen omar na ratsa kwanyar sa. "Can ya nisa yace shikenan na gode da shawarar ka. Omar yyi murmushi yace u r wlcm. "Anan sukaci gaba da hirar su.
****""
Bayan sati biyu, farooq ne ya samu daddy har dakinsa ya sanar masa zancen auren sa, daddy da murna yace wacece? Farooq yace amira 'Yar alhji mukhtar. Daddy yyi murmushi yace good naji dadi sosai, ai namiji idan yyi aure yafi martaba. Farooq dai ya sunkuyar da kansa, mummy dake gefe itama tayi murna tasa albarka. "Daddy yace toh dan uwan naka fah shi be fitar da matar bane? Farooq ya Sosa kai, yace be sanar dani ba daddy, daddy yace turomin shi. Farooq yace toh. "Bayan minti biyar yyi omar a falon daddy, daddy yace kai kuma fa ya mgnr naka auren? Omar ya Sosa kai yace emm daddy har yanxu ban samu wacce ta dace dani ba. "Daddy yace haka kace? Omar ya girgiza kai. Daddy yace ohk zaka iya tafiya. Omar ya tashi cike da farinciki ganin daddy be dau abun da zafi ba. "Bayan fitar sa, daddy ya kalli mummy yace yaronki yana wasa da mgn ta. Mummy itama da damuwa ta kalli daddy dan ta kosa ta fara ganin jikokin ta, tace toh Amman baka CE masa komai ba ya tafi, daddy yace shi yarone? Akanme zanyi ta maimaita mgn? Ga dan uwansa nan ya samawa kansa lpy ai. "Mummy tace yanxu wanne hukunci ka yanke next? Daddy yace akwai mata dayawa d suka nuna suna sonsa acikin su zan sama masa wata saidai yaji anyi masa aure, mummy ta nisa sannan tace Allah ya zabar da abinda yafi alkhairi daddy yace ameen.Nuceey luv😘
YOU ARE READING
OMAR KO FAROOQ?
General FictionOMAR KO FAROOQ? Dukkansu 'yan biyu ne masu matukar Kama daya Wanda ake Kira da identical twins, Kowanne su yanaji da matukar Izza da ji da kai tamkar wasu jinin sarauta, Sun taso ne cikin gata Wanda mafi rayuwar su sunyita ne a kasashen turai Hakan...