007

101 8 2
                                    

*—•@••«•»•@•«•»••@•—*

    *TSAKAR GIDA🏚*

*—•«Start on: 1/1/2021»•—*

*WATTPAD: @Smart_Feenert*
      *_BE-SMART✍🏻_*

*_{🌳EMAIL- smartfeenert@yahoo.com🌳}_*

*—•@••«•»•@•«•»••@•—*

*_🌴BISMILLAHI RAHMANI RAHEEM🌴_*
*—•@••«•»•@•«•»••@•—*

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*—•@••«•»•@•«•»••@•—*

_Joining My Wattpad Link:👇🏻_
       https://my.w.tt/qyn8iY2cHcb

*—•@••«•»•@•«•»••@•—*

006

Numfasawa tayi kafin ta ce da ita "Tabbas haka yake, sai dai kamar yanda na ce maki a d'azu! shine ba komai na sani dangane da tarihin gidan ba, amma sai dai zan gaya maki iya sanina. Wato Alhaji Mudassir Sanusi, shine cikakken sunanshi kuma shine jagoran wannan Family domin dik wata d'aukaka da wannan Family'n ya samu ta sanadiyyarshi ne, Haifaffen garin Kano ne haka Matarshi mai suna Maimunatu, domin auren zumunta ne aka masu, wanda har yanzu suna tare, suna da Yara ukku, Mahir shi ne na farko, wanda ko da muka had'u da su a wannan lokacin bai wuce shekara shida zuwa bakwai ba, sai Khalid wanda shi ke bi mashi sannan Khalil, wanda a halin yanzu wannan labarin da nake baki ya kai tsawon shekara ashirin kenan da had'uwarmu da su, sannan a tare da Alhaji Mudassir akwai k'annensa Maza su ukku wad'an da yake tare da su tun bayan mutuwar iyayensu, suka tare a Abuja a Unguwar Asokoro, dukansu suna tare da matansu da yaransu a gida d'aya tamkar Family dubu, Alhaji Nasiru shi ne wanda ke bi ma Alhaji Mudassir wanda a yanzu yana da Mata d'aya mai suna Ruk'ayya amma Yaran gidan na kiranta da suna Nanni kasancewarta macce ce mai matuk'ar kula da yara sosai a gidan tana da Yara Maza guda
hud'u wanda Abdul-Rahman shine na farko sai Abdul-Rahim wanda ke bima shi, sannan Imran da Irfan su kuma tagwaye ne. sai Alhaji Mas'ud shi ma yana da Mata d'aya Aisha da yara Hud'u, Mukhtar , hi ne na farko sannan Lukhman, wanda shi ne na biyu sai kuma Lamrat wadda ita ce ta ukku sannan autarsu Husna. sai kuma Alhaji Al-k'asim, yanada Mata d'aya mai suna Sumayya tana da yara shidda kuma duka mata, akwai Rufaidat wadda ita ce babba sannan Zubaidat sai Rafi'at, sannan Badi'at, sai Zalihat, da Samirat, dukansu tazarar shekara biyu ce a tsakaninsu!. idan kin shiga gidan dik zaki k'ara fahimta da wasu abubuwa harda ma wad'an da ban sanar da ke su ba, sannan ki bi a hankali domin wannan Family da ki ke gani makirin Family ne sai kin yi taka-tsan-tsan a cikinsu domin kowa idonshi a bude yake, sannan sanannen Family ne da zan iya ce maki duniya ta san da shi har lak'ani ake mashi da STAR GOLD FAMILY, domin sun shahara ta ko wanne b'angaren, wlhy Banafsha idan kika yi sake har suka gano asalin gudurinki a kansu, zasu halakaki ne domin akwai wani b'oyayyen sirri da suke da shi a gidan, wanda ni kaina ban kai ga sanin shi ba, amma dai kiyi a hankali dan Allah.!" Nisawa Banafsha tayi a hankali kafin ta dafa kafad'unta ta ce "Ni k'o nake da masaniyar hakan Momty, domin mu ma an kashe muna iyaye ta siffar da ba zamu tab'a ganosu cikin sauk'i ba, sannan ba su bar wata alamar da zamu iya sanin dililin da ya haddasa yin kisan ba ko kuma mafarin abin, da haka Nake masu Albishir da cewa Mutuwarsu na k'ok'arin tunkaro wajen da suke, dan na rantse da wanda ya busa man numfashi muddin na gano suke da alhakin salwantan da rayuwar iyayenmu Na rantse da Al-samad sai na d'auki fansar abin da aka man muddin ina numfashi fiye da d'aya a duniyar nan.!" Murmushin gefen baki Momty tayi ba tare da Banafsha ta lura da hakan ba, wanda ita kad'ai ta san fassarar yinshi, a ranta take cewa "Banafsha kin mutu murtutus kin koma toka, sai dai na ce Allah ya jik'anki, domin ba wani iblishin da zai iya warware wannan nad'in da aka riga aka nad'eshi tun kan a haifeki duniya, sai ni da na d'aurashi, Uhmm yaro man kaza.!" a fili kuwa cewa take "karki damu, komai ya yi zafi maganinsa Allah, mu dai yi ta addu'a Allah ya bayyana muna gaskiyar wannan al-amarin.!" Haka dai suka k'ark'are firar har lokacin sallar azzahar ya gabato ko waccensu ta tashi ta nufi nata b'angaren.

TSAKAR GIDAWhere stories live. Discover now