*—•@••«•»•@•«•»••@•—*
*TSAKAR GIDA🏚*
*—•«Start on: 1/1/2021»•—*
*WATTPAD: @Smart_Feenert*
*_BE-SMART✍🏻_**_{🌳EMAIL- smartfeenert@yahoo.com🌳}_*
*—•@••«•»•@•«•»••@•—*
*_🌴BISMILLAHI RAHMANI RAHEEM🌴_*
*—•@••«•»•@•«•»••@•—**🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation*—•@••«•»•@•«•»••@•—*
_Joining My Wattpad Link:👇🏻_
https://my.w.tt/qyn8iY2cHcb*—•@••«•»•@•«•»••@•—*
006
"Gold ne, wanda ba a tab'a samun irinshi a Nigeria ba, har ma da wasu k'asashe da Allah ya yi ma ni'amarsu, lokacin da ya gama yi man bayanin komai, dukanmu sai da muka yi sallah raka'a biyu dan godewa ubangiji, haka muka d'auki tsawon satittika da wannan Gold a d'akina ba tare da kowa ya san abinda ake ciki ba domin ba wanda ya san da wannan zancen daga ni sai shi sai Allah, domin bai yadda da na gayawa kowa ba kasancewar kuma duka iyayenmu a wannan lokacin basa raye, ba mu da kowa, shi ya sa muka samu kwarin gwiwar boye sirrinmu a iya mu biyu kad'ai, sai wata rana kwatsam, ya zo man da zancen wani Alhaji Mudassir dake Abuja wanda sana'arshi ce sai da gwala-gwalai, kuma har sun shirya ranar da zaizo ya d'auke gwal d'in domin aje da shi a auna a tabbatar da gwal d'in ne ko ba shi ba ne, haka ko aka yi ranar wata Laraba Alhaji Mudassir da kanshi ya zo da jirgi aka d'auke wannan gwal d'in aka je tare da mai gidana Abuja, sai da suka d'auki wajen kwanaki hud'u a Abuja suka wuce k'asar Dubai da wannan Gold d'in, kasancewar Alhaji Mudassir na hannun daman Shugaban k'asa ne a wannan lokaci shi ya sa basu sha wata wahala wajen fita da shi ba, Wata biyu da suka wuce har na d'ebe zaton dawowarshi nan kusa, sai gashi yazo shi da Alhaji Mudassir suka daukeni muka koma Abuja, a wannan lokacin ban tambayeshi komai game da tafiyarshi ba kasancewar nakudar da ta sakani a gaba, wanda da zuwanmu Abuja aka wuce dani a babban asibiti dake cikin garin Abuja kuma sosai aka bani kulawa har lokacin da Allah ya saukeni lafiya na haifo yarona, Satina d'aya a Asibiti kasancewar na zubar da jini sosai, aka sallameni, bayan na ida mirmijewa na fara meda jikina dan har munyi arba'in amma bai ce da ni ko k'ala ba game da yanda tafiyarshi ta kasance, kuma ni ma ban tambayeshi ba, sai lokacin da na kasa hak'uri domin naga shirun ya yi yawa kuma ni ina son naji yanda abin ya kasance, da dare muna kwance Muhsin ya yi bacci na soma tambayar abin da ya faru, numfasawa ya yi a hankali kafin ya ce da ni, tun farko abinda ya sa bai gayaman ba ya barni ne har na ida samun lafiya tukunna kafin muyi wannan batun, nan dai ya soma koraman baya sannan ya tabbatar man da cewa har yanzu an kasa auna wannan Gold, domin su kansu sun tabbatar mashi da ba zasu iya auna shi ba sai an turashi wata k'asa, amma sun bashi Dala Millions 3 da companys biyu Manya a kasar Dubai na zinare ya rik'e kafin komai ya kammalu, sannan ya shaida man nan da wata biyu masu zuwa zai koma Dubai sannan ba zai dawo ba sai anyi komai an gama tukunna zai dawo, ajiyar zuciya na sauke tare da fatan alkhairi kawai domin ko kad'an haka kawai naji ban gamsu da maganganun da ya gayaman ba, domin na san Alhaji'na sarai mutum ne mai matuk'ar saurin yadda da mutane sannan baya da zargi balantana ya iya hango matsalar dake tattare da kai, bayan wata ukku da sati biyu lokacin muhsin ya d'an fara iya zama kuma mun fara fita ziyara gidan abokananshi, lokacin muna gidan Alhaji Mudassir, a wata ranar juma'at, ranar da ba zan tab'a mantawa da ita a rayuwata ba, ranar da ta zamo ranar tashin hankali a gareni kuma ranar bak'in ciki mai had'e da rud'ani.!" Wata guntuwar kwallace ta sake fad'o mata a fuska ta saka tissue ta goge sannan ta ce "Banafsha! a wannan lokacin ina d'akin Hajiya Maimuna, na gama sallar La'asar kenan, sai ga Alhaji Mudassir ya zo ya d'auki Muhsin ya ce man abokanansu ne suka zo, suna buk'atar ganin yaron, dik da a wannan lokacin ina jin yanayin da nake ciki baya man dad'i tun safiyar ranar wanda hakan ne ya saka muka tsira tafiya gidan Alhaji Mudassir dan yaye damuwa, ashe kana ta ka ne, Allah yana ta shi, domin babbar damuwar da muka fad'a a gidan Alhaji Mudassir ta ninka wanda nake ciki a wannan ranar, bayan Alhaji Mudassir ya zo ya d'auki Muhsin ba a wuce 1hour da tafiyarshi ba, sai kukan fire-service muka ji ta shigo gidan, hankali tashe gabad'ai mutanen gidan suka fito a ciki harda ni ma, ko da muka ida fita waje gaba d'ai, anan mu kaci karo da tashin hankalin dake faruwa, wa'iyazu billahi, d'akin Alhaji-Mudassir ne wanda ke wajen gida wanda yake sauke manyan bak'inshi idan sun zo daga nesa, gaba d'ai ya kama da wuta kurumus kamar wajen da Kantar man Fetur ta fad'i, da k'yar aka samu aka kashe wutar, sai da komai ya fara lafawa hankalina ya fara kawowa ga yarona da Alhaji Mudassir ya d'auka sannan naga Alhaji Mudassir shi kad'ai ba Yarona ba Mijina, agigice na yo wajenshi na rirrik'eshi ina tambayarshi Mijina da kuma Yarona, ganin ya kasa cewa da ni ko k'ala yasa hankalina k'ara tashi, inda matan gidan gabad'ai suka rirrik'eni domin har na fara fita a cikin hayyacina, nan sai ga masu bada agajin gaggawa sun fito daga cikin d'akin d'auke da gawar mijina da kuma ta yarona, Innadillahi wa'inna ilaihim raju'un, tun daga wannan lokacin ban k'ara sanin inda kaina yake ba sai bayan Wata biyu da faruwar abin, na falka na ganni a gadon asibiti, ina son in tuno komai da ya faru da ni har aka kawoni asibiti amma na kasa tunawa, sai bayan kwanaki ukku bayan an sallameni a asibiti, Alhaji Mudassir ya zo shi da Matarsa suka d'aukeni da niyyar su tafi da ni gidansu na ce masu su kaini gidana kawai hankalina zaifi kwantuwa acan, domin a wannan lokacin dik wani abin da ya faru a wannan lokacin yana k'ok'arin dawo mani a kai, haka ko aka yi, bayan sun ajeni gidana, Alhaji Mudassir ya k'ara man da wasu nasihohinshi akai, kamar ina jin abin da yake cewa haka na yi shiru har ya gama suka yi man sallama shi da matarsa suka bar gidan, Bayan wasu 'yan watanni Alhaji Mudassir ya kawo man kud'i da wasu takardu wad'anda ake son saka hannuna na wannan gold d'in, sai dai ya nuna man Mijina ya riga da ya saida wannan gold d'in tun kafin rasuwarshi sannan ya nuna man wad'an nan takardun da kud'ad'en dik suna cikin kadarar da mai-gidana ya bari, ba tare da nace da shi ko k'ala ba na amshi kud'ad'en na aje gefe, takardun kuma na saka hannu na mik'a mashi ya tafi da su, bayan sati biyu ya dawo man da takardun na shaidar dik wata kadara ta Mijina ta dawo hannuna, dik da ina ji a jikina cikin dukiyar da mijina ya bari cikin kashi goma ko rabin kashi guda ba'a bani ba sai dai haka na karb'a na barwa Allah komai domin shi kad'ai ke isar ma bawanshi ga komai, sannan ni dama ba dukiyarce a gabana ba, har i kawo yanzu da nake da company's 8 na Zinare, Hud'u a cikin K'asata biyu kuma a K'asa mai tsarki, wato Saudiya biyu kuma a Dubai, sannan mutanen da ke cin abinci a k'ark'ashina sunfi mutum Dubu d'aya, a haka kuma ba rageni su kayi ba sai dai k'arani, kinji takaitaccen tarihina Banafsha, sai dai akwai abu guda da ban gaya maki shi ba.!" Ajiyar zuciya Banafsha ta sauk'e mai cike da zallar tausayin Hajiya Balkisu, sannan ta ce "Ina ji a jikina kamar na san wannan abin da kika mata baki fad'a man ba!, wato tak'aitaccen tarin Star Gold Family...........!"
FOLLOW ME ON WATTPAD AND VOTE: Smart_Feenert
# Be-smart
Pls share
YOU ARE READING
TSAKAR GIDA
Fantasy"Wallahi summa Tallahi, in dai ni ce sanadiyyar zama ajalinka, Yau-yau d'in nan sai ka mutu!, sai na maka kisa mafi k'ask'anta a cikin kisa-kissai a duniyar nan, zan barka kayi iya abin da za kayi na iya Yau ne domin gobe wada haka kana barzahu kan...