*—•@••«•»•@•«•»••@•—*
*TSAKAR GIDA🏚*
*—•«Start on: 1/1/2021»•—*
*WATTPAD: @Smart_Feenert*
*_BE-SMART✍🏻_**_{🌳EMAIL- smartfeenert@yahoo.com🌳}_*
*—•@••«•»•@•«•»••@•—*
*_🌴BISMILLAHI RAHMANI RAHEEM🌴_*
*—•@••«•»•@•«•»••@•—**🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation*—•@••«•»•@•«•»••@•—*
_Joining My Wattpad Link:👇🏻_
https://my.w.tt/qyn8iY2cHcb*—•@••«•»•@•«•»••@•—*
004
Cike da wani k'ololon bak'in cikin da ya tokare mata mak'ogoro ya sakata bud'e marfin motar da k'arfi ta fita a guje tare da sakin wani wawan kukan da yaci karfinta ta fad'a cikin babban palo a guje ba tare da ta ce ma kowa ko k'ala ba, wanda jin sautin k'arar kukanta ne ya dawo da hankalin wasu daga cikinsu wajenta, sai dai dukansu sunyi mamaki matuka da ganinta domin ba wanda ya san da zuwanta kamar yanda ku ka gani, wanda kai tsaye farin cikin ya koma ciki, kowa da abinda yake tsakawa a ranshi ta dalillin wani sabon halin da suka ga Lamrat na k'ok'arin bijirowa da shi, Wata Mata ce wadda kimanin shekarunta ba zasu haurawa 44 ba sai dai tsabar hutu da kwanciyar hankali da ya zauna a jikinta ba zaka taba gane asalin yawan shekarunta ba, ta tallafo fuskar Mahir dake tsaye a gabanta cikin damuwa ta ce "My son! Dama tare da Lamrat ku ke? amma me ya sa tun farko ba ku sanar da mu zuwanku gaba d'ai ba? Sannan wani abu ya had'aku ne naga ta fito a mota ranta a b'ace? Me ya faru ne haka My son?.!" Kafin ya kai ga bata amsa tuni wata mata wadda ita ma shekarunta ba zasu haurawa 40 ba, sannan tsabar kamarsu da Lamrat kad'ai zaka kallan ka san mahaifiyarta ce, ta ce "Haba Aunty Maimuna! ai kya barshi ya huta ko dan gajiyar da ya kwaso, gashi ko ciki ba ki bari ya ida shiga ba, kin tareshi da tambayoyi masu yawa haka!." Duka cikin kawaici take yin wadan nan maganganun dan kar wani abu marar dad'i ya faru, cikin murmushi irin nasu na manyan mata Aunty Maimuna ta ce "wato idan na fahimceki Aisha, kina son ki kare d'anki ne daga tambayar da nake mashi, bacin ni ga tawa 'Ya can an b'ata mata rai.!" Dukansu dariya suka saka cikin farin ciki, inda Mahaifiyar Lamrat ta sake cewa "ai in dai yawan fushi ne, kowa ya san ba a bar Lamrat a baya ba, kin manta ne Aunty, tun tana k'aramarta haka take? girma ne da ya zo ya saka abin ya lafa kamar da gaske amma gashi kuma yana son dawowa!." Nan dai aka ci gaba da firar cikin nishad'i, kafin dukansu su kama hanyar shiga ciki, inda 'yan aikin gidan suka zo suka kwashe kayansu suka wuce masu da su ciki.
~~~~~
Bangaren Lamrat, tun lokacin da ta shigo cikin wannan babban palo ta kasa gane inda part dinsu yake, wanda hakan ya sakata dube-dube tako ina domin gano abinda take muradi, runtse idanunwanta tayi domin canko wajen sai dai kafin tayi yunk'urin aikata wani abu, sai jin tayi an dank'e mata hannu da k'arfi wanda a zabura ta bud'e idanuwanta domin ganin wanda ya rik'e mata hannun, sai dai ta sake wata nannauyar ajiyar zuciya a lolacin da tayi tozali da wata kyakkyawar yarinya wadda shekarunta ba zasu wuce 6 ba, ta k'ara shigewa jikinta, tana cewa "Oyoyo Aunty Lamrat! shine zaki dawo kuma Mom bata sanar da ni ba?." Mamaki wannan yarinyar ta tsaya yi ganin k'ananan shekarunta bai hana bayyanar wayo k'arara a fuskarta ba, nan dai ta sake sauke wata nannauyar ajiyar zuciya ta ce "Ya sunanki?!" cike da fuskar mamaki da kuma yarinta wannan yarinyar ta saketa tare da cewa "Aunty! Husna ce ni fa!." d'an dafe kanta tayi a hankali ta ce "Srry My Husna! Kaina n........." bata ida zancenta ba, cikin b'acin rai wannan yarinyar ta k'ara cewa "My Husna kuma Aunty! Baby doll fa ki ke ce man!." a hanzarce ta ce "Sorry My Baby doll, kaina ne ke man zafi ba komai nake ganewa ba, ki kaini d'akina kinji.!" Ta k'are maganar tana mai dahe kanta tare da mik'a mata hannunta, ta jata suka haura sama fuskar Husna cike da mamakin canzawar da Auntynta tayi mata, sai dai hakan bai yi wani tasiri a cikin zuciyarta ba dan tuni ta kawar da zancen har suka ida hawa saman upstairs, inda Husna ta bud'e wata k'atuwar k'ofa tuni wani Makeken palo ya bayyana wanda yake tsaf da shi kamar ba a mutuwa domin ba abinda ya rasa komai akwai a ciki, kalar fentin dake d'akin kalar kayan dake d'akin abin dai gwanin birgewa, da wutsiyar Ido Lamrat ke kallon komai dake cikin d'akin a natse har Husna ta ida shiga da ita cikin wani makeken Bedroom wanda shi kad'ai abin kallo ne, juya fuskarta tayi a wani gefe taga wani makeken Elargement a gefen gadonta wanda suka d'auki photon Su shidda a ciki, wata nannauyar aziyar zuciya ta sauke a karo na ba adadi sannan ta samu ta zauna a saman gadon, wanda har ita ma Husna ta d'ale can k'ololuwar gadon tana mata suruttan da ita hankalinta ba ma a wajen yake ba, ta ce "My Baby doll, kije zan huta yanzu zuwa anjima zan fito babban palo muyi fira kinji Babyna.!" Da dariya Husna ta ce "Ok! Aunty! have a great day" ta ce "Thanks my heart beat" a guje Husna ta bar d'akin, inda ita kuma cikin hanzari ta tashi ta saka ma k'ofar key, ta zo gaban wannan enlargement ta tsaya tana mai k'are mai kallo, anan ta fara fahimta da wasu abubuwa dangane da wannan Family domin sai a sannan ta iya gane Matar da take a matsayin Mahaifiyarta da kuma wanda yake a matsayin Mahaifinta sai wani saurayi wanda shekarunsa ba zasu haurawa 25 ba da kuma wani wanda shi ma shekarunsa ba zasu haurawa 23ba sai ita da take da 21da kuma Husna, dukansu cikin shiga iri d'aya inda mahaifinsu da yannenta maza suke sanye da wata tsadaddiyar shadda kalar ruwan kwai, ita kuma da maihaifiyarsu da Husna suna sanye cikin wani tsadadden Lace Brown mai ratsin milk a cikinsa, Murmushin mugunta tayi kafin ta k'arasa gaban madubin dake d'akin, wanda anan ainahin siffarta ta bayyana, sai da ta k'arema ko ina na jikinta kallo, kafin ta ce "Har kullum a haka zaki kasance da siffar da ba taki ba, tabbas ki k'ok'arta ki maida hankalinki wajen fahimtar komai dake wakana a gidan, da kuma lura da shige da ficen kowa da ke wannan gidan, lallai wannan aikinki ne Manafsha...............,"
FOLLOW ME ON WATTPAD AND VOTE: Smart_Feenert
#Be-smart
Pls share
YOU ARE READING
TSAKAR GIDA
Fantasy"Wallahi summa Tallahi, in dai ni ce sanadiyyar zama ajalinka, Yau-yau d'in nan sai ka mutu!, sai na maka kisa mafi k'ask'anta a cikin kisa-kissai a duniyar nan, zan barka kayi iya abin da za kayi na iya Yau ne domin gobe wada haka kana barzahu kan...