005

75 7 2
                                    

*—•@••«•»•@•«•»••@•—*

    *TSAKAR GIDA🏚*

*—•«Start on: 1/1/2021»•—*

*WATTPAD: @Smart_Feenert*
      *_BE-SMART✍🏻_*

*_{🌳EMAIL- smartfeenert@yahoo.com🌳}_*

*—•@••«•»•@•«•»••@•—*

*_🌴BISMILLAHI RAHMANI RAHEEM🌴_*
*—•@••«•»•@•«•»••@•—*

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*—•@••«•»•@•«•»••@•—*

_Joining My Wattpad Link:👇🏻_
       https://my.w.tt/qyn8iY2cHcb

*—•@••«•»•@•«•»••@•—*

005

Ta b'agaren Banafsha kuwa, bayan ta dawo gida a Yau d'in nan kamar yanda suka tsara suka aiwatar, su ma dai kam masu kud'i ne domin kuwa tsarin gidan kad'ai zaka kalla kasan ba k'ananan kud'i suka ginashi ba, Zaune suke a babban Palour wanda aka k'awatashi da kayan alatu kala-kala masu d'aukar hankali, wata farar mata ce fara sol, wadda shekarunta ba zasu wuce 40 ba, Hajiya Balkisu kenan mai gadon zinare, wani kawataccen murmushi ta sauke wanda yake cike da maganganu bila-adadin a cikinshi kafin ta kai ga zama saman nunannin kujerun alfarmar da ke palo'n, ta ce "Gobe zaki shiga cikin wannan Family'n, wato STAR GOLD FAMILY, kiyi kuma rayuwa a cikinsu har na tsawon lokacin da zamu kai ga cin ma burinmu akansu.!" Murmushi shinfid'e a fuskar Banafsha ta ce "In sha Allah Momty, sai dai har yanzu ina ji kamar ban ida fahimtar hanyar da muka dosa a wannan tafiyar ba Momty'na, ina buk'atar k'arin fahimtar zancen, domim har yanzu ban ida sanin taka-manmen asalin labarin gidan ba wanda yake tamkar makami ne a gareni na d'aukar fansa, domin ban san ta inda zan fara wannan yak'in ba dik da, da farko na fara gane hanya amma a yanzu kuma ina ji dik wata idea da gareni tana neman kwacewa a kaina, amma ina saurarenki Momty'na, Mene ne mafita?." Murmushi Momty tayi mai cike da k'ayatarwa kafin ta ce "A dah! aikin bai soma ba tukunna, yanzu ne nake saka ran zaya soma, sannan daman ba zaki tab'a sanin komai ba domin kuwa labarin a rufe yake kamar yanda nake gaya maki, ni ma ba komai na sani ba, amma sai dai na san kad'an daga cikin tarihin gidan tun kan ya narke izuwa dalma wadda idan ta zube k'asa baka isa ka kwasheta da hannu ba!" Banafsha ta ce "Lallai kuwa indai haka ne, ina da tabbacin ko iya abin da kika sani dangane da gidan kad'ai kika sanar da ni, ina da tabbacin zai iya kaini ga rabin hanyar da nake son cinma.!" Furzar da wani zazzafan iska a baki Hajiya Balkisu ta yi kafin ta ce "Tabbas ni na sani cewa Mijina Alhaji Mubarak da kuma D'ana Muhsin, ba mutuwar Allah da Annabi ce suka yi ba, kashesu ne aka yi, kuma a cikin wannan lankwasasshen gidan!." Dummm! gaban Banafsha ya bada ta sanadiyyar jin wannan murd'ad'd'ain al-amari da yake kokarin tab'a mata kwakwalwa domin ta kasa gazgata labarin da Hajiya Balkisu ke kokarin bata, a d'imauce bakinta na rawa ta ce "Momty! ban gane abinda kike kok'arin cewa ba! dama kina nufin kin tab'a aure? a ciki kuma harda k'aruwar D'a Namiji?, to amma idan haka ne, me ya sa ba ki tab'a bamu labarin ba dik tsawon shekarun da muka d'auka a tare Momty?!" Kwalla ne suka fara gangaro mata a fuska kafin ta kai ga amsa mata tambayarta da cewa "Tabbas abinda kika ji na fad'a a yanzu gaskiya ne, haka ma labarin da zan fad'a maki a yanzu ya faru a karan kaina ne da kuma iyalina, dan haka ki kwantar da hankalinki domin na iya samun natsuwar da zan fayyace maki komai akai, na kuma warware maki tufka cikin nad'i ta yanda zaki fi fahimtar yarena!, sannan abinda ya saka ba ku tab'a jin wannan labarin a wajena ba, ba komai ba ne sai dan na kasance ko kad'an bana son tunawa da labarin ne domin yana matuk'ar soye man kitsen dake saman kogon zuciyata, yanzun ma abinda ya saka zan sanar dake shi, sai dan ina saka ran zai k'ara maki azama wajen bibiyar al-amarin gidan, ki iya fahimtar abinda Ni na kasa fahimta.!" Shiru Banafsha tayi na d'an wani lokaci tana sauraren abinda Hajiya Balkisu ke gaya mata, tare da mik'a dukkanin ilahirin hankalinta waje guda don jin yanda abin yake, Murmushin yak'e Hajiya Balkisu tayi cikin ranta tana ayyana abubuwa iri-iri wad'an da ita kad'ai ta san manufarsu, kafin ta soma cewa "Ni 'Yar asalin garin Mai-duguri ce, haka ma mijina wanda muka yi auren soyayya da shi, tun bashi da komai har Allah ya mashi bud'i ya fara samun arzik'in kanshi, kasancewar mijina baiyi zurfi a cikin karatun zamani ba, ya saka ya bud'e shagon kanshi na sana'ar bu-burutu, ma'ana sana'ar saida karafuna da gwan-gwaye, wasa-wasa ya fara samu a wannan sana'ar har Allah ya bud'e mashi k'ofar arziki ya fara lodin kaya daga Mai-duguri zuwa legos, inda shi ma ake yo mashi lodin kayan daga k'auyuka ana kawo mashi yana saya, sai wata rana kwatsam, anyo mashi Lodi daga Zamfara an kawo mashi kaya, bayan an gama saukewa da daddare misalin karfe 10pm ya koma shagonshi domin d'auko wasu kaya da ya manta da su a shagon, bayan ya d'auko kayan ne ya fito har ya kulle shagonshi zai bar wajen kasancewar lokacin Sanyi ne ba kowa ke waje ba, ya hango bas-bas-niyar hasken wani abu dake tashi a cikin k'arafunan da aka kawo mashi a wannan lokacin, cikin k'arfin hali ya sake bud'e shagon nashi ya maida kayan da ya d'auko ya fito yaje wajen wad'annan k'arafunan da 'yar fitilarshi ya yada kayan, ganin hasken wannan abin na son dashashe hasken fitilar ya saka ya kashe fitilar ya saka hannu ya shiga tonon kayan domin ganin abinda ke nan a wajen, wasa-wasa abin ya fara d'aukarshi tsawon lokaci har dare ya fara tsalawa sosai a garin, ni kuma hankalina dik ya tashi musamman idan na duba agogon dake dakin naga lokaci na gudu, gani da tsohon ciki sannan a wannan lokacin ba wayar hannu balantana ka kira ka iya jin halin da mutum yake ciki, kuma mak'ota kowa ya rufe kofarshi baka jin k'arar komai a wannan daren sai na karnuka, a lokacin da na sake duba agogon d'akin naga wajen k'arfe 1:45am cike da tsoron abinda ke shirin faruwa naje na d'auro alwala na fara gabatar da sallolin da ban san adadin yawansu ba, ina sallame raka'a ta k'arshe naji alamun an bud'e gida an shigo kuma an sake kullewa, wanda ta wani bangare hankalina ya tashi, in da ta wani bangaren kuma nake jin sauk'i a raina, sallamarshi da naji ne ta katse ma zuciyata shakkun da take, na ganshi kinkime da wani k'atoton dutse dik ya saka k'yallaye ya nannad'eshi sai dai dik da hakan haske ne zau a jikinshi wanda sai da ya d'an haskake d'akin.!" Nisawa tayi a hankali tare da kiran sunan Banafsha da ta shantake tana saurenta, ta ce "Banafsha! kin san ko menene wannan abin?" cikin k'agowa da son sani ko mene ne wannan abin Banafsha ta ce "A'a sai kin fad'a Momty" murmushin k'arfin hali tayi mai cike da mabanbantan abubuwa, ta ce da ita................
FOLLOW ME ON WATTPAD AND VOTE: Smart_Feenert
# Be-Smart
Pls share

TSAKAR GIDAWhere stories live. Discover now