010

61 7 0
                                    

*—•@••«•»•@•«•»••@•—*

*TSAKAR GIDA!!!🏚*

*—•«Start on: 1/1/2021»•—*

*_FROM D WRITER OF👇🏻_*

*_WAHALA DA GATA seasons 1 & 2._*
*_RUBINA♦️!!!_*
_{Rayuwata su ke son d'auka}._
*_'YAR BALLAJJA'U!._*
*_AND NOW👇🏻_*
*_TSAKAR GIDA!!!._*

*_BEE SMART✍🏻_*

*WATTPAD: @Smart_Feenert*
_Joining My Wattpad Link:👇🏻_
https://my.w.tt/qyn8iY2cHcb

*_{🌳EMAIL- smartfeenert@yahoo.com🌳}_*

*—•@••«•»•@•«•»••@•—*

*_🌴BISMILLAHI RAHMANI RAHEEM🌴_*
*—•@••«•»•@•«•»••@•—*

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*—•@••«•»•@•«•»••@•—*

010

Murmushin Lamrat ta yi cikin ranta ta ke ce wa "Dama na san za'ayi hakan! kin zo gidan nan ne domin ki b'ata shirina.!" ta na maganar ne a cikin ranta dai-dai lokacin da take k'ok'arin zama a saman dinning seat idanuwansu na mak'ale da juna, in da ita kuma Banafsha ke cewa "Babu shakka wannan dik inda ta fito ba mutum ba ce, ita ma Macijiya ce tamkar Ni, domin ina ganin alamun hakan a tattare da ita, wanda ya zama wajibi a gareni, na yi dik yanda zanyi na gano asalin gudurin da ke cikin zuciyarta, idan ya zama dai-dai da nawa sai mu yi tafiyar a tare, idan kuma akasin hakan ne, sai mu d'aura d'amarar yak'i Ni da it.......!" Muryar Umma ce da taji dukansu ta katse masu tunani, inda suka ji Umma na cewa "Lamrat! Banafsha, kun san juna ne?.!" Murmushin da bai kai ciki ba dukansu su kayi cikin hararar junansu, Lamrat ta ce "A'a Umma, kawai ina ji kamar na tab'a ganinta ne, amma ina ga ma ba ita ba ce domin ita wadda nake tunani a America ta ke.!" Murmushin manya Umma ta yi kafin ta ce "Yana yuwa ma ita d'in ce dai ba wata ba, domin wannan ma a can ta fito.!" Nan dai aka shashashe da zancen a dai-dai lokacin da Mahir ke zuwa shi da Mukhtar suna tafe suna zantawa a gefe guda kuma Husna ce tare da su, gaisawa su ka yi da iyayen na su cikin kulawa, kafin ko wannensu ya nemi d'aya daga cikin jerin kujerun dinning table d'in dake wajen ya zaune, wanda ba fara'a ko kad'an a tattare da fuskar Mahir wanda a d'an zaman da na yi a gidan na 'yan awanni na fuskance kowa tsoronshi yake a gidan, idan ka fidda iyayensu domin ya na matuk'ar girmamasu, inda ta b'angare guda kuma, Rufaidat ce da Zubaidat suka tashi suna saving dinmu, inda a gefe guda kuma, na lura da tun lokacin da na iso wannan wajen d'ai daga cikin samarin da ke zaune a wajen ya kafeni da wasu rinannin idanuwanshi na jaraba, Yana jifana da wani mugun kallo irin wanda na tsana a rayuwata, muryar Rufaidat ce da na ji alamun k'asa-k'asa ta na man magana, ya katse man hanzari wajen ci gaba da hanyar tunanin da na lula, inda na ji tana ce man, " Ya dai 'yar shisshigi? kin wani k'ure mazan mutane da ido kamar wadda bata tab'a ganin maza a rayuwarta ba! dan haka, Ina mai gargad'inki da ki iya takonki, domin mu nan gidan ba a mana gwananta, sai ni na taune kwanyar kanki da hak'orana idan ki ka neme shiga gona ta.!" d'ago kaina nayi sama na kalleta dan Ni ban ma ida fahimtar abin da take magana akai ba, a dai-dai lokacin da take k'ok'arin barin wajen, murmushi dukanmu muka sakarwa juna kamar da gaske, na mik'e tsaye tare da ce mata "D'an tsaya.!" cak ta tsaya tana jiran abinda zan ce mata ta k'aryatani a wajen, wanda hankalin wasu da dama a wajen ya dawo ta kanmu, mik'ewa tsaye na yi a hankali na k'arasa wajen da take tsaye, na tsaya dai-dai kunnenta na saka hannayena na kama kunnen a hankali ina yi kamar gyara mata d'an kunnenta ne nake, wanda a bad'ilance kuma magana ce nake soka mata mai mugun zafin gaske, kamar yanda ta man, na ce da ita, "Malama sai famar maganar Maza ki ke a nan wajen, bacin ni banga alamun mazan da ki ke magana a kansu ba a wajen, Ni sai na ga kamar duka mata ne a wajen idan kin cire su Abba Ni banga wasu maza ba bayansu!, shin ko kina man magana ne akan karan kan ki? dan na ga kamar dik a cikinsu kinfi kama da Mazan, sai dai ina mai baki hak'uri da cewa a yi hak'uri a kai kasuwa, wata k'ila a can za a fi amfanin saya, ba dai a wajena ba, sannan karki saka komai a ranki dan Allah, ba wai nak'i tayin da ki ka man ba ne, ke d'in ce ba ki man ba ne, kin gane?" Juyo fuskarta na yi saitin da tawa inai mata murmushin da ya fitar da annurin da ke fuskata k'arara, na ga dik ta wani cika fam kamar ta fashe, na sake sakin wani k'ayataccen murmushina mai mugun cin ran wanda aka yi wa shi, a fakaice na ce da ita "Smile pls!." komawa nayi wajen zamana na rik'a cokali, daga nan na soma zuba ma hanjina bayani, su Umma kuwa sai kallonmu su ke cike da farin ciki domin dik tunaninsu wani abin arziki ne ake tsinanawa Ni da ita, hannun rigarta ta gyara tare da d'aukar flat d'in abincinta, fuuu ta haura sama a zuciye, wanda a tsawace Hajiya Sumayya ta kira sunanta da k'arfi wanda sai da ta kai ga tsayawa da hanzari tare da juyowa fuskarta shane-shane da kwalla, a fad'ace Hajiya Sumayya ke ce mata "Ina kuma zaki ba a gama cin abinci ba?.!" cikin karkarwar murya ta ce "Mummy kaina ne na ji ya na sarawa, ina son naje na sha magani.!" tana gama fad'in hakan ta ida k'arasa hawa upstairs d'in, bakina na tab'e tare da maida harmata wajen ci gaba ba abinda nake. Inda ta ko wanne b'angaren abinci ake ci, ana d'an tab'a fira jifa-jifa, ta wani b'angare kuma shiru ne kake ji musamman ta b'angare Mahir domin shi dai sai zak'a loma yake a hankali yana kurb'ar drinks a gaggauce ya mik'e tsaye tare da d'aukar tissue ya goge bakinshi sannan ya haura sama ba tare da ance mashi dawo ba, wasa-wasa kowa ya fara ajiye cokalinshi aka fara watsewa....
Follow me on wattpad and vote.

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Feb 27, 2022 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

TSAKAR GIDAWhere stories live. Discover now