009

68 4 0
                                    

*—•@••«•»•@•«•»••@•—*

*TSAKAR GIDA!!!🏚*

*—•«Start on: 1/1/2021»•—*

*_FROM D WRITER OF👇🏻_*

*_WAHALA DA GATA seasons 1 & 2._*
*_RUBINA♦️!!!_*
_{Rayuwata su ke son d'auka}._
*_'YAR BALLAJJA'U!._*
*_AND NOW👇🏻_*
*_TSAKAR GIDA!!!._*

*_BEE SMART✍🏻_*

*WATTPAD: @Smart_Feenert*
_Joining My Wattpad Link:👇🏻_
https://my.w.tt/qyn8iY2cHcb

*_{🌳EMAIL- smartfeenert@yahoo.com🌳}_*

*—•@••«•»•@•«•»••@•—*

*_🌴BISMILLAHI RAHMANI RAHEEM🌴_*
*—•@••«•»•@•«•»••@•—*

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*—•@••«•»•@•«•»••@•—*

009

Tuni wannan Zoben ya shanye gaba d'ai jinin da ke cikin wannan kwaryar, Ta koma fari fat kamar ba a tab'a zuba wani abu makamancin jini a cikinta ba.

Hannu ta saka ta d'auki wannan zoben, tana mai k'are mashi kallo kafin ta sake bushewa da wata makirar dariyar wadda lokaci guda ta sake tamke fuska ta ce

"Wannan jinin da kasha, jinin wani musaki ne wanda ya busar da zuciyarshi da baiwar da Allah ya yi mashi, Ya maida zuwa wajena tamkar wajen bauta a gareshi akan wasu 'Yan kud'ad'en da nake bashi, sai dai abin da ya kasa fahimta tun farko shi ne, wannan sadakar da yake zuwa yana amsa a wajena, tamkar rance ce a wajenshi domin gashi lokacin biyan bashin ya yi wanda ba shi da jinkiri ko k'arin lokaci, Hahahaaaa!" Ta sake bushewa da dariya kafin ta k'ara da cewa.

"Kud'i.... kud'ii..... kud'i masu gidan rana wad'an da ke sa a kauce hanya wajen nemansu, Na rantse da tafasasshin ruwan zafi, akan kud'i ba abin da ba zan iya yi ba!, Sai ni MARURO Bokanyar da babu wata bayanta, Bokanyar da ta bada rayuwar D'anta dan cikar burinta, Bokanyar da ta raine mak'iyanta a hannunta, ta tufatar da su da guminta, ta 'yantar da su suka zamo mutane ga kowa.!" sakin zancen tayi a hankali tare da gyara zamanta ta sake cewa.

"Sai dai Ina tausaya maki Manafsha! domin kin riga kin bi hanyar da ba zata iya fitar da ke ba, kin bi hanyar da ki ke tunani ita ce mafita a gareki, amma kiyi dik iya abin da zaki iya sai dai ki sani cewa rayuwarku a tafin hannuna take, domin ban raine ku dan ku d'auki fansar iyayenku ba, na raine ku ne dan cikar burina, tabbas idan kuka cika man burina ni ma nayi maku alk'awarin bayyanar maku da kaina a matsayin wadda ke da hannu dumu-dumu a cikin kisan da aka yi ma iyayenku, kai ba ma su kad'ai ba har ma da wad'an da baku sani ba duka zaku sani a wannan ranar, sai dai albishirin da zan maku a nan shi ne, kuna jin wannan labarin zaku shek'e har lahira domin babu wanda ya tab'a jin wannan labarin ya kwana duniya musamman ga ku mak'iyan gaske!" Dariya ta sake fashewa da ita a dai-dai lokacin da ta ce

"Lallai Banafsha ke abin tausayi ce matuk'a, da har ki kayi kuskuren mik'a dukkanin yardarki ga wadda ta kasance mak'iyiya abin nema a gareki, dik da kasancewata mak'iyiyar gaske a gareki amma dolancinki ya saka kin kasa gane hakan a tattare da ni, sai dai wani abin dariya anan shi ne, Yaron da ki ke son ganin bayanshi shi ma tsohon mak'iyi ne, shi kanshi da ya san asalin ko wane ne shi da tuni Star gold Family ya hargitse domin ba ainahin masu wannan sunan ne a cikinsa ba dukansu Jabu ne ma'ana ba wanda yake da wata kyakkyawar alak'a da su idan na cire Hajiya Maimuna wadda ta kasance 'yar aiki ce a wajensu, hhhhh Marigayiya Banafsha da Marigayiya Manafsha, tun a yanzu zan hak'a maku kushewarku domin ku tamkar gawa ce mai motsi a wajena.!"

TSAKAR GIDAWhere stories live. Discover now