Page 7

127 5 0
                                    

Ba wani abun da zan fada anan illah na cigaba da baku labari
Ayi hakuri dani na dade banyi update ba nagode masu karatu da kuma fans Ina
I love you all
Muke zuwa



Eh yaya na ganshi da manyan kaya ina ganin kamar mutumin kirki ne ba irin su kawu mansur ba". Yaron yace "To amma amana". Na kallesa nace mishi "yaro ka yarda dani bazan cuce ku ba. Saidai ma in taimaka muku".
Kwarai a lokacin da tausayin su a raina.

Yaron ya shiga bani labari kamar haka: Yace mahaifinsa mai kudi ne duk anguwar babu kamarsa a dukiya. Yana da kani daya yaya daya. kawu abba da kuma kawu Mansur kawo abba shine karame wato kanin babanmu saurayi ne kuma shi mutum ne mai tausayi sabanin kawu mansur wato yayan su shida baban mu. Kawu abba yana san mu sosai mun shaku da shi sosai dake a gidan mu yake da zama shima yana da dakinsa daban. Hatta makaranta shi yake kai mu.
Ranar wata alhamishi ce mun dawo daga school muka tarar da abban mu da kuma kawu mansur suna rikici cacar baki abun kamar a buga. bamu san me ya hada su ba, koda ganin mu sai kawu mansur ya nufo hanyar fita wajen har ya kusan zuwa kofa ya juyo yayi bakaken maganganu hade da barazana wa baban mu, sannan ya fice baban mu yaji haushi sosai domin a lokacin daki ya shiga ya rufo. Kawu abba kuwa yaje yana tambayar maman mu ta fada mishi abunda ya faru amma taki gaya sai dai itama zubda hawaye take.

Da da dare.
Har wajen karfe sha daya baban mu baiyi barci ba domin kuwa yasan halin dan uwan nasa zai iya turo mishi barayi su kwashe kudin kamar yanda ya fada. Kudin wasu filayan sa ne guda biyu ya sayar million biyu da rabi shine kawu mansur yazo ya tsare shi wai sai ya bashi million daya yaja jari. Shi kuwa baban mu yace yayi hakuri ba yanzu ba yanzu akwai abunda zaiyi da kudin. Shine abunda ya faru har kawu mansur yaji haushi ya hau fada harda barazana.

Karfe 12:30am da yaji shiru-shiru ya kwanta a tunaninsa dama barazana ce kawai. Bai dade da kwanciya bq yaji hayaniya a kofar gida kuma kamar muryan mai gadi can kuma sai yaji ya kwala wani ihu! Wanda ya shaida mishi ba lafiya ba. Cikin sauri ya dauki jakar kudin ya nufi dakin kawu abba wanda muma a can muke a kwance. Bayan ya tayar da mu ya bawa kawu abba jakar kudin yace mu gudu ta kofar baya ga barayi nan sun zo wai shi zai tsaya in suka zo yace kudin basa a tare da shi.

Kawu abba yayi juyin duniyar nan a kan baban mu ya taso ummanmu mu gudu tare amma yaki. Jin ana bubuga kofar palo ana neman ballata a shigo yasa ya ja hannun kawu abba har bakin kofar baya ya bude muna muka shiga nan fa muka bude yar kofar muka hau gudu. Bamuyi nisa ba mukayi yo wani ihu wanda muka tabbata na baban mu ne. kawu abba ya mika min jakar yace mu shiga wani dan lungun mu buya bari yaje ya gano. Haka kuwa akayi muka shiga wani dan guri mai duhu muka boye shi kuma ya koma, ko da shigarsa palo sai ya tarar an kashe baban mu da maman mu 'yan daban suna ganinshi sukayi chaf da shi suna cewa ga wanda aka bawa ajiyar kudin.

Baban cikin su wani kato ne baki mumuna fuskarsa kadai abar tsoro ce. Shine ya tambayi kawu abba cikin tsawo ya fada mishi ina kudi amma yaki. Nan fa suka hau bugo naushin sa da mangarar sa. Hada masu yankarsa da dai yaga zasu kashe shi sai ya tsaida su yace zai fada. Nan take ya shaida musu kudin na wajen mu kuma ya nuna musu hanyar da muka bi. Koda gama nuna musu sai ogan barayin nan yasa hannu biyu ya murde wa kawu abba kai nan ya fadi matacce, su kuwa suka biyo hanya neman mu.
Tun daga nesa na hange su sun nufo hanyar da torch a hannunsu suna ha haskawa da dai naga in suka iso gare mu ba shakka sai sun gan mu. Nan take na kama hannun kanwata na dauki jakar muka ruga a guje. Har mun danyi nisa tukun suka hango mu. Suka kuwa rufa mana baya, tsabar gudu ban sani ba ta tsakiyar wasu masifafun karnuka na anguwar mu nabi. Ai kuwa suka hayayako har sun nufo mu kuma suka juya sakamkon jin gudun barayin nan. Nan muka barsu suna fama da karnuka inda mu kuma muka tsero fada mar nan yau kwana biyar kenan da faruwar haka in mukaji yunwa sai in dauki kudi in shiga gari in sayo mana abinci.
Wata doguwar ajiyar zuciya nayi da jin labarin yaron nan. Nace "masa yanzu ina kudin?". "Zan dauko maka ne kawai domin na yarda da kai ina ganin tausayi a idan ka kamar bazaka cuce mu ba". A cewar yaron, kallonsa nayi nace "gaskiya ka fada yaro ni ba kamar kawun ku mansur bane ku dauke ni kamar kawun ku abba". Nan take yaron ya tashi yaje ya daga wasu ciyayi ya fido katuwar jakar ya kawo gabana ya ajiye. Kwata-kwata yarinyar bazata haura shekara 8 ba shi kuwa babban namijin zaikai shekara 13 ko sama da haka.

Koda ya kawo jakar gabana ya bude naga makudan kudin dake ciki kudin da ban taba ganin masu yawansu ba a duk tsawan rayuwata. Nan take naji zuciyata ta canza daga tausayi ya zuwa rashinsa zuciyoyi suka fara aikin bani shawar wari wasu na cewa in kashe yaran nan in mallaki kudaden wata zuciyar kuwa na cewa in dauke su in kaisu gidana. Daga karshe dai na aminta da shawara ta farko wato in kashe sun nan kuma na fara tunanin hanyar da zan bi dan kashe su. Sai kuma na tuna a kusa da ruwa fa muke, banyi wata-wata ba nasa kotar gatari na na bigi kan yaron domin nasan shine zaifi bani matsala nan take ya fadi kasa matacce, da ganin haka sai yarinyar ta fara ihu! Ni kuwa ganin zata tona min asiri na shake wuyanta har ta langabe gaba dayansu na kwashe su na zuba a wani ruwa dake wucewa ta tsakiyar fadama. Ruwan yaja su ya tafi da su, ni kuwa na dauko kudin na dawo gida nayi karyar cewa gonar mu na sayar mutane kuwa ciki harda matata da babanta gashi suka aminta sukayi farin ciki. Ba'a dade ba na bude shago na kama sana'a dan gudun kar kudin su kare. Ko da ganin na sama wannan kudi sai na shiga sabuwar rayuwa wato ta rashin mutunci bana ragawa kowa kuma bana san kowa ya raga min watta matata taga canji sosai a tare dani, ko ta bangaren addini na samu tawaya domin ko makaranta daina zuwa nayi wannan shine abunda ya faru inji Muhsin.

"Innalilahi wa'inailaihir raji'un". Wannan kalmar ce take fita a bakin Aisha da kuma mahaifinta. Nan da nan Aisha ta fara kuka tana fadin "Muhsin haka kake dama ashe zaka iya kashe mutum ashe ba iyakar rashin mutun cin kawai kake da shi ba harda rashin imani?". Haka ta jero mishi wadan nan tagwayen tambayoyin wanda shi kanshi baisan wace kalar amsa zai bata ba sai kawai hawaye dake fita a idanunsa da gani kasan yayi nadama.Aisha zata daga baki tayi magana abbanta ya dakatar da ita. Lokacin aljanar tace ina zuwa.

Bat! Ta bace lokaci daya kuma sai gata ta dawo ita da wata yarinya wacce da gani a galabaice take tana cikin kunci da tsabar rayuwa kasan jikinta kadai zasu fada maka hakan. Koda yarinya da aka kawo mai suna maryam taga Muhsin sai ta fashe da kuka ta tashi ta ruga a guje, har ta kusa kai bakin kofa aljanar nan ta mika hannunta wanda a nan take ya kara tsawo ya kamo maryam dake shirin guduwa. Koda ji an sakalota sai ta fara kokarin kwacewa tana fadar "Shine ya kashe yaya sadiq dan allah karku bari ya kashe ni, macuci ne".

Aljanar tace kwantar da hankalinki kawata ba abunda zai miki tsaya baya na. Muhsin yayi matukar girgiza da ganin maryam wanda shi a tunaninsa saida ya kasheta tukun ya Jefata ruwa. "Wannan itace yarinyar da Muhsin ya kashe yayan ta kuma yayi yunkurin kashe ta itama amma Allah baiyi ba. Ta kubuta da rayuwarta daga mutuwa wanda ta fada wata rayuwar kuma wacce gwarama mutuwar da ita. Wannan yarinyar da kake gani fadamar nan ta koma mata gida duk sanyi duk zafi a nan take da safe take shigowa gari ta nemi abincin da zataci da dadare kuma ta koma fadama. Kwana uku baya nazo wucewa na ganta ana mata tamkar yanda kamin wato taje neman taimako ya bata abinda zataci ya kore ta. Ta koma gefe zauna tana kuka saboda tsabar yunwar da take ji dan duk ranar bata sa komai a bakinta ba. Koda naga haka sai na rikida zuwa tsohuwa na kai mata abinci bayan taci ne nake tambayarta ina iyayenta nan ne ta bani labarin duk abunda ya faru. Kaji irin rayuwar da ka jefata kai kuwa ka shiga farinciki.Muhsin hukuncin da na yanke biyu ne ciki ka zabi daya...............................

Ko biyu ni shafi na gaba Muga wane hukunci Alhanar ta yanke mashi......

🥰🥰💋nice taku Yasmeen.

Rayuwar RaihanaWhere stories live. Discover now