Page 8 and 9

126 3 0
                                    

💃🏻 *Kowa ni yake jira to gani na iso, Samari yan mata na nesa ku marmatso. Domin kar ayi babu ku haka sam! Sam! Bani so.  Wannan pagen ku ne karku bari ya wuce wanda aka baya nan bai more kallo ba* 💃🏻😜

😍 wayyo my fans you will kille me with you love. Ina sanku ina alfahari daku  *ANA TARE* supports

         *KARSHEN PAGEN BAYA*
Kaji irin tsadar rayuwar da ka jefata kai kuwa ka shiga farinciki. Muhsin hukuncin da na yanke biyu ne ciki ka zabi daya.»   Muhsin ko dai ka mayarwa da yarinyar nan dokiyar ta ta hanyar bata duk wani abu da ka mallaka ta sanadiyar dukiyar su, ko kuwa ka zame mata ahali kamar yanda ka rabata da yayanta a baya, Dole ka bata kulawa kamar wacce zaka bawa diyarka ko kuma ma tafi haka. Domin da bazarta kake rawa.


Malam ya kalli aljanar yace "lalai wannan hukunci yayi duk mai adalci haka zai yi, saboda haka ni na aminta Muhsin sai ka zaba daya kodai ka tatara duk abunda ka mallaka hatta gidan nan dan da a gidan haya kake ka mayar mata ko kuwa ka rike ta zabi ya rage ga mai shiga rijiya ko ya shiga ta kai ko ya shiga ta kafa. Muhsin yace na aminta da zabi na biyun zan riketa amana isha'allah domin ni yanzu NAYI NADAMA sannan zan ci gaba da rokon Allah ya yafe min laifukan da nayi, Kuma na gode wa wannan aljana da ta tsamo ni daga cikin halaka.
Maryam zo mana daga yau kin zama 'yata".  Ya mika mata hannu da farko taki amincewa saida aljanar tasaka baki tukun.

Aisha farin ciki tuni ya mamaye ta jin ta sama 'ya a bagas! Ta sama mai maye mata gurbin yarta hawwer da ta mutu.  Aljanar ce ta wani tashi saman iska gaba daya iskan wajen ya hau zagaya ta ita kuwa ta fara wata kalar shu'umar dariya marar dadin saurare, Magana ta fara yi muryar na fitowa uku-uku  bazaka iya banbance namiji ne ke maganar ba ko mace ko kuwa yarinya.  "Nice nan aljana SUFURATU marainiyar aljana, Sai na cika burina na ganin ba maraya da zai kasance a cikin kunci. Aikin ma yanzu na fara. Sannan Muhsin ina gargadin ka a kan maryam kuma ka zama mai adalci domin zan dinga bibiyar rayuwar ku".

Sama tayi kamar wacce ake ja tana tafe tana gagaba dariya, su kuwa da gaba daya in aka fitar da malam ba wanda bai tsorata ba, domin Aisha har dan fitsari ne ya fara kubice mata.   Tun suna ganinta har ta bace cikin gajimare. Malam ya kara yiwa Muhsin nasiha sannan ya bashi addu'o'i wanda zai tuba ga Allah ya kara da cewa ya yawaita sadaka, tukun ya musu bankwana ya koma. Su Muhsin sunga abun mamaki yau kam duk cikin su ba wanda tsoro ya sake shi, nan fa aka shiga tarairaya da tattalin maryam  dan gani suke kamar itace ma aljanar.


Acan gidan kamala kuwa da asuba da suka farka sama ko kasa suka nema yarinya suka rasa sun shiga rudu da tashin hankali don har ga Allah yarinyar ta shiga ransu fiye  da zato, a cikin su ba wanda  baiyi mafarkinta ba. Khadija ta zauna tayi zugum ba abunda take sai faman kuka tana tuna yarinyar nan da irin shakuwar da ta shiga tsakanin su tun a jiya.  Yau komi bata iya ci ba har wajen karfe 9:00 ta zauna ne kawai ta zurawa kofa ido a zatanta zataga ta shigo. Kamal da yaga abun yayi yawa yayi lalashin amma kamar kara haukatata ne yake. "Khadija tunda kinki hakura tashi muje nemanta".  Firgigit ta tashi da gudu ta shiga ta dauko hijab. Sun taho sai sauri take tana leke-leke wani wajen ma har gidaje take tatan bayawa. Amma har wajen 11 babu labari. Duk sun gaji sunyi tikilis.  Sufuratu tazo wucewa ta hange su a karkashin wata inuwar mangwaro da sauri ta sauko kasa tazo daidai inda suke, ita har tama manta da su, "Allah sarki da gani nemana kuke na gode da halacin da kuka min bazan taba mantawa da ku ba. Badan aikin dake gaban Sufuratu nada yawa ba da ba makawa DAKE ZAN ZAUNA".duk abunda take fada baji ba suke kuma basa ganinnta.  Kwasar su tayi ciki  abun da baifi seconds 5 ba ta kaisu gida. Mamaki iya mamaki sunyi shi ya akayi hakan ta faru mu da muke tsaye a gindin bishiya kuma gamu a gida. Tambayar dake dauke a bakin ko wannan su kenan.


"Na tafi sai mun sake haduwa" gaba daya sunji an fadi wannan saidai basu san taka mai-mai ta inda muryan ta fito ba. Nan fa suka shiga dube-dube.  Aljana Sufuratu kenan yarinya ce a cikin aljanun ma domin da kadan zata haura shekara 150 musulmar aljanace labarin ta nada dan tsayi da abunda yasa ta fara taimakon marayu. Kasan cewar itama yarinya ce yasa tafi shiga rayuwar yara marayu, dan a ganinta sunfi ban tausayi. Indai taga yarinya cikin wahala saita bibiya rayuwarta ta kuma san labarinta. A yanzu haka ta bar garin abuja ta nufi bauchi.

Inda ta sauka a G.R.A anguwar masu kudi ce, kowa harkar gabansa yake yi tankama-tankaman gidaje ne tsabar rana da akeyi yasa kowa yana cikin gidansa. A farkon anguwar Safuratu tayi gamo da abunda ya bata mamaki wata yar digil gilar yarinya ce karama wace in tayi gudu takai 10 years ko 9 da rabi. Sanye take da kaya atamfa dinkin riga da sket sun mata kyau sosai da gani kasan ba yar talaka bace.  Kanta wani dan bokitin ruwa ne wanda da gani kasan yafi karfinta jan haline kawai yasa take dauke da shi sai jibi take da alamun gajiya a tare da ita daga nesa ta debo shi.  Ba wani abu yabawa Safuratu mamaki ba sai ganin gari da wuta kuma zaiyi wuya a sama gidan da ba tanki a anguwar.  Hakan yasa tace a ranta bari ta bita sai taga wace marar mutun cin uwace wannan, da take neman hallaka diyarta. 

kofar wani gida ta kalla nan take ta saki murmushi, da kyar ta samu ta sauke ruwan ta ruga da gudu kofar gidan nan wata yar baby ce (Diyar roba ta dauka)  nan fa ta sama waje ta zauna ta fara wasa da ita ta bar ruwan da ta dauko din kan titi, dake motoci basa wucewa. "Kutumelesi lalai Raihana yau kuwa zaki daku wato har kin sama damar taba yar babyn nuratu ko".  Kafin ta juyo tuni yarinyar dake maganar ta warce yar babyn hade da kifa mata mari wanda saida ta gigice. Kuka ta farayi Wiiii!-Wiii  ta juye ta kalli wacce ta mare ta din tace "Wllh sai na gayawa mama asiya".  "Jeki ki fada din kiyi sauri kar kuda ya riga ki". Cewar mai marin,

Raihana bata kara cewa komai faman kuka da take ga hawaye ga jibi abun yayi mata biyu. Zuwa tayi taje ta fara kikiniyar dora bokiti a kai,Da kadan ta fadi ita da ruwan badan Safuratu tayi sauri ta tallafa mata ba. Dungwai-Dungwai ta hau titi ta tafi tana kugin kuka. a bakin wani makeken gida ta tsaya tana kwalla kira "Me gadi bude-me gadi".  Aljana safuratu dake binta a baya ta tsaya ta kare wa gidan kallo tas! Taga a duk anguwar gida daya ne za'ace sunzo daya da wannan gidan ta girman shi da kyawan shi, da gani kasan an kashe nera, "To ke kuwa me zakiyi a nan gidan ko wata sabuwar tsokanar ce domin bana tunanin yar nan gidan ce ke".  Safuratu ke magana ita kadai.  Mai gadi ne ya taso da sauri yana masifa "Ke ki tsaya inzo in bude mana kin ishi mutane da kira". Bayan ya bude ya gallah mata harara wa kuma ya tabaki kika zo kina bude mana baki?".  "Zulaihat ce ta mare ni". Ta fada lokacin da ta wuce ciki, "Dan an dan mare ki shine zaki ishe mu da kuka kuma, yarinyar nan dai anyi ja'ira".

Tun a kofar falo ta fara kira "Aunty ameera-aunty ameera". Da sauri ta fito tana mata masifa to jarababa kin dawo wato har kinzo kin fara takurawa mutane".  Ameerar ke fada haka lokacin da ta sauke mata ruwan tana juyewa. Hanyar daki ta nufa da sauri ta kamota, ubanki nace Raihana dan iskanci ina zaki?. Ko kina nufin wannan ruwan ne zai ishe ni wanki?".  "Aunty zuwa zanyi in gayawa mama asiya Zulaihat ta mare ni".  Ta fada tana shashekar kuka "Muna fuka ai ba'a banxa zata mare ki ba da abunda kika mata, oya ni wuce ki karo min ruwa wllh sai kinyi sawo uku nan gaba". Rushewa tayi da kuka "wllh ni dai na gaji wajen yayi nisa aunty ki tausaya min ki deba a can". Wani tankin ruwa ne ta nuna da yatsarta ya cika sai zuba yake ma. A lokacin Safuratu ta gane cewa ba rashin ruwa yasa aka tura Raihana ba mugunta ne kawai.


"Kan uba! Iyee Raihana ni zaki dinga fadawa kin gaji in aike ki kice kin gaji?".  Kwashe ta da mari tayi dan karfin marin  har saida ta kusan faduwa.  Wani sabon kukan ta dora dashi mai karfi. Da gudu naga wata budurwar ta fito daga falo tazo ta kama Raihana tana kalan waccan, "Haba ameera wai miyasa ke muguwa ce bakya jin tausayin yarinyar nan ko kadan shin so kike ki kashe ta ne?. Kin turata debo ruwa dan iyayi bayan ga ruwa nan yanzu kuma kina dakar ta gaskiya karki kara dukanta".

"An daka din kiyi abunda zaki yi bari ma ki gani inci ubanta a gaban ki inga ubanda ya isa ya hanani".Raihana ta nufa ta daga hannu zata kara marinta da sauri Wacce ake kira Iddau charaf! ta rike hannun, "Ameera wllh bazaki dake ta ba a kan me wato ita batada gata ko?". Ameera tace, "Sake min hannu, sakar min hannu".  "Anki a saki ki kwace in kina da karfi".  Haba wa ai kafi ta rufe baki tuni Ameera tayi kukan kura ta chakume ta, nan fa suka hau kunce harda naushe-naushe. Safuratu na tsaye tana kallan ikon Allah abun ya fara rikitata.

Wasu yan mata ne a daki su biyu kusan kansu daya da kadan dayar ta dara daya Zan iya cewa daya shekarar ta 12 dayar kuma 14. Daga ganin su kaga mararsa jin magana ta kwaliyar da sukayi ma kadai ta isa ta sheda maka hakan ba kauya wa day ba wannan kwaliyar taci uwar ta kauyawa day a hauka. Kamar ance wa mai suna Asma'u ta kallo waje ta window.  Wani dan kara tayi na jin dadi nan da nan ta mike.Yawa bigi ciki aunty ameera, karki bari ta kada ki aunty iddau". (fiddausi suke kira da iddau) koda jin haka naga dayar ta bar abunda take da gudu tazo ta haye kan gadon itama ta fara leke. Tsalle tsalle suke suna dunkule hannu suna fadin bamu rabawa saidai mu kara zugawa bigi cikin dan bari bakin. Maganar da suke tana kaiwa har kunnuwan masu fadan amma basu bari ba sai ma kowacce ta kara dadagewa. Su kuwa su Asma'u komawa sukayi Kamar dai supports a filin Wrestling ko wacce ta zaba wacce take so............

Rayuwar RaihanaWhere stories live. Discover now