page 5

842 36 8
                                    

Bismillahir Rahmanir Rahim

Toh masu karatu yau zan cigaba da rubuta maku abunda zai faru da Muhsin

Dan Allah a yafe ni Dan banyi updating da wuri ba

Aisha gaba daya da firgice dan itama abun ya bata tsoro aiko a guje ta kwasa waje tana zubar hawaye da Sauri ta bude randar ta na kasa Wanda ke da ruwa ciki yayi sanyi sosai ta debo ta koma Inda mijin ta yake ta kwarara mai ruwan nan aiko nan take ya mike tsaye yana zare idanuwa yana waige waige kamar wanda ke neman wani abu dayan hannun sa kuma yasa yana goge fuskar sa da shi domin ruwan da Aisha ta kwarara mai

Ganin abunda yake nema bai ganshi ba yayi saurin mikewa zuwa kofar daki a guje ya rufe ta yasa mukulli da sakata ya rufe dakin gam yana fadin Aisha wallahi kashe ni zatayi dan Allah ki taimaka man mu kara jawo drawer Innan mu kara rufe dakin ita ko Aisha tsaye tayi tana kallon shi yadda duk yabi ya wani rikice yana abu kamar wani mahaukaci tana cewa Wai lafiyan Ka lau kuwa, Ya kake ta wasu irin Abubuwa wanda ban taba gani ba.

Tsawa ya daka mata kamar yanda Ya saba, zabur ta mike saboda tsawar da Ya sake daka mata,  nace kizo ki Kama wannan drawer mu kai mu rufe dakin nan,  Aljana ce wallahi in ta sake shigowa kashe ni Zata Yi,  Aisha Sai yanzu ta gane mijin nata gamo yayi,  maigida wace aljana Kuma, oh my God Ya fada, tinda baza ki Kama ba,  baza ki taimaki mijin ki ba so kike a hallaka ni toh bari inkai ni inje inyi da kai na, kikir-kikir Kake ji Yana Jan drawer har wajen kofar dakin ya danne kofar amman dannewar ke da wuya yaji an fara girgiza kofar dakin aikuwa da gudu ya haye kan gado ya lullube kansa da bargo sai kyarma yake tayi kamar wani mai jin sanyi , Aisha tazo kanshi ta fara tofa mashi addu'a har Allah Ya taimake shi bacci yayi gaba dashi, tinda da asuba ya tashi yaci gaba da zabure zaburen sa Aisha na tofa masa addu'a amman Aisha taga abun yafi qarfin ta, hakan yasa ta dauki waya ta kira baban ta,  tana kuka ta gaya mashi duk abunda ya faru yace gashi nan Zuwa.

Muhsin ba abunda yake sai surutai duk bayan mintuna Kuma Sai ya dinga tsorata yana boye wa bayan gado yana fadin ga tanan ga tanan, Aisha ita Kanta ta shiga Rudu, ba'afi mintuna ashirin ba malam hamza ya karaso gidan su Muhsin, yana Zuwa da sallamar sa da gudu Muhsin ya makalkale Malam hamza yana surutai.  Sai da malam hamza yayi dagaske tukunnan ya raba kansa da Muhsin Lokacin daya fara tofa masa addu'a tukunnan ya dan Samu hakan ya dan rage ya lafa, malam Ya zaunar dashi a kan tabarmar da Aisha ta shinfida masu,  bayan sun zauna ne malam ya karanto ayatul kursiyyu tareda sauran ayoyi masu largo,  ba'a Dade a karatun ba Sai ganin wannan yarinyar sukayi Cikin Kayan da khadija ta sa mata a gaban malam zaune tareda masu sallama.

Muhsin har zai ruga malam ya ruko shi ya zaunar dashi harta Aisha ta tsorata Dan ganin abun tayi kamar a mafarki Yau ga aljana ta bayyana a gaban ta.  Malam Ya kalleta yace baiwar Allah mi wannan mutumin ya maki yana mai nuna Muhsin, an bani labarin irin azabtarwar da kika mai jiya da daddare, muryar ta Marar dadin ji tace Ka tambaye shi malam ai shi Yasan abunda yayi,  malam baiyi gardama ba Ya juya Ya tambayi Muhsin mi yayi mata, a tsorace ya bayyano duk abunda ya faru tsakanin su... Karya Kake munafuki azzalumi macuci, Ko daya ni ba Dan wannan Na shiga rayuwar Ka ba wannan ma nayi ne Dan in tabbatar da rishin mutuncin Ka da mutane ke fada Sai gashi naji da bakin Ka kake fadan kai Marar mutunci ne.

Malam Muhsin shin Ka manta abunda Kayi ne shekara daya da rabi da suka wuce?  Yarinyar ce take fadan hakan Cikin tsiwa tana hararar Muhsin din....

Toh masu karatu a nan Zan Dakata Sai ku biyo ni a babi Na gaba muji shin mi Muhsin ya aikata shekara daya da rabi da suka wuce.

Ku gafarce ni nasan na dade ban yi updating ba.  Makaranta ne Ya Hanani.

I love you my fans.  Please continue voting and also wait for more of my pages thank u all😍😍😍😍

Rayuwar RaihanaWhere stories live. Discover now