Page 12&13

169 5 1
                                    

KARSHEN PAGEN BAYA*

kafin kace me tuni sun ruga upstairs tana biye da su koda tahau matakala na daya biyu sai sulbi ya kwashe ta ji kake tum ta fado kasa kamar an yarda buhun masara. Kanta ne ya bugu da kasa. Su asmart da suka juyo sukaga abunda ya faru sai suka dora da wata sabuwar dariyar.

»» gidan ALHAJI SALIM S.O kenan babban gida ne dake cike da iyalai. alhaji salim mata hudu gare shi saidai daya ta mutu yanzu uku ke a raye. Asiya uwar gida yaranta biyar biyu mata sune AMEERA DA ASAMA'U. Maza uku SAFIYANU babban danta sai mai bi mashi YUSIF. Da kuma yayan ameeera ABBA.

Mai biwa asiya ZUWAIRA 'Ya'yanta hudu FIDDAUSI. NASIMA. ABDUL Sai ALIYU. A yanzu HAUWA'U Ce amarya yaranta biyu kadai kanana ILIYASU ABUBAKAR.

Shekarar hindatu (Mamar Raihanna) uku a gidan ta rasu sai dai ta mutu ta bar raihanna  tana yar shekara biyu. Yarinyar fara kyakyawa a duk gidan tafi kowa kyau domin ita ta dara mahaifiyarta ma kyau. Alhj salim kuwa ya dauki duk san duniyar nan ya dora a kan Raihanna domin yana jin tausayinta sosai kasan cewarta karama kuma marainiya hakan yasa ya dauki amanarta yabawa asiya.

Irin san da yake nuna mata shi ya jawo mata ta zama kamar jaba a gidan in aka cire Fiddausi, maza da mata yara da manya baki daya ba mai ragawa Rihanna a gidan bata samun sauki da farin ciki sai abbanta na gida.

Hakan yasa ma in baya nan sai ta shiga daki abunta wani lokacin tata barci wani tym din kuma tata kuka abunta. idan ta tuno mahaifiyarta. A labarin da nake baku yanzu Raihanna takai shekara 9 da rabi a duniya ta iya yiwa kanta komai. Dan ko da tana karama bayi mata ake ba, Asiya da dauda take barinta. Rihanna na shan wuya sosai Domin har ta saba da wahalar da yan uwan nata suke bata bama kamar Asmart, da Nasmat. Wadan nan biyu ba irin wuyar da basa bawa Rihanna.

*Cigaban labarin*
Washe gari Rihanna ce ta tashi daga barci ta kalli dan agogon dake ajiye a kan mirror dakin nasu firgigit ta zabura ganin karfe 6:10 bata yi sallah ba. Sauran yan uwan nata mata da suke tare a dakin ta kalla. Sai bacci suke abunsu. Fiddausi kawai ta tayar domin ita tace ta dinga tadata. Rihanna sauran ta kalla ita ba abun ta tashe su ba tasha fada in bataci sa'a bama har duka. Tashi tayi ta nufi ban daki a guje. Tayi alwala ta dawo ta tayar da sallah. Naji muku haushi sosai da baku ji karatun yarinyar nan ba.

A hankali bayan tayi fatiha take jan suratul الغا شية ghaashiya. Muryarta na fitowa a hankali. Kamar kar karatun ya kare. Tayi zaman tahiya kafin ta karasa ta sallame. Tun kafin matar ta karaso take kwalla uban kira. "Rihan ! Rihanna!" Da karfi. Rihanna najin haka ta kama sauri Allah-Allah take ta idar da sallah kafin matar ta shigo.


domin tasan halin mama asiya kwarai bata bata dadi kuma tafi kowa musguna mata a gidan. Asiya dingishi take sakamakon double faduwa da tayi jiya. Banko dakin tayi.

Kamar wacce zata karya shi. Ta tsaya a gurin ta kama baki. "Iyye! Gaga 'yar banza wato sai yanzu ma kike sallah baki tashi da asuba kinyi ba ko?. inji mama asiya. A zuciya kuwa tace "yarinya kina kokari domin kuwa ni banma yi ba tukun". Daidai lokacin Rihanna  ta idar da sallah ta juyo ta dan risina tace, "mama asiya ina kwana". Da ban kwana ba zaki ganni ne dan ubanki?. Sunkuyar da kai kawai rihanna tayi. "Munafuka Kaganta kamar wata salaha. To da ban kwana ba zaki ganni ne?, Tambayarki nake, Maza-maza ki iske ni a kitchen.
Yau dake zamu hada kayan kari. Saura kuma ki ki zuwa da wuri ta kama kunnan rihanna  ta murda. "Kinga kunnan nan to sai na cira shi. Ko in ba-ba-laki in yaso in bada kudin dori".

Rihanna sai da tayi dan kara domin zafin da taji na murda kunnan gashi har yanzu taki sakinta. Asiya tace. "Bazaki bar yiwa mutane ihu ba sai kin tada mana yara. Maza ki iske ni a kitchen kinji ko?". Gyda kai rihanna tayi tace "naji gani nan zuwa mama". Mari ta wanka mata. "Wacece mamarki din?, Allah ya suttura in haifi yarinya kamarki". Ta nuna wasu yan mata dake gefe a gado suna ta sharar barci tace "kinga yarana can ba kamarki ba". Mtseww Ta ja tsaki ta fice.


Nan ta bar rihanna tana kuka. Ta zubda hawaye sosai tukun ta tashi taje da sauri ta shiga bedroom tayi brush tukun ta canza kaya ta fito. Dugi-dugi ta nufi kitchen. Rihanna  tasha wuya sosai a kitchen din dake gaba daya ake haduwa ayi girki a gidan. ba mai tausaya mata a cikin matan baban nata duk su ukun miko wancan kulkula wannan wanke can gyara can. Ba mai tausaya mata ko ganin kankantarta a cikin matan. Bayan an kamala ita suka dinga dorawa kulolin abincin tana kaiwa dinning. Saida aka kamala komai tukun suka korata daki kuma suka ce in ta shiga ta kwanta kmr mai barci kar ta yarda alhj ya gane cewa ta tashi balle ma ya gano tayi aiki. Haka ta tafi tayi yanda sukace ta hau gadanta tayi shiru. Tana ajiyar zuciya. Su kuwa kowacce. Sai ta shigo dakin ta tada ya-nata-ya-nata duk suka yi wanka sukayi brush tukun aka nufi dinning. A nan kwance suka bar Rihanna. Tana jinsu duk abunda suke.
...................................................

Rayuwar RaihanaWhere stories live. Discover now