page 2

1.1K 39 1
                                    

Bismillahir Rahmanir Rahim...

Kamala jin saboda abinci ne ya dake ta dan takaici bai ko sake mai wata magana ba ya kama hannun yarinyar ya nufa gidan shi da ita dake ba nisa daga nan. Yana rike da hannun ta tana bin shi a baya har suka isa gidan matar sa Khadijah tana sharar tsakar gida. Tana jin sallamar shi ta mike tana kallon sa tana kuma kallon yarinyar. Baby sannu da zuwa, wannan kuma yarinyar daga Ina take fada lokacin da take kokarin Kama hannun yarinyar.

Rai a bace ya kwashe duk abunda ya faru tsakanin shi da Muhsin ya gaya mata. Khadija na da mutunci sosai nan take taji tausayin yarinyar da kuma sonta a cikin ranta. Ta jawo yarinyar kusa da ita tana goge mata hawaye hade da cewa haba mana dena kuka kinji er diya ta. Ya sunan ki daga Ina kike. Wannan tagwayen tambayoyin ta jera mata amman shuru yarinya taki magana sai ido da take binsu dashi daya bayan daya tana kallon su.

Kamal ya maimai ta tambayar da matar shi ta mata Amman shuru kake ji. Sun maimai ta maganar ta Kai sau biyar amman taki magana ko uhum baka ji. Kamal ya kalli matar shi sai tace baby Ina tunanin wannan yarinyar kurma ce shiyasa ko Muhsin bata ma magana ba, Kamal ya ce kwarai nima nayi tunanin haka.

Yanzu abunda nake so da ke shi ne kije kiyi mata wanka ki canza mata kaya ki wanke mata gashi sai kuma ki bata abinci taci. Ni bari in je in siyo mata takalmi ji kafar ta ko takalmi bata da shi domin yasan matar sa ba me bijirewa umurnin sa bace. Komi yace ta mashi inde ba a bun sabawa ma Allah bane tana iya kokarin ta taga ta faran ta mashi. Toh baby a dawo lafiya ta fada lokacin da ta ga ya mike zai fita. Kan wani lokaci tini Khadija tayi mata wanka da wanke mata kai saboda tsabar dauda sai da tayi amfani da bokiti ukku. Da ace mai kyama ce Khadija baza ta iya ba dan tana yi tana dode hancin ta saboda tsabar wari.

Bayan ta gama Mata wankan bata maida mata rigar ta ba sai dai ta dakko wani rigar tasa mata shi ta shigar da ita taki ta zuba mata abinci ita kuma kamar wanda ya shekara dubu bai ci abinci ba haka ta fara cin abincin ta tsoma duka hannuwan ta biyu duka dama da haggu tana ci dasu. Tana gama cin abincin ne sai ga Kamal ya shigo da wasu sababbin takalma ya mika ma Khadija su yace gasu ki sa mata ni zan koma shago. Toh Khadija ta amsa masa. Kamal kafin ya fita ya juya ya kalli yarinyar ya ga wani irin kyau data kara gata tayi haske Masha Allahu ashe datti ne daman ya maida ta mummuna bai Kara cewa komai ba ya juya ya tafi. Koda tafiyan shi Khadija ta juya tasa mata takalman ta tattara mata gashin ta dauko ribbon inta da take dashi ta daure mata gashi da shi.

Tana gama shirya ta ta mikar da ita tsaye ta kalle ta daga sama har kasa tace wow Masha Allahu yarinya mai kyau. Khadija tace Allah Mai iko ga yarinya mai kyau kamar aljana. Bari in dauko jambaki da powder in sa maki kina so? Khadija ta tambaye ta Dan lokacin har ta manta da yarinyar bata magana a bun mamaki kuma sai taga yarinyar na daga kai sama da kasa alamun eh sai Khadija ta dan yi murmushi hade da cewa daman kina jin magana ashe magana ce kawai bakya yi nan ma ta kara girgiza kanta nan ta ke murna da farin ciki ya kama Khadija ta kuwa fara jera mata tambayoyi acikin tambayoyin nan kuwa ta tambaye ta Ina ne gidan su yarinyar ta nuna mata bata sani ba ta kuma Kara tambayar ta Ina iyayen ta suke nan ma ta sake nuna mata cewar bata sani ba har hawaye ya fara zubo mata a fuska.

Khadija ta shiga lallashin ta tana cewa daga yau na zama mamar ki kin yadda yarinyar ta girgiza mata kai alamun eh aikuwa nan take Khadija ta janyo ta ta rungume ta kakam kamar wadda aka ce za'a raba uwa da diyar ta haka ta rungume ta cikin farin ciki domin kuwa Allah ya mata son yara kuma har yau Allah bai bata ba dan so biyu tana samun ciki yana barewa. A ranar kau Khadija wuni tayi tana cikin farin ciki Dan kuwa duk inda tayi yarinyar na biye da ita danko tini sunyi wata shakuwa mai tsanani a tsakanin su har wasanni suke yi.

Da magriba haka Kamal ya dawo ya iske su Khadija suna ta wasa. Khadija na ganin shi ta rungume shi ta gaishe shi sannan ta dinga bashi labarin abunda ya faru tace ashe magana ne bata yi amman tana jin magana nan Kamal ya mata magana nan ma ta girgiza kai sai yace toh yanzu tinda bata magana ya za'ayi musan sunan ta Khadija tace kaji wata matsalar Kuma ni nama manta in tambaye ta tin dazu saboda tsananin murna ta juya wajen yarinyar ta tambaye ta tace kin iya rubutu yarinyar ta girgiza Kai alamun a'a Kamal yace toh mu saka Mata suna Walida mana tinda daman can muna son sunan. Khadija ta juya ta kalle ta tace kin yadda mu sa maki suna Walida yarinyar ta girgiza Kai alamun eh.........

Ku biyo ni page na gaba muji mi zai faru bayan sun rada Mata suna Walida.......
😍😘😘😘😍😍😍

Ina son ku Allah ya saka da alkhairi...

Please kindly vote and follow me thank u😍😍😘😘😘😘😘😍😍😘😘😘😍😍😘😘😘😘😘😍😍😘😘😘😘😍😍😘😘😍😍😍😘😘😍😍😘😘😘😘😍😍😘😘😘😍😍😘😘🤗

Rayuwar RaihanaWhere stories live. Discover now