page 6

472 26 2
                                    

Assalamu alaikum. 

Toh masu karatu mun tsaya a inda aljanar take tamabayar Muhsin shin ko ya manta abunda yayi shekara daya da rabi da suka wuce

Nan fa kwalwar Muhsin ta shiga juya Mai yana kokarin tuno wani Abu, ganin ya shiga cikin wani dogon tunani ta sake daka mashi wani Tsawa wadda ita kanta Aisha Sai da ta firgita sosai kamar ta gudu Sai taji ance" kai azzalumi Muhsin, wato Ka manta yaron da ka kashe Ka raba sa da dukiyar sa, Ka raba yaya da kanwa koh?  yarinyar ce ta fada hakan, dum  gaban shi ya fadi jin ta dauko zancen da a tunanin sa ba wanda ya sani daga shi Sai Allah sai Kuma wannan yarinyar. What???  Yaron da Ya kashe?  Aisha da malam ne suke fadan haka a tare, bugun kirjin sa ne Ya tsananta, nan take jikin sa Ya fara Bari,  matsowa Ya fara Yi gaban yarinyar yana fadan Ashe Daman ke aljana ce ban Sani ba, Dan Allah ki rufa man asiri karki tona wannan sirrin, duk abunda kike so Zan maki amman ki taimake ni karki tona wannan asirin ai tun kafin ya dasa aya a maganar sa ta daka mai wata rikitacciyar tsawar da Ya tsayar dashi.

Nan take ta bata rai fuskar ta ba walwala tace ai bani bace wannan yarinyar daka kashe wa yaya ba Dan da nice wallahi bazaka Kara kwana ba a ranar. Ka basu labarin abunda ka aikatawa wannan yarinyar inkuwa ba haka ba yanzu kuwa ka gaya wa en garin ku. Karashe maganar tayi cikin daga murya nan kuwa take tsoro ya kara kama Muhsin. Muhsin yace toh toh bari in fada karki man komai Dan Allah , malam da diyar sa ba abunda suke yi idan ba kallan ikon Allah ba, Aisha tunani take shin wannan wane irin boyayyen al'amari ne da bata sani ba game da mijin nata, ita dai tasan mugun halinsa wanda yake a bayyane kowa yasan dashi amman kuma bata san wane Abu bane wannan. Muhsin ganin kowa yayi shuru shi ake saurare kuma aljanar sai wullo mashi wani irin mugun kallo take mai tsoratarwa hakan tasa ya shiga bada labari duk ilahirin jikin sa yana rawa, sai ya fara da cewa kimanin shekara daya da rabi da suka gabata duka ba'afi wata ukku dayin aure na da aisha ba, lokacin ne na shiga wani mawuyacin hali, talauci ya kamani, talauci har ya Kai da ko bredi ban iya saya mana wanda zamu ci ni da Aisha. Bakomai bane ya kara talaucina ba sai matsalar da muka samu da ogana na gareji har ya sa na bar aikin. Nayi buge buge na, na shiga nan na fita nan domin samun aiki amman banyi nasara ba. Ranar wata alhamis Dana ga abincin sakawa a bakin mu ya gagaremu yasa na shirya na dauki gatari na nufi jeji domin na saro itace nazo cikin gari na sayar wa mutane dan mu samu na ci, Hanya nabi Ina tafiya Ina tunanin yadda rayuwa ta juya man baya sai kace wanda aka tsinana mawa, nikam bansan yadda zanyi da rayuwar nan ba domin ko sarar itacen Ma ban iya ba, Ina ta tafiya Ina ta tafiya har nakai wani wajen da nake son in ratsa in cigaba da tafiya sai na juyo magangan wasu mutane, Ina lekawa sai naga wasu yara guda biyu, na Dan tsorata da ganin su, kamar yadda suma suka ji tsoro da suka ganin. Yarinyar ta kankame na mijin wanda ya kasance daga gani yayanta ne. Bayan en tambayoyi dana masu suka bani amsa nan da nan na saki jiki dasu nace su fito, suna fito wa muka samu waje muka zauna, na tambaye su mi suke yi cikin dajin nan, na mijin ya kalli kanwar sa yake cewa Iman in fada mashi? Maganar da yarinyar tayi ya tabbatar min da cewa mai Wayyo ce.

Ku biyo ni shafi na gaba muji shi ya labarin zai kasance kuma mi muhsin ya ji da har yasa ya kashe mata Dan uwa.....

☺️☺️☺️kuyi hakuri na dade ban yi update ba nagode 🥰🥰😍😍🥰

Kindly vote and follow me please🥰🥰🥰 thank you.

Rayuwar RaihanaWhere stories live. Discover now