page 1

2.3K 87 1
                                    

Bismillahir Rahma nir Rahim. Da sunan Allah Zan Fara rubuta wannan littafi da kuma taima kon shi Zan ida.

Allah ya bani ikon Rubuta maku abunda zai amfanar daku DA kuma Alumma gaba Ki dayan ta.

😍😍😘😘😘😘😍😘😘😘😍😍😘😘😍😍

Acikin kauyen sauka dake garin Abuja. Unguwar dake da taron mutane kuma garin duhu ne Dan daga lokacin da karfe shidda tayi sai an haska da fitila.

Wata yarinya ce sanye da doguwar riga fara amman har tayi baki saboda tsabar dauda. Yarinyar fara ce doguwa gata da dogon gashi amman duk yayi dauda saboda rashin gyara.

Yarinyar ta isa bakin wani shago ta mai tsaye tana kallon shi. Mai shagon yana dagowa ya ganta tana kallon shi sai gaban shi ya fadi nan take yanayin shi ya can za. Kallo daya zaka mashi ka gane ya fusata.

Mai shagon yace ke uban miye Zan maki haka jiya Kika zo Kika Mani tsaye bakin shago kina wani nuna Mani baki da ciki. Haka yau ma ta sake daga hannuwanta sama ta sake gwada mai baki da ciki alamun yunwa dan duk wanda ya gani yasan abunda take nufi kenan. Shi kan shi ya gane abunda take nufi amman ya gwada kaman bai gane ba sai cewa yayi ni ubanki ne daxaki wani zo kice in baki abinci.

Nan take yace in baki wuce kin bani waje ba sai na zazzane ki baki San daman na Dade banyi zalinci ba dan ni da zalunci kamar riga muke Dan in banyi ba ji nake kamar zindir nake ba kaya a jiki na.

Aiko nan ya fiddo wata tsaleliyar bulala mai Kai biyu wadda tasha mai daman kuma ya siyo ta ne dan yara.
yana nan yana ta surutan shi yayi tunanin juya wan daya yi ya dauka bulala zata ruga kaman yadda sauran yaran keyi idan sun ganshi da ita amman Kuma yana juya wa sai yaga akasin haka. Juya wa yayi ya ganta tsaye tana kallon sai kuma ta Kara gwada mai alamun tana jin yunwa aiko a bun ya Kara fusata shi. Ya dauki bulalar nan yana ta bugun ta da ita tin tana yi tana kuka a hankali har ta Kai da ta fara kuka DA karfi

Mutane na jin kukan ta aiko suka yo chaaa suka kwace ta daga gareshi shi kuwa sai masifa yake yana cewa gobe ma ta kara dawowa. Wani saurayi ne nagani daga can gefe yana lallashin ta ko kyamar ta bayaji kamar yadda sauran mutanen ke kyamar ta. Cewa yake yi shiru kinji dena kuka kinji sai ya juya ya kalli mai shagon yace haba Muhsin ashe dama haka kake ban sani ba, ashe daman mugu ne Kai mai zaluntar yara ban sani ba ai da na dauka rashin mutuncin ka DA masifar ka bai wuce iya mu manya ba ashe harda yara ma basu tsira ba.

Muhsin yace eh Kamalu da da kake tunanin mutuncin nawa iya Ku ya tsaya toh gashi yanzu ka gani da idonka cewar ba haka bane, in da yadda zaka yi dani kayi in gani. Da jin haka mutanen wajen suka fara watsewa suna barin su su biyu domin kuwa kowa gudu yake yi yayi ma Muhsin magana ya bude baki ya mashi rashin kunya daman awajen Kamala ne kadai baya raga mashi duk rashin mutunci shi yana tsoron Kamala.

Kamala yace kade ji kunya wallahi yanzu wannan karamar yarinyar mi ta maka da zaka dake ta haka, Muhsin ya wani taso da wata muguwar masifa kaman zai haye Kamala yace Kai kaga Kamala kabar ganin Ina raga maka wallahi ba tsoron ka nake ji ba, ya za ayi akan wata Karamar yarinya gata nan kamar wata er mahaukaciya zaka zo kana man masifa. Kawai ta wani zo shago na tana cemani wai tana jin yunwa haka ma jiya tazo shiyasa na Zane ta kuma gobe ma in ta Kara zuwa sai na kara Zane ta yana gama fadan haka bai ko tsaya jin abunda Kamala zai fada ya juya ya koma shagon sa.....................

Ku biyo ni page na gaba muji ya abun zai kare tsakanin Kamala da yarinyar😍😍😍😍😘😘.

Please kindly vote if u like my book and also follow me on my account. I love u guys😍😍😍.

Ni ce taku Mai rubutu Yasmeen.

08161606431

Idan nayi kuskure a gafarta Mani.😁😁😁😁

Rayuwar RaihanaWhere stories live. Discover now