Part........57&58

42 3 0
                                    


   *ZAFAFA WRITERS FORUM*
              Z.W.F


              _____BUTULU______

              NA
MARYAM ABDOUL
    *MAI_K'OSAI*

        WATTPAD@MARYAMAD856.

     PAGE........57$58

BISIMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM.

     

___________ Da k'arfinsa ya tura qofar d'akin , jiyake zuciyarsa na masa suya, shi za'a kawowa qaton gardi cikin gida, kuma ace za'a cutar dashi.

      Tura qofar sane ya sanyasu juyowa tare da katsemu su hanzarin su, duk da Latifa bata cika tsoron abubu ko samuwarsa, amma yanayin dataga Abdallah aciki sai da hantar cikinta ta kada.

   Bece uffan ba, saima qarasawa yai gabansu, qafarsa ya dora gefen gadon da suke kai, duk da cewa be damu da ya nayin da suke ciki ba, fuskarsa a daure ya soma magana.

     "Ban San me na aikata miki haka da zafiba, amma kisani duk wani Abu nawa da kika sani mallakina ne na baki nan da second uku ki kawo min su nan, Abu na gaba kije na sawwake miki har igiya uku, sannan nan da minti daya bana buqatar sakya ganin qazamar fuskar ki anan."

    Kai kuma, ya juya yana me fuskantar Bash kana yace " kai kuma kaje, amma ka tuna aure zakayi, kana da mata, zaka haifi 'ya ka qimanta in Kaine akama haka ya zakaji zafin rad'ad'in hakan a ranka?"

    Juyawa yai kan Latifa tana zaune, ganin batta da niyyar miqewa ya kuma daka mawa tsawa.cikin abinda baifi minti d'aya ba ta hado komi da tasani nasa ta ajjiye mai, ko kayan ta be Bari ta d'auka ba ya iza qiyarta zuwa waje. daman Bash tuni ya cikawa wandon sa iska, dan yaga Abdallah ba sauqi, kar nan gaba yayi mai abinda zai nakastashi.

     Kulle d'akin nata yai, yai wucewarsa d'akin sa, Abu goma da ashirin sun taru sun masa zafi, "ya ilahi" itace Kalmar da ya furta a fili.

%

            Su fatima kam koda suka koma gida maida zancan suka shigayi ,nan Daddy yai tabawa Fatima haquri irin yadda Abdallah ya zalinceta har Saida ta sanya kuka akan danme zai dinga bata baki?, sannan kowa yai shiru da maganar.

    
    %

Kiran wayar bata Jima da shiga ba aka d'aga, cikin girmamawa ya shiga gaida mutumin, tare da mai bayanin abinda yasa yai kiran nasa.

    Sosai yaji dadi qwarai da gaske, be ta'ba tsammanin abinda ya rasa din zai dawo gareshi ba.

     "A jikin lalitar akwai address Dina, ka kashe ko nawane Dan Allah ka kawo min, in kuma ba dama ni ganin yanzu zan taho"  

Abinda ya iya cewa kenan kawai sabida tsabar farin ciki, ba tare da ya jira amsar Ammar ba ya katse kiran.

    Kallon Innar tasu yai dan Jin me zata ce, nunfasawa tai kan tace " ka barshi yazo din, amma inaga ka tura mai kwatance unguwar tamu, dan naga farin ciki ya hanashi ya tambaya"

   Dariya sukai dukan su, Dan gaskiya ta fad'a. Nan Ammar ya shiga rubuta masa kwatance tare da tura mai, suka zauna zaman jiransa.

   

     %

Abdallah kuwa juye Kawai yake kan gadon sa, zuciyar sa ciki da malolon tarin bakin ciki da damuwa.

    Tabba ya tafka babban kuskure Wanda har abada bazai ta'ba iya gyarawa ba, ya kalubalanci Fatiman sa akan yawo gidan kwartaye, sai gashi shi kwarton a ka kawo masa har cikin gidan, abinda be ta'ba hangowa ba koda a mafarki, yanzu ya zaiyi, ta ina ZAI fara gyara kuskuren sa??

             BUTULU.....Where stories live. Discover now