Part......63&64

46 2 0
                                        

*ZAFAFA WRITERS FORUM*
             Z.W.F.........


           _______BUTULU______

      NA
MARYAM ABDUL-AZIZ
    (MAI_K'OSAI)


WATTPAD@MARYAMAD856.

Page...... 63%64

Bisimillahir Rahmanir Raheem.

       NOTE:-Masoyana Kuyi hakuri bisa jina shiru da kukayi, hakan ya farune sabida Wasu dalilai.nagode.



__________Komi na gidan yayi qura, kai ka rantse ba'a ta'ba zama a gidan ba, kasancewa sa watanni ba mace a gidan, kuma ko 'yan aikin babu, illa Kawai mamallakin gidan ne ke zaune a cikin sa.

    A hankali ya tura k'ofar d'akin nasa, a raku'be  ya hangoshi, ya rame yayi baqi dashi, cikin sauri ya qarasa inda yake a kwancen, tallafo kansa yai tare da d'ora shi kan cinyarsa, wani hucin zafine ya ziyarci duk ilahirin jikin nasa kasantuwar rabar da yamasa.

  Sabeer kenan, wanda dawowar kenan, ko gida be leqaba ya fara biyowa tanan, dan yaga shi mutumin ko waya baya masa.

   Shine kuma ya taddashi a wannan ya nayin.

    "Me yai zafi haka Abdallah, me yasa kakesan kashe kanka?"

   Bai bashi amsa ba illah fashewa da kukan da yai, Dan wannan tambayar sai ta dad'a fama mai wani sashi na zuciyarsa, abinda ya Jima yana jira wani ya masa tambaya akan hakan, amma sai yanzu.

    Ganin bashi da niyyar magana, ya sanya zaro wayar sa ya latsa lambobin likitan da suke gani in wata matsalar ta shafesu.

  Nan ya shiga gaya mai halin da abokin nasa kuma dan uwan yake ciki.

   Befi minti ashirin ba sai gashi, nan yama sa duk wani bincike da ya kamata yayi, amma yana tantamar abu d'aya, hakan yasa ya nemi da suje asibitin.

      %

Watan cikin Fatima biyar cif yanzu, yayin da Hisham keta shirye-shiryen tafiya USA ,duk da cewa su duka biyun ba'a San ransu bane, yaso tafiya da ita, amma hakan be masu ba Dan taqi bashi hadin kai .

    Yau ya rage saura kwana biyu tafiyar tasa, duk tabi ta rame ,gashi batasn yai tafiyar kuma batason binshi, gudun kar ya fasa take ta danne wasu abubuwan.

   Tana zaune tana had'a mai kayan ya shigo, sabida tsabar zurfin tunanin da tai batasan lokacin da ya shigo d'in ba.

   Kafad'arta ya dafa cike da yak'e yace " sai da nace na miki biza mu tafi tare kika ce " a'a" ni inaga Kawai zan fasa tafiyar."

   Cikin sauri ta goge qwallar data zub'o mata tace " Dan Allah kar kace haka, nifa bani da wata matsala"

    " hmm amma kike kuka, kuma kika rame?" Yace.

    " ba haka bane, Kawai dai nasan zanyi kewar ka ne, amma ai komi zai wuce, ba kullum muna maqale a waya ba, nasan ina nan din ka"

   Ta qarashe tana nuna mai saitin zuciyarta.

   Dariya ta bashi, sai dai ba yadda ya iya, duk da yasan ba hakan bane, amma shikkenan tunda tace hakan.

    " to shikkenan my queen, ai tamana addu'a dai, kuma adaina kukan nan dai, kinga zo inji lafiyar baby nama"

  Ya qarasa yana me janyota jikinsa.

       %

Bincike da yai ya tabbatar masa da gaskiyar hasashen da yakeyi.

   Gyara zaman gilas d'in dake makale a fuskarsa yai kana yace" gaskiyar magana, Abdallah yana cikin wani hali, dan memory nasa ya jirkice, a yanzu dai haka zamu iya cewa ma yana shirin haukacewa dalilin surutan da yakeyi da yawan tunani da ya tsanantawa kwakwalwarsa, sannan yana dab da kamuwa da ciwon zuciya, wannan shine abinda bincike da mukai ya nuna mana"

   "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un" , shine abinda Sabeer keta nanatawa, "to yanzu meye mafita??"

   Likitan ya nunfasa kana yace " mafita d'aya ce, asami abinda yake da muradi, duk da naji yamata ambaton Fatima, yakamata asama masa ita tayi jinyarsa yawan ganinta zaisa memory nasa ya dawo, kuma zai sami sauqin ciwon nasa."

Tir'kashi, Ana wata ga wata, Fatiman dake gidan mijin ta......Bari muga ni zata zauna ko Kowa me zai faru....!!!

    

       %

Tun asuba ya kammala shirinsa na tafiyarsa, da yake jirgin 6:30am zai bi, da qyar suka rabu da juna cikin kewar zuqatansu.

Ita dai Fatima badan ranta yaso kawai zaiyi tafiyar nan ba, Dan koda ya tafi sai taji gidan ya zame mata tamkar kurkuku, ji take wani iri sabida ba sahibinta a tare da ita.



   Hisham kam bashi suka ISA ba sai wajen 10:45pm , a wani hotel suka sauka, kowa ya kama d'akin sa, da yake tafiyar ta qungiya ce daga ma'aikatar su.

    Sai da ya watsa ruwa sannan ya zauna ya shiga fidda kayan sa dan ajjiyesu a inda ya dace.

  Rubutun da yai arba dashi NE ajikin wani kwali karami yaja hankalina sa "*I love u but I miss u my one* " shine abinda aka rubuta.

  Nan ya shiga warware kwalin, wani qamshin ya dake hancinsa, cake ne a ciki, sai pepper chicken a jikin pepper rafa, sai kuma wata takarda .

   Takardar ya bude ya karanta, Wanda acikin tane yaji sak'on lallai ya bude kwalin data bashi me girman.

Nan ya sauka daga gadon ya shiga budewa, flask ne mai d'auke da sakwara , d'an qaramin kuwa miyar dage-dage  ne aciki, ,sai fruit salad, da lemon K'wai da madara.

  Wani dad'ine ya cika mai cikin zuciyar sa, wayarsa ya janyo ya danna mata video call,dan yana San kasantuwar da ita.


      %

Sabeer kuwa baisan inda zaisa kansa ba, shiri yai kawai ya nufi gidan su Na'ima, Allah ya temakeshi ya sami Hajiyar Na'iman, nan ya shaida mata halin da mutumin yake ciki, in San samune su Daddy su shigo cikin lamarin.

  Sosai ta kid'ima da Jin batun, kuma insha Allahu zasu tattauna da su Daddyn asan yadda za'ai.

  Nan suka a rabu a kan jibi zata masa bayanin abinda suka tattauna.


    
       %

"Wallah ina gaya miki irin alkhairin da yaron nan yamin, kedai Allah ya saka mai da alkhairi"

   Nunfasawa Hajiya Lubabatu tai kana tace " ameen, ai Alhaji kyautatawa tana da kyau a rayuwa, tana sa mutum ya qara  samun ci gaba a rayuwarsa"

   Ya gyad'a kai kana yace " tabbas, Allah yabamu ikon kyautata ma mutane"

    "Ameen tace masa"

Suna haka Mansur ya shigo ,nan suka sakya gaisawa da iyayen nasa, Alhaji da abin arziki ya sameshi takya bakinsa ya soma zuba.

   Cikin farin ciki Mansur yace " madallah, amma wannan mutumin yanada kirki, ba kowa ne zai maka haka"

   "Hakane" inji baban nashi, daga haka basu qara tattaunawa ba akan batun.


   
Vote , Share , and Comment




*Real Mai_k'osai.........*
  
  

             BUTULU.....Onde histórias criam vida. Descubra agora