*BUTULU*
By
*Maryam Abduul**wattpad@maryamad856*
💫 *DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION.*💫
*DAGA MARUBUCIYAR:-*
*BIYAYYA**Part.....23*
BISIMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM.
.....................Taga da yaji shaqa nan ya fara qoqarin neman temako, Tabawa jin kamar ana kiran ta yasata fitowa daga d'akin, nan tashiga qoqarin qwatarsa tare da sa ihu za'a kashe mata d'a.
Mama Suwaiba ce ta fito cikin sai sauri ta qarasa inda suke tate da qoqarin cire hannunsa akan wuyan Taga.
Nan malam Audu ya sigo ya taddasu suna fad'a kaca-kaca, tsawa yadaka musu kan su rabu, sosai Tabawa take haki.
Nan yasoma tambayar meke faruwa, karaf Tabawa ta cafe da fad'in " malam kawai bai san hawa bai san sauka ba yakamashi da duka, kasan baqin halin nasa ai, ni wllh sai an d'au mun mataki"
Mal Audu da yasahaqa ya fesar kallon Ammar yai kan yace" amma anyi d'an banzan yaro, wannam wani irin iskanci ne haka, ti ka bud'e kunnenka kaji ne dakyau daga yau sai yau bakai ba gidan nan dan haka maza kafice kabani waje kar na qara ganinka acikin gidan haka kawai zaku kashe mata d'a "
Cikim firgice Mama Suwaiba ta kalli mala. audu kan tace" haba malam wannan wani irin hukunci ne wannan, yakamata ka tsaya kabi ba'asi kan kai haka, kada kayanke hukunci cikin fushi"
"Dalla yimin shiru ni har zaki gayawa bincike bayan wanda nai yanzu, wllh idan baka fitaba sai na tsinemaka yanzun nan" malam Audu ya fad'a a fusace.
Jin hakan yasa Ammar suma bashi haquri amma ina kamar yana zuga malam Audu, ganin hakan yasa Mama Suwaiba jan hannunsa tare dayin soro dashi, kallonsa tai idanta cike taf da qwalla kan tace" jeka Ammar ganian fitowa maza jeka wajen Inna."
Nan Ammar yasa kai ya fice yayinda Mama Suwaiba ta koma ciki tare da d'akko mayafinta tai waje, tanaji malam Audu nata zuba masifarsa.
Itakam Tabawa tasa d'an nata tai zuwa cikin d'akin ta, nan malam Audu ya mara musu baya.
Taga d'ane ga Tabawa su biyu ta haifa amma ba tare da malam ba, Zaliha itace 'yarta ta biyu, sam yaran basu da tarbiya ko kad'an, sun raina kowa basa ganin kowa da gashi.
Fitarsu ke da wuya suka wuce wajen Inna, bata ta'ba kai qararsa wajentaba amma batajin yau akan wani banza can zata jure wannan iskancin.
Inna na zaune tana lazimi suka shiga, bayan sun gaisa ne Mama Suwaiba ta shiga gayamata abindabke faruwa"
Iya qololowa Inna takai bata ta'ba tsammanin haukan nasa yakai hakaba, nan ta miqe tare da zarar mayafinta tace" suje gidan"
Suna shiga ta taddasu zaune a saman tabarma suna maida zance, yayinda malam ke bata haquri, wani takaice ne yakama Inna.
Nan ta shiga surfamai tata masifar ta inda take shiga bata nan take fitaba, sosai tamusu tatas dan ba wanda ta bari acikinsu.
Suna haka 'ya'yan suka fito, dan bayan fitarsu Zaliha ta shigo.nan ta had'e su ta zagesu, tate da fad'in " duk randa ka sake cewa yabar ma gida to wllh nima ka tabbatar ka barni har abada, dan bani bakai" daga nan taja hannun Mama Suwaiba sukai d'aki.
Nan tashiga rarrashinta da lalla'bata tare da bata baki akan ta qara haquri alan wamda takeyi watarana imsha Allahu sai labari.
Sukam su malam qusqus suka shiga yi, daganan ma ficewarsa yai daga gidan.Inna kam bata bar gidanba sai bayan azahar, yayinda Ammar ya rigada ya fita aikinsa.
YOU ARE READING
BUTULU.....
RandomQalubale daga wajen mijinta sabida wasu larurori datake fama dasu.......kubiyoni dai acikin wannan 'kayataccen labarin Dan jin ya zata kasance. Banyishi Dan cin zarafin wani ko wata ba...'kir'kirarran labarine....kada a juyaminshi...Dan Allah akiya...