butulu...part..14

142 6 1
                                    

〰〰〰
*BUTULU*
〰〰〰

Story...writing by
  *Maryam Abduul*
  
Wattpad @maryamad856

💫 *DA BAZARMU WRITERS ASS.💫*

We are here to make you happy.....smile and educated to realized that we are the best among all
*DA BAZARMU MUKE TUN'KAHO*💃💃💃

*Marubuciyar:
    *BIYAYYA*

   
*page....14*

*BISIMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM*

********Ranar da akasanya bikinmu tazo, nan aka tsaida bikin nanda sati biyu tunda anrigada anyi duk wani shirye-shirye da za'ayi.

Acikin wannan satittukanne naga qauna da tsantsar soyayya dan kwa kusan kullum sai yaya Abdallah yazo, kuma bazai ta'ba zuwa hakaba sai yazomin da wani abin bazatar, har kwana yayi agidan aunty sabida ni, cayaimata ma shifa yaqagu ayi bikin nan.

Lokacin kam ya Ihsan wani yafito nemanta saidai ita sam tace batta da ra'ayin yin aure hakan yasa yajanye amma bai daina neman soyayyartaba.

Sosai aunty tamaida hankali gareni wajen yimin gyaran jiki, da sauran abubuwan da akewa amare.

Nan fa akashiga hidindimu kamar ba gobe, Saliha kam gidan aunty ta dawo dayake nima d'in ban dawo gidaba sun roqa da abarni anan agama bikin.

Anakshe kud'i sosai awajen bikin namu dan event kala hud'u akai, wannan ranar saida na tuna da mamina sosai nadinga kuka kai kace ruwan hawayen nawa zasu qare.

Saida ya Abdallah yazo sannan ya rarrasheni, wanda ko da nayi shirunma ba abinda nakeyi sai ajjiyar nunfashi.

Ranar Asabar shine ranar da aka d'aura aurena da ya Abdallah wannan rana mace azama tamkar me awajena, bazan ta'ba mantawa da ita arayuwataba, dan rana ce da takasance abar alfahari awajena, rana mai matuqar mahimmanci da farin ciki, dan nasan na aure farin cikin zuciyata kuma masoyina na har abada nasan bani da wata fargaba.

Satinmu biyu da yin auren na fara samun matsala da aunty zubaida dan daddy ba wani samun isasshen hutu yakeba ayyuka sunmai yawa bai zama yanzu.

Ga kuma Granny da itama tafara manyanta abubuwa sai ahankali, gashi data fara sa damuwa sai ciwin kai da qirji wanda hakan yasa akace tana d'auke da hawan jini, wannan yasa nace mata" ta dinga d'auke kai abubuwan dasuke faruwa, komi mai wucewane".

Ranar da aka kawoni gidanmu amatsayin amarya kuma matar ya Abdallah aranarma saida aunty zubaida ta shuka rashin mutuncinta, dan har qaryar rashin lafiyata wanda dole kowa hankalinsa ya karkata kanta, dan batari mun kebe da ya Abdallah ba har natsawon kwana biyu.

Muna cikin sati na ukune Daddy yayi magana da Granny wanda bamusan me sukaceba, alokacinne kuma aka yankoma visa ta barowarmu daga garin, wanda nibansan abinda ake shiryawa sai da ana gobe tafiyar Daddy ya kirani yashiga min fad'a da nasiha, sannan ya gayan abinda aka shirya, acewarsa kar na fad'awa kowa koda Saliha ce.

Aikam ba wanda na gayawa amma can qasan zuciyata inajin ba dad'i sabida banason rabuwa da 'yan uwana musamman Saliha da Granny.

Ranar da zamu tafi da daddarene aka shirya komi, aunty zubaida sam batason wainar da ake to yawa ba, har jirhin mu ya d'aga indawi mukayo garin Kano ta dabo tunbin giwa.

Koda muka sauka hotel muka kama dan har alikacin bamu sami gidan da zamu zaunaba dan shi yaya Abdallah cayai" gidan da Daddy yabashi bai masaba"

Saida mukai sati guda cif sannan muka sami gida a rijiyar zaki, zamanmu nida yaya Abdallah sai nace sam barka, dan bani da wata damuwa, kuma mukanyi waya da su Daddy da Granny awayar yaya Abdallah, wannan yasa naji dad'in zamana anan har nakejin garin ya matuqar burgeni sa'banin da danazo da farko.

             BUTULU.....Where stories live. Discover now