P 47&48

43 2 0
                                    

               ******BUTULU.......




              NA

Maryam Abdoul
       *Mai__Qosai*





Part.....47/48


Typing.............



Bisimillahir Rahmanir Raheem.






           Kano ta dabo tunbin giwa (koda me kazo an fika).


  ----------------Yalwatacciyar iskar garin ce take kada ya nayin yayi kama da lokacin damina, sai dai ko kadan ba lokacin bane.

   Kwance yake kan gadon sa sai faman neman layin Sabir yake amma amsar d'aya ce dai "switch-off"

   Tsaki yaja kan yai wurgi da wayar, cikin Jin haushi yaceb" banza haka yana can yana shashancin nasa "


   Sakkowa yai daga kan gadon , kayansa ya maida jikin ya zari mukullin motarsa yai waje, duk da besan ma ina ya nufa ba.



    Tuqi yake amma yana tunanin halin da makomar sa take ciki, tabbas duk wanda yaiwa Allah butulci akan abinda ya basa to ba makawa zai halaka, kuma bazai kuma samin rahma irin ta ba, matuqar ba tuba yai ba.

       Da wannan tunanin ya qarasa wajen aikin Sabir sai dai nan ma shima aka tabbatar mai da baya nan, tsaki ya kuma ja a karo na biyu, kan ya juya akalar motar tasa.






*********
     Su granny kuwa jirgin karfe shida Na safe suka biyu, zuciyar su cike da d'okin ganin 'yar uwar ta su.


    Koda suka iso Dr.Auwal ne da Daddy sai Sabir suka je dakko su.



   Wayyo zukuga murna wajen Fatima, Granny da kuma Saliha, da yake su biyun suka taho .


   Kamar zasu hadiye juna Fatima da Saliha abinka da anjima ba a hadu ba.


  Da qyar suka samu suka ci abinci, nan aka hau horar yausha gamo, tare da maimaita baqin labarin da suka riska.


   Sosai zuqatansu suka tabo da Jin wannan mummunan lamarin, Saliha kam har kuka Sai da tayi "iya zalinchi yaya ya zalunchi kansa, kuma da Sannu zai girbi abinda ya aikata" wannan shine Kalmar da Kawai ta iya furtawa.


   Cikin nuna juriya da San kauda bacin ran dake qasan zuciyar ta granny ta kalli Saliha tace " kul kar Na kuma ji daga bakin ki, kemai fatan shiriya Kawai, kar ki manta komi da zai sami bawa muqaddarine kuma an rigada an rubuta shi a littafina bawa, wannan jarrabawa ce, kamata yai ki taya ta addu'a fatan samun nasarar cinyeta "


   Cikin kuka Saliha tace " amma granny kinga irin abinda ya aikata kuwa"

  " ke gani kai? ,ba labari Kawai aka baki ba, fan haka bana son fitina, aure dai sai a gyara shi ta koma Allah ya rufa asiri"

   Cikin sauri Saliha tace " Wllh granny ba inda Aunty Fatima zata koma ,ko shine autan maza na rantse"


    "Tunda kice Fatiman ko bana son shashancin banza"


   Ganin hakan yasa Daddy katsesu ta hanyar fad'in " a'a Hajiya ai aure daman ya Riga da ya rabo, dan yanzu bikin 'yara nan da sati uku masu zuwa  , Allah ya bata miji fiye da Abdallah, Hajiya abar zancan shi yaiwa kansa"


   Jikin granny ne yai sanyi , tabbas taso ita ma hakan, amma tana matuqar son Abdallah da Fatima, amma bakomi shi yaiwa kansa, Abu guda dai ta sani tabbas da wuya yasani irin Fatima.



  Wunin ranar hirar su Kawai sukeyi ta sakya sabon ganin juna, duk second daya ya buga sai Saliha ta tsinewa yaya Abdallah ta a zuciyar ta irin yadda ya wahalar mata da yaya, har sana din sa me sunan Daddy ya bar duniya.



********
   Ammar kuwa sai wajen hudu da rabi na yamma motar su ta tsaya a nan tashar IBB dake cikin garin Kano.

 
    Yanzu dai gashi a kano, sai dai shi kansa besan waca nahiyar zai SA kansa gaba ba.

  Waje ya samu ya zauna, tare da tunanin mafita ga rayuwarsa ta yanzu.



  Jerin wasu matasa ne yaja hankalina sa, yayin da ya zuba musu Ido, sosai ya fahimci abinda sukeyi (dako) Dan ya lura idan mutum ya sauka a mota sai suje suna " Hajiya/alhaji d'auka ne? "

   Idan ance ehh su d'auka, Sanda suka dawo wajen su nan zakaga fuskar su cike da murmushi wasu na mueza kudin da ke hannun su.


    "Nima haka zan fara daga yanzu"

Ya fad'a yana me murmusawa.

Miqewa yai ya dau kayan sa ya rataya a hannun sa na dama, ya hau jerin layin matasan.






             BUTULU.....Donde viven las historias. Descúbrelo ahora