*WATA UNGUWA*
*(Labarin game da wata hargitsattsiyar unguwa mai cike da abubuwan al'ajabi)**ALƘALAMIN RUƘAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)*
*MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH*
*YAR GANTALI*
*RIKICIN MASOYA*
*RASHIN GATA (GAJEREN LABARI*
*HALITTAR ALLAH CE*
*AND NOW*
*WATA UNGUWA**AREWA WRITERS ASSOCIATION*
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
Free page
P2
BABI NA BIYU
A wannan ranar da misalin ƙarfe 11 na safe, wata ƙaramar yarinya da ba za ta wuce shekaru biyar ba a duniya ce na hango a cikin wani layi tana tahowa daga nesa.
Bata sanye da komai face bante fari wanda tsabar dattin da yayi idan ka gan shi sai ka ɗauka kalar ruwan zuma ne. Fuskarta ta yi face-face da busasshen kunu hancinta dame-dame da majina, kallo ɗaya zaka yiwa jikinta ka fahimci cewa jikinta ya jima bai ga ruwa ba.
Tafe take tana yan wasanninta irin na yara har ta zo ƙofar wani gida, turus ta tsaya tana kallon ƙofar gidan. Turawa ta yi ta ji kofar a rufe gam.b
Da ganin haka ta koma gefen kofar ta zauna tana kuka tana faɗin "Mama! Mama!! Mama!!!"
Wata sassanyar iska ce ta ratsa ta shiga cikin jiki da ɓargonta, ta ƙara takure jikinta guri ɗaya alamun sanyin ya ratsa ta sosai.
Can bayan wani lokaci da ta ga ba alamar dawowar mahaifiyarta yanzu sai ta miƙe ta fara tafiya tana kuka tana shiga gida-gida tana neman Maman nata.
Wani gida ta shiga a layinsu ko sallama bata yi ba.Matar gidan tana duƙe tana wanke-wanke ta ga yarinya tsaye a kanta tana kuka. ɗagowa ta yi tana duban yarinyar "A'ah! Salma! Lafiya ki ke kuka?"
"Mamata!" Ta faɗa cikin kuka
"Me Maman naki ta yi?" Ladidi ta tambaya.
Cikın shessheƙa ta ce "Ita nake nema bata shigo ba?"
"Bata shigo ba, je gidan yaya Hanne ki duba ta."
Yarinyar ta fice tana ci gaba da kukanta.Ita kuwa ta ci gaba da wanke-wankenta tana faɗar "Biba ikon Allah! Yau kuma gantalin ya tashi a unguwa ko ina ta shiga ta bar wannan kucakar yarinyar?"
Ganin ba mai amsa mata ya saka ta ci gaba da aikinta.
Salma tana fita ta miƙe hanyar da za ta sada ta da layin gidan yaya Hanne(yayar mahaifiyarta) tana shigowa kan layin gidan dai dai nan wani Babur ya danno cikin layin zai fita, bai yi aune ba ya kaɗe ta.
Ihu ta ƙwala wanda ya gigita shi, bai tsaya ganin ko 'yar waye ba kawai ya ƙarawa babur ɗinsa giya ya fece ya na faɗar "Ku ga yarinya zata jaza mun bala'i yasin ba zan tsaya ba."
Kawu Sadi da ya shigo layin yanzu ya hango abun da ke faruwa sai dai kafin ya ƙaraso gun tuni mai laifin ya gudu.
Da hanzari ya ƙaraso inda take ya tada ta zaune don duba ko ta ji rauni.
Tabbas ta ji rauni, bakinta ya fashe da jini ɗaya daga cikin ƙananun hakoranta masu kama da haƙoran ɓera ya fita, kanta ya fashe sakamakon ƙumuwa da kan ya yi da dutse yayin da take faɗuwar.Kan kace me, jama'ar layin sun cika gun an kewaye ta ana ta jimami. Wani ƙaramin yaro ne na ga ya juya da gudu ya shige wa gida a layin, zuwa jimawa kaɗan sai ga shi ya dawo tare da Biba da yaya Hanne.
"Innalillahi wa innailaihir raji'un! Salma me ya zo dake nan?" Ta faɗa kamar za ta fashe da kuka ta rarumi 'yar ta zuwa shagon magani mafi kusa.
Sun mata duk taimakon da ya dace sannan ta saba 'yar ta a baya ta nufi gidanta.
YOU ARE READING
WATA UNGUWA
Actionlabarin kwamacalar dake afkuwa a wata hargitsattsiyar unguwa, akwai al'ajabi a labarin.