*WATA UNGUWA*
*(Labarin game da wata hargitsattsiyar unguwa mai cike da abubuwan al'ajabi)**ALƘALAMIN RUƘAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)*
*AREWA WRITERS ASSOCIATION*
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
11 June 2021
Free page 7
BABI NA BAKWAI
Jibgarta yake ba ji ba gani, ko gani baya yi sosai tsabar ɓacin ran da yake jiki. Tuni ya makance da hango duk wani aibu dake tattare da dukkan da yake mata, sai buga mata icen yake duk inda ya samu.
Umma da ta ga abun bana ƙare ba ne, kuma idan har ta zuba ido komai zai iya faruwa ga tilon yarta mace, hakan ya sa ta ƙarfafi zuciyarta tare da shiga ɗakin cikin hanzari.
"Don Allah Malam ka dakata haka, idan rai ya ɓaci bai kamata hankali ya gushe ba, zaka iya raunata ta fa.""Ki bari in mata dukkan kawo wuƙa Indo, ta yanda zamu raba raini, kinga gobe in har na ɗora mata doka ba za ta tsallaka ba." Ya faɗa yana huci kaɗan kaɗan.
Icen dake Hannunsa Umma ta riƙe ta ce "Don girman Allah ka yi haƙuri Malam, idan kace zaka daka ta yaran zamani to lallai sai dai ka illata su ka janyo wa kanka abun faɗa."
Karɓe icen ta yi daga hannunsa, har ya juya zai tafi ya dawo daga baya, ya fuskanci Maheerah ya ce "Ki ji ni da kyau, ni ne dai mahaifinki damar zaɓa miki miji tana hannuna, don haka na ba ki nan da sati biyu ki yankewa kanki hukunci, in har ba za ki auri Irfan ba to ki samo madadinsa a tarbiyya, in ba haka ba zan aura miki duk wanda na ga dama."
Yana gama faɗa ya fice cike da damuwa ya yi waje, sai da ya zo soron gidan ya tuna da ya bar baƙonsa a waje, don haka ya yi saurin ƙarasawa gunsa.
Daga cikin gida kuwa Malam na fita Umma ta kalli Maheerah "kin dai ga abinda kika jawa kanki ko? Ga irinta nan, a karon banza da wofi kin jawa kanki jibga. Ina gaya miki ki ajiye wannan girman kan ki yi biyayya gare mu ko kya samu tsira a gobe ƙiyama."
Yunƙurawa ta yi daƙyar ta tashi, don duk jikinta ya yi tsami ta ce "Umma ba wai ina bijirewa zancenku ba ne, a cikin zuciyata ne bana son kowa sai Ja'afar a yanda nake ji zan iya shan guba idan na rasa shi."
"La'ilaha illallah! Har abun na ki ya kai da mummunan ƙuduri haka? Lallai kin yi nisa bakya jin kira, Allah ya shirye ki."
Da gama faɗa ta juya zuwa ɗakinta tana mamakin wannan al'amari na Mahee, ko dai yaron nan asiri ya mata ne?
Bayan kamar mintuna arba'in Maheerah na kwance tana jinyar jikinta da ya mata nauyi, ji take kamar wasu gaɓoɓin jikin nata sun karye. Ta tsunduma kogin tunanin abun sonta ko me Baba ya masa? Mummunan faɗuwar gaba ce ta ziyarce ta, hankalinta ya kasa kwanciya.
Wani ɓangare na zuciyarta ya shawarce ta da ta kira shi, domin tabbas ba lafiya, shirun ya yi yawa.
Hannu ta miƙa ta janyo wayarta da ke nesa da ita kaɗan, ta hau dubawa. Kamar dai yanda ta yi tsammani bai kira ba, bai turo saƙo ba.
Jikinta ne ya yi sanyi laƙwas, kamar wacce aka zarewa lakka ta ɗaga wayar tare da kiransa, sai da ta kira sau biyar bai daga ba.
Hankalinta ya kai ƙololuwar tashi, domin tun da take Ja'afar bai taɓa ƙin daga wayarta ba sai yau, babu shakka ko ba a gaya mata ba tasan fushi ya yi.
Tana nan cikin tashin hankali da tunanin mafita sai ga saƙonsa ya shigo wayar.
Da sauri ta fara karantawa kamar haka: "ke Malama, kada ki takura mun a daidai lokacin da nake tsakiyar shauƙin soyayya da Sahibata. Tun da har Abbanki ya kore ni shi ke nan, na yi masa alƙawarin ba zai kuma gani na ba a gidansa indai ni ɗan halal ne."
YOU ARE READING
WATA UNGUWA
Actionlabarin kwamacalar dake afkuwa a wata hargitsattsiyar unguwa, akwai al'ajabi a labarin.