p 15

49 0 0
                                    

*WATA UNGUWA*
*(Labarin game da wata hargitsattsiyar unguwa mai cike da abubuwan al'ajabi)*

*ALƘALAMIN RUƘAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)*

*AREWA WRITERS ASSOCIATION*

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*


22 JULY 2021

LAST FREE PAGE 15

BABI NA SHA BIYAR

Ganin Mahee bata da niyyar ko motsawa domin ta yi nisa sosai a cikin barcinta, hakan yasa bisa ga tilas Umman ta haƙura da tayar da itan ta koma ɗakinta ta zauna tana mamakin wannan barci haka. A ranta ta ce "Inta ta shi ai sai ta rama sallolin da bata yi ba, amma wannan barci..."

Maheerah kuwa bata farka ba sai wajajen 12:30 na dare. Da salati a bakinta ta buɗe idonta a hankali tana ƙarewa ɗakin kallo.

Jim ta yi na ɗan lokaci tana tuna abunda ya faru a yammacin ranar, da ƙarfi ta runtse idonta, wasu hawaye masu zafi suka sirnano mata.
"Astaqfurrullah! Astaqfurrullah!! Astaqfurrullahil azim!!" Abun da take ta maimaitawa kenan kafin ta buɗe idonta tana jin wani irin kunci da ya mamaye zuciyarta.

"Ka cutar da ni Ja'afar! Na ɗauke ka a matsayin masoyi nagari, ina yi maka kallon nagartaccen mutum ashe ban sani ba kura ce da fatar Akuya, ka zamo tamkar hankaka gabanka fari bayanka baƙi." Ta furta a hankali tana sauke ajiyar zuciya.

Wayarta ta janyo da nufin ta duba lokaci.
"Kai! Ashe haka lokaci ya ja ko sallar Magriba ban yi ba?" Ta furta da yanayin mamaki haɗe da takaicin halin da ta tsinci kanta a ciki.

Har zata ajiye wayar ta lura da misscalls ɗin dake gaban wayarta, cire key ɗin ƙaramar wayar ta yi tare da dubawa.

"Mtsww!" Ta ja wani dogon tsaki.
"Allah ya fika macuci kawai." Ta furta domin ganin kiran Ja'afar ne ta rasa.

Ajiye wayar ta yi sannan ta yunƙura daƙyar ta miƙe zuciyarta na mata zafi. Sai dai har zuwa lokacin jikinta baya da ƙwari ko kaɗan duk da cewa mayen ya sake ta.
A haka ta samu ta rama sallolinta sannan ta kuma kwanciya duk da idonta ya bushe ƙyam bako alamar barci.

Daren a haka ta kwana har gari ya waye bata rumtsa ba sai saƙe-saƙe  take a ranta.

Ta yankewa kanta hukuncin cewa ba zata sake ɗaga wayar Ja'afar ba, haka duk abinda zai sake kusanta ta da shi ba zata yi ba.
Ko da yake har yanzu ba wai zuciyarta ta haƙura da Ja'afar ɗin ba ne. Kawai tana so ne ya fuskanci girman kuskuren da ya aikata, sa'annan ita yar gidan Malamai masu daraja ce.

ASALINTA

MAHEERAH 'ya ce ga Malam Isah Saminu Kaita, Malam Isah haifaffen ƙauyen Kaita ne a cikin jihar Samburi dake ƙasar ta su.
Mahaifinsa ya kasance shararren Malami ne a ƙauyen nasu, su biyu ne kacal a gurin mahaifinsu daga shi sai ƙaninsa Sa'adu, sun ta so a ƙarƙashin kulawar malamin addini saboda haka suka kasance masu tarbiyya da ilimi sosai, da suka fara tasawa sai suka fara taya mahaifinsu aikin nasa na karantarwa a makarantarsa dake ƙofar gidan nasu. Kwanci tashi har su ma suka zama manyan Malamai da har suka so su zarta Mahaifin nasu.

Watarana kawai sai suka wayi gari da gawar Mahaifin nasu.  Mutuwar ta taɓa su sosai, bayan rasuwar mahaifin wani sirri ya bayyana a gare su cewa 'yan uwansa Malamai ne suka jefe shi saboda suna hassadar ɗaukakar da ya samu.
A lokacin sun ƙaryata wannan maganar a zahiri domin cewa suka yi "Ba wanda zai mutu sai in har kwanansa sun ƙare dama, kuma Allah ya faɗa a cikin alƙur'ani 'Kullu nafsin za'ikatul maut.'" don haka suka rufe wannan babin.

Sai dai wani abunda jama'ar garin da Malam Sa'adu ba su sani ba, wannan maganar ta tasirantu sosai a cikin zuciyar Malam Isah har ta ɗarsa masa tsoro. Dalilin kenan da ya sanya ya gayawa ɗan uwansa cewa shi zai matsa zuwa gari na gaba domin ya ci gaba da ba da karatu, sa'annan ya ƙaro ilimin zaman rayuwa domin shi ilimi kogi ne. Dama 'yan magana sunce zama guri ɗaya tsautsayi ne,  kuma ma ace kullum mutum yana zaune guri ɗaya tamkar kifin gwangwani?

WATA UNGUWAWhere stories live. Discover now