*WATA UNGUWA*
*(Labarin game da wata hargitsattsiyar unguwa mai cike da abubuwan al'ajabi)**ALƘALAMIN RUƘAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)*
*AREWA WRITERS ASSOCIATION*
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
13 kune 2021
Free p8
BABI NA TAKWAS
A tsakiyar wani ɗan madaidaiciya gida ne na hango wata ƙatuwar tabarma an Shimfiɗa ta a tsakar gidan yara ne 'yan ƙanana ga su nan kamar ƴaƴan ɓeraye a kan yawa, sai ƙiriniya wasu ke yi.
Daga gefe kuma masu ɗan girman ne ke cin abinci sun tasa kwano a tsaka sai rige-rigen ci ake.
Can Safiya ta yi saurin wawurar tarin shinkafa da Naman da ke gaban Na'eesha.
Na'eesha da saurin hasala ko tsayawa jin ba'asi ba ta yi ba kawai ta wanke ƙanwar tata da Mari.
"Lalalala! Ni kika mara?" Cewar Sadiya yar 13y,
"An mare kin Ubanwa ya ce ki ci mun abincin gabana....?"
Kafin ta gama rufe bakinta ta ji saukar wani gigitaccen mari da ya kiɗima ta, da sauri ta juya tana waige-waige ko za ta ga Gardin da ya mare ta, domin bata taɓa tsammanin wai Sadiya ce ta iya aikata hakan ba.Ko da ta fahimci haka, sai ta harzuƙa ainun ta kama kan yarinyar ta maka da bango tana kai mata naushi.
Cikin hanzari Inna Halima ta jefar da butar hannunta ta yi gun da sauri ta ƙwace Sadiya a hannun Na'eesha tare da ture Na'eeshar gefe ta ce "Amma ke dai wannan yarinyar akwai halin banza, don zalunci haka kawai ki kama yarinya da bugu, ka ga shegiya mai kama da aljanu?"
"Ban haifi azzaluma ba, haka ban haifi shegiya ba ga shegiya nan a gabanki ita da ta tasarwa zambo, kuma ita ta ja." Mama Rakiya da ke zaune a ɗakinta tana jiyo su ta faɗa.
Cikin masifa Inna Halima ta nufo ƙofar ɗakin tana faɗar "Ke Rakiya ki fita idona in rufe, in masifa ki ke ji nafi ki iyawa yanzun sai mu yi namu, ashe ma kina jin su da yake kin ga yarki ce Babba shi ne kika zuba ido ana zaluntar 'yata?"
Wata ƙatuwar dariya Rakiya ta saki tare da faɗar "Yaya Halima kenan, kinsan ni ban cika shiga sha'anin yara ba kamar ke, barin su na yi mai ƙarfi ta ƙwaci kanta. Sannan faɗa da ni ba daɗi yanzu zaki kirawa kanki ruwan da ba zaki iya tare su ba."
Habawa ko da Inna Halima ta ji haka sai ta harzuƙa ainun, nan fa su ka hau cecekuce dama kowa zuciyarsa a baki take.
Sosai suke musayar yawu kamar za su buga, yara masu wasa suka dakatar sai kallonsu suke, wannan na faɗar 'Innarmu tafi ƙarfi, wannan ya ce Mamarmu tafi zuciya, to ku bari dai mu ga wa za'a yiwa kaye." Haka yaran suke ta faɗa a tsakaninsu.
Suna tsaka da haka ne Sakina('yar gidan iya mai bakin Aku) ta shigo gidan da sallamarta ta zo siyen Lalle gurin Lantai(ɗaya daga cikin matan gidan) sai dai ko da ta zo ƙofar Lantai a rufe hakan ya tabbatar mata da ta fita sai rigima da ta tarar Ana yi.
Talatu(matar gidan)da ke kwance a ɗaki tana jin duk bidirin da ake, sai yanzu da ta ji Sallama ta leƙo tana faɗar "Me kike so Sakina?"
"Am Lalle na zo siya.. ta faɗa tana kallon ɓangaren masu faɗan.
Da alama gabaki ɗayan hankalinta yana gun masu rigimar tana ɗaukar rahoto."Af wannan ne dama? To kawo kuɗinki na ba ki, ga shi ta bari a guna."
Ba musu ta miƙa kuɗin lokaci ɗaya kuma tana ci gaba da kallon dramar da ake a gidan.
Can Talatu ta miƙo mata lallen ta ce "Ga shi sai ki yi azama, da alama in kika tsaya kallon dramar gidan nan za ki kwana a nan ko kanki ya faɗo." Tana 'yar dariya ta yi maganar tare da shigewa ciki abunta.
YOU ARE READING
WATA UNGUWA
Actionlabarin kwamacalar dake afkuwa a wata hargitsattsiyar unguwa, akwai al'ajabi a labarin.