Wace Ta Dace Dani

7 3 0
                                    

*_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*

*WACE TA DACE DANI?*


*story n written by*
*Ummy Ontop*




Page 3-4



Lamis kwance tana juyi ita kadai kan madaidaicin gadon ta gaba daya ta tsumduma kogin tunanin Dameer daya taimaka mata a makaranta , tunani take be Santa ba betaba ganinta ba amma ya taimaka mata gaskia mutumin kirki ne, a iya rayuwarta bataga namiji daya dace da ita ba sai Dameer , shine irin mijin da take mafarkin ta aura shine wanda take zana siffarshi cikin mafarkin ta ashe dagaske akwaishi ckin duniyar acewa wani sashi na zuciyar ta , dole tashiga cikin rayuwar shi dole ta nemo a inda yake , zuciyar ta baxata barta ta nutsu ba idan bata nemo mata mamallakin ta ba, kamar wacce aka mintsina tayi zunbur ta mike zaune batare da tasani ba tafurta a fili nayi sake dana bari yatafi ban San indah yake ba ko sunanshi ban sani ba dole na nemoshi nasani xaki iya lamis bantaba son Abu na rasa ba kuma bazan fara rasawa ba akan Kyakkyawan saurayin nan ba.

******

Bayan Dameer yagama cin abincin yatashi yayi wajen ammin tare yagansu sai hiransu suke ita da Dr mahad anashan daria, yacce Dr mahad ya baje yake zuba shine yabawa dameer mamaki kamar ya manta da fitan dazasuyi du ya azalzaleshi amma yanxu yazo nan ya baje yanata zuba, gyaran murya Dameer yayi sannan yace" wai Hiran mei kukeyi ne haka ammi tun dagacen nake jiyo dariyar Ku , ammi tace sirri ne biya kasha labari Mahad yace ahto kai baka xauna cen ba kai kadai anyi bakai, harara Dameer ya sakarwa Mahad yace tou seka tashi mutafi ka azalzaleni kuma kaxo nan kayi zamanka ammi mu zamu fita, tou saikun dawo Ku kula da kanku Allah ya taaremin Ku suka amsa da ameen sannan sukasa kai suka fice a gidan,

Kayansu dasuka iso daga itali yaje dubawa kaya sunyi sun gama komai sai bayan magariba sukabar wajan , a hanyarsu ta dawowa Dameer yake fadawa Dr Mahad labarin Lamis, Dameer yace " yarinyar tayi sedai abunda zai baka takaici da ita batada class , wannan idan kanwata ce saina zaneta muka koma gida, itama abunda yasa na taimaka mata kasan banason ganin ana wulakanta mace du lalacin ta gayen nan ya batamun rai da banxo wajen ba cin mutuncin daze mata saiyafi haka, Mahad yace ai kadan ka gane matan zamanin nan fa sun wuce tunanin ka danma ba mu'amala kake da matan ba sosai shiyasa amma sunzama abunda suka zama , tou Allah ya shiryamu baki daya Dameer ga fada yana sauke ajiyar zuciya har gida Dr mahad yakai Dameer sedai yaki shiga ciki kasancewa yana Sauri ze wuce asibiti kuma dare yayi, saukeni bakin gate ma tunda kaga jiranka ake  a asibiti basai ka kaini ciki ba Dameer ya fada yana jawo wayarshidake ajiye gefe , tou Aboki Allah bamu alkhairi sai munyi waya anan sukai sallama Dr ya wuce Dameer yakarasa shigewa gida.

Yana shiga ya Tatar da ammi a falo tana kallo lami na zaune tana matsa mata k'afa har andawo ina Dr mahad din , ya wuce hospital Dameer ya fada a takaice, Ga abincin ka a dining yana jiranka , a koshe nake ammi kuma na gaji ne xanje masallaci idan na dawo zandan kwanta ne zandai sha tea ne kawai shikuma sai bayan na dawo, tou shikenan adawo lafiya .

*****



12:00am dare ya soma nisa Dameer ya fito daga toile dauke da towel daure a qugunsa da daya yana goge ruwan dake sumar kanshi, seda yagama tsane ruwan yajawo farar jalla biyarshi ya zira yasa turarenshi mai sanyin kamshi ya haye kan sallayar shi domin gabtar da salla daya saba gabatarwa nafila kafin yakwanta bacci kullum ne saiyayi wanna salla tazamemai kamar wani sashi na rayuwarshi koda bacci yadaukeshi beyi ba saiya tashi yayi, Dameer ma'abocin ibada ne baya wasa da ibada ko kadan, salla yayi raka'a biyu yazauna yayi addua sosai bayan ya kammala ya nade dadduma ya nufi makeken gadonshi wanda yake bango guda ne ya haye yayi addua bacci , sedai bacci yaqi samuwa fuskar Lamis ta giftamai ta cikin idanunshi kawar da tunanin yayi Amma Sam fuskarta yaki dainamai gizo , zancen ta ke fadomai  *Yazaka tafi banyima godiya ba* yarinyar tanada zakin murya muryarta ya burgeni da yanayin yacce take magana yafada yana smiling ahaka bacci yayi awun gaba dashi.





******

Wanene Dameer?

Muhammad Yusuf Muhammad shine asalin sunanshi ana kiranshi da Dameer Yusuf dashi kowa yasanshi d'ane ga Ambassador Yusuf Muhammad Raji, babanshi babban dan kasuwa ne kuma dan siyaya mutumin kirki ne maison taimakon al'umma da gajiyayyu mai gaskia da amana ne mahaifinshi mutum ne na mutane, alokacin dayayi tafiya U.S hanyar dawowa jirginsu yayi hatsari, a lokacin da labarin mutuwarshi ta baza koh ina mutane sunyi kukan rashinshi sosai har suka dangana , sai danshi yazamar wa jamaA jigo kamar mahaifinshi.


Mahaifiyarshi shi matar kirki ce kamar mahaifinshi sedai ita tanada zafi bata daukar raini koh wulakanci amma mutuninyar kirki ce

Suna zaune a kano.

Dameer mutumin kirki ne kamar mahaifinshi, yanada hakuri da biyayya ga iyaye da duk wanda ya fushi yana bawa kowa girman shi baya raina mutane koh ya suke , yanada gudun zuciya tausayi saukin kai sedai baya daukar raini ba'a shiryawa dashi anan bashida surutu sosai.

Fari ne dogo mei dan jiki yana da sumar kai wacce ta karamai kyau da gemunshi luf gwanin burgewa,
yayi karatunshi mai zurfi har zuwa matakin MSC a business administration, yazama babban dan kasuwa Dan baya aikin gwamnati dorawa yayi daga inda babanshi ya tsaya, sabida shi kadaine mahaifinshi ya haifa a duniya , Hajia zainab ita kadai ce matarshi
Tunda aka haifi dameer Allah bekuma basu haihuwa ba sedai hajiya zainab tayi bari da dama .

******

Wacece Lamis

Y'ace ga Alhaji Nasir Aminu, da hajiya Binta garba, mahaifinta yanada rufin asiri daidi gwargwa do ma'aikacin gwamnati ne a gidan nepa tun tana k'arama sukayi hatsarin mota ita kadai ce ta tsira mahaifin ta da kanin mahaifinta Ya'au Aminu da mahaifiyarta babu wanda yayi rai duka suka mutu , a hannun k'anwar mahaifinta ta taso Yasira, alokacin da ana tunanin wane zai dauki lamis ya rike ta dage ita zata rike lamis harta aurar da ita bakomai yasa tayi wannan yunkuri ba saidan kadarorin lamis da mahaifanta suka mutu suka barmata zaidawo hannunta, haka kowa ya hakura ya sallama mata aka barmata lamis a wajen ta tun tana shekara daya a dunia ta raine ta har ta girma


Baba yasira ita da mijinta  tanko mai turare yana sayar da turare dan duri a kifar gidanshi suka haye kan dukiyar marainiya suke watayawa San ransu , ita kuwa lamis basu damu da ita ba baba yasira tanada yah guda biyu duka mata maryam da habiba su kana kallonsu kasan sunajin dadi ita kuma lamis sai yacce hali yayi , babu wata cikakkiyar kulawa datake samu bare har ayi maganar tarbiya.

Lamis asalin sunanta Aisha ake kiranta da lamis ,
tunda ta taso babu cikakkiyar kulawa babu ishasshiyar tarbiya a tare da ita asalima dama itadin mai rawar kai ce cike take da yarinta a tare da ita, sedai du abun nan sun kula da karatun ta sabida gudun maganar dangi, ahakanma wataran sai ankai ruwa rana kafin a kukuta a biya mata kudin makaranta.

Shiyasa lamis ta taso ba kintsi ba kamin kai itace cin bashi itace kula kawayen banza sedai duda haka batayi watsi da martabar ta ba.

Wannan kenan


******


Maimunatooh

WACE TA DACE DANIWhere stories live. Discover now