Wace Ta Dace Dani?

7 4 0
                                    

*_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*

*WACE TA DACE DANI?*

*story n written by*
*Ummy Ontop*





9-10


Naifa sai kai kawo take cikin harabar Asibitin cen tasamu waje ta zauna ta zabga tagumi tare da tunani kala kala cikin zuciyar ta saka wannan warware wance take tayi lallai Lamis nacikin mawuyacin hali fatan ta Allah ya bawa Aminiyar ta lafiya, cen Saiga Dr mahad ya fito kiran Naifa yayi suka shiga office dinshi bayan yamata izinin zama shima ya zauna a tashi kujerar ya hade hannayenshi biyu tare da sunkuyar da kai kana Yakuma dago dakanshi ya kalli Naifa tare da ajiye siririyar ajiyar zuciya sannan ya soma magana" mene alakarki da Mara lafiyar da kika kawo, Naifa tace Aminiya tace" ina iyayen ta Dr mahad yayi tambayar tare da kurawa Naifa ido danjin Mezata ce,


Iyayen ta basa nan, karatu take anan ,tou ko zaki iya fadamin gaskia tundake aminiyar ta CE nasan kinsan gaskiyar, inshaAllah Dr , Mahad ya sauke numfashi sannan yace" Amma yarinyar nan tana shaye shaye koh , damm gaban Naifa ya yanke ya fadi domin tasan abunda Dr ya fada gaskia ne, karki boyemin , Naifa ta sunkuyar da kai k'asa sannan tayi kokarin furta Tabbas tanayi amma ...
Amma mei? Dr ya tambaya, amma a baya ne yanzu ba sosai takeyi ba,
Dr mahad yace "tou abunda yajanyo mata halin data ke ciki yanzu kenan, wannan shaye shaye yaso ya juyar mata da tunani gaba daya , yazamar mata dole ta daina domin lafiyarta idan har bata daina ba tabbas lafiyarta nacikin matsala babba, a matsayin ki na Aminiyar ta yakamata kitaka muhimmiyar rawa wajen taimakawa lafiyarta, Naifa tayi shiru cen k'asan ranta tana ayyana taya zata shawo kanta bayan itama halinta ne shaye shayen duda ita batakai Lamis din ba.
Ina fatan kin fahimci menake nufi maganar Dr yadawo da ita hayyacin ta, du maganin dazan bata da wani temako matukar bata daina ba a banza zai zama, inshaAllah Dr zanyi du iyakar kokarina zankuma sanar sda iyayen ta dansu sa ido akanta sosai. Shine dai mafita cewan Dr.
Yanzu baxamu sallame ta ba sedai ko zuwa gobe tasake samun hutu. Bakomai Dr Allah yakaimu goben , ameen bari na rubuta miki magungu nan dazaki siyo wa kawar taki, takadda yaja ya rubuta mata sannan yabata tamai sallama tafita a office din.

Dr yayi jugum mamaki du ya isheshi ace yarinya burwa mai karancin shekaru amma cikin wannan hali lallai zamani yazo karshe.



Koda fitan Naifa wajen magani tawuce dan tasiyo tana siyowa tayo dakin da aka kwantar da Lamis kwance take hannunta daure da drip tana bacci bakin gadon taje ta zauna tana kallon ta yacce take bacci a nitse. Allah yabaki lpia kawata



****



A hankali tasoma bude idonta harta gama budesu duka ta saukesu cikin dakin tanabin dakin da kallo ruwan dake daure a hannunta tagani sai lokacin ta fahimci asibiti take, turo kofar akayi a hankali Naifa tashigo dauke da flaks din tea da leda hannunta ajiyewa tayi gefe , Lamis kin farka ya jikin naki, Alhmdlhi naji sauki Naifa, karasawa kusa da Lamis tayi ta tallafota ta zauna muje ki watsa ruwa nakawo miki kayanki, da abun break.. Bari na kira nurse ta cire miki abun nan naga Dr bai karaso ba , Naifa ta juya zataje kiran nurse lamis tayi saurin rik'o hannunta jiyowa Naifa tayi lamis ta sakar mata murmushi sannan tace" nagode aminiyata dabadan ke ba nasan sai yacce hali Yayi nagode , uhm lamis kinjiki dawani Abu ai ke yerUwa tace, nidai ina zuwa bari na
Kira nurse bata tsaya jin mei lamis zata ce ba tasakai tafita daga dakin.

Dameer ne yafado mata a rai wasu zafafan hawaye suka zubo mata , meyasa! Meyasa ne kake wahalar da marainiyar zuciya ta , a ina zan sameka a ina zan ganka yaushe zakazo gareni soyayyar ka tana neman hallakani ka tausayawa jaririyar zuciya ta wacce bata taba sani *SO* ba sedata ganka, najima ina jiran bayyanar ka kuma na ganka saika bacemin...turo kofar da akayi ne yasa tayi saurin goge hawayen dasuka zubo mata, nurse din tacire mata sannu koh ya jikin naki lamis ta amsa da sauki , kamata Naifa tayi takaita toilet ta dawo, bayan ta gama wankan tafito kayanta tasa Naifa ta hada mata tea da break hadda wainar kwai ta zauna taci sannan tasha magani, Dr mahad ne yashigo ya yadda Lamis nacin abinci lallai kinsamu sauki tunda har ana iyacin abinci Lamis ta sunkuyar dakai kasa tana murmushi, Naifa tace ai saukin kam yasamu Dr tou Allah yakaro sauki Naifa ta amsa da amin bari naje na dawo sai a rubuta muku sallama ko tou Dr cewan Naifa.



Bayan fitan Dr wayarshi tasoma ruri Sunan Dameer yana tsalle saman scream din dauka Yayi tare da kara wayar a kunnenshi, Aboki ya akayi katashi lpia, banji meyace ba kawai Dr yace ok tou seka shigo ina jiranka daga haka ya katse wayar ya wuce office dinshi.




*******




Dina na zaune ta zabga tagumi abun dunia ya isheta tarasa meke mata dadi tunanin wanda tagani a yanar gizo take har yau be karbi request din nata ba kamar ma anjima ba'ahau account din ba gashi tagani dan kano ne garinsu ma daya kodanshi zataso takoma koma kano sedai gaba daya karatun nata saura kadan gara tabari tagama ta taho gaba daya tunda idan tazo kano ma basanin shi tayi ba ba kuma tasan ta ina zata fara ganinshi ba gashi koda hotonshi bata gani sosai sai iyakar suman kai da idanu abunda tasani du inda taga wannan idanun tana kyautata zaton zata ganeshi.

Misha ta jijjigata ta motsa a firgice misha tayi. Dariya ganin yacce ta tsorata kd kuwa ina hankalinki yake sai faman mgn nake kin zubawa window ido bakyajina ,uhm tunanin mexanyi daya wuce project dina. Kai dina shine zesaki irin wannan zurfin tunani kedai akwai wani abun bashi ba Tou ni karki dameni tunda baki yadda ba dina ta fada tana mikewa daga wajen da niyar barin gurin Misha tayi dariya sannan tace idan tayi tsami zamuji ne.




*******



Kofa aka tura bayan anyi nocking anji shiru amma seyaga wayam babu kowa cikin office din kai ina kuma Dr Yayi bayan nacemai ganinan zuwa wayarshi yazaro dan kiran Dr mahad din saikuma yaganoshi cen yashiga wani daki tsuka yaja ya bi bayanshi wata nurse ta karya kwana hannunta rike da files dayawa tana zabga Sauri dawuri kamar zata tashi sama sukasha karo itada Dameer komai ya zube shikuma ya dafe kanshi dan ya bugu saurin kwashewa tayi ta dago tana bashi hakuri bakomai kawai ya iya furta mata sannan yayi gaba   dakin dayaga Dr mahad yashiga nan ya nufa,


Dr mahad yace tou zaku iya tafiya yanzu tunda ansallameku dan Allah Ku kula da kyau kubi du dokokin dana shinfidaku akai shine kawai samun saukin Naifa ta amsa da inshaAllah Dr za"a kiyaye , yawwa Allah ya kara sauwakewa , daidai lokacin da Dameer ya karaso nocking yayi tare da murda kofar ya tura a hankali.....







Maimunatooh

WACE TA DACE DANIWhere stories live. Discover now