Wace Ta Dace Dani?

6 4 0
                                    

*_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*

*WACE TA DACE DANI?*

*story n written by*
*Ummy Ontop*




7-8





Ranar Monday tunda sassafe Damir ya kira Dr Mahad wayar tagama ruri be dauka ba , saukowa yayi daga tangameman gadonshi ya fada toilet ya sheko wanka ya fito a gaggauce yayi shirin sa cikin Sauri duda gaggawa yake amma yayi kyau milk colour shadda daya sa tahau jikinsa sosai, gashin kanshi ya kwanta luff gwanin burgewa sai kamshi yake turarawa kowani sashi na jikinshi na fidda sanyanyan kamshi mai dadi zuqa.



a gogon shi ya Zara ya daura a hannu yadau car key da wayarshi yasanya hula ya karewa kanshi kallo gaban dressing mirror shi kanshi yasan yes yayi kyau 💯, smiling yayi yana tunano gashi ga lamis yau sun hadu , sedai koh me zefara cemata, ganin dai yanata b'ata lokaci yasashi ya fita a dakin koda ya sakko k'asa bega kowa ba alamu sun nuna mutan gidan basu fito ba gani yayi kamar ze bata lokaci idan yace sai ya jira an hada breakfast yaci kuma yasan koda yaje site din Ammi ba lallai yanzu ta tashi ba yasan ta koma bacci idan tayi salla asuba tayi azkar nata tagama tanadan komawa bacci 10am take tashi ta kintsa a hadu a breakfast. Kuma yanzu 8:30 agogon dake makale a hannun shi ya nunamai.

Zefita yayi kicibis da inna balaraba mai aikinsu ta gaidashi a gaggauce ya amsa yayi waje zuciyarshi cike da farinciki, inna balaraba ta juya tana kallanshi ganin yacce yau yake zambada Sauri gaisuwarma ta gagara yacce aka saba cen qasan zuciyar ta tace yaukuma ko farincikin me akeyi da gaggawan nan ganindai bamai bata amsa yasa tayi ciki dan fara aikinta.

Wajen da aka tanada dan ajiye motoci yaje yayi parking nashi motar sannan yafito cike da zumudin yaga lamis inda suka hadu nan ya nufa sedai babu kowa a wajen beyi k'asa a gwiwa ba yasamu waje yazauna a wajen yana jiran tsammani.


Tun makaranta bata cika ba har dalibai suka cikata anata kai kawo shiru har aka shafe sama da awa biyu babu giftawar lamis amma hakan baisa Damir ya karaya ba yasawa zuciyarshi tabbas zega lamis yau

Wayarshi ce tahau ruri ya duba sunan Dr mahad yake yawo kan screen din dan murmusawa yayi sannan yadauki kiran , Dr mahad yace barka Aboki ka kirani nashiga wanka lokacin kuma dana fito banbi takan wayar ba nayi asibiti sai yanxu nasamu kaina, bakomai Aboki ni yanzuma haka ina makarantar su lamis, mutumi na baka da dama kace harka shiga, touh meza'a jira Dr ,Dr Mahad yasa dariya kafin yace" ince dai andace, inafa tun shigowa ta banga Mai kama da ita ba bare nasa ran zan ganta, zuciya ta tafaramin zafi Dr Nasoma karaya burina naga yarinyar nan yau nasamu na zayyana mata halin da zuciya ta ke ciki ko zansamu sassauci daga radadin da takemin, ka kwantar da hankalin ka Aboki inshaAllah xa'a dace kasake jira kadan nadan lokaci nima ina hanya zanzo na taddaka, tou shikenan saika karaso daga haka sukai sallama Dr mahad ya kashe wayar yana jijjiga kai da tunano Dameer lallai Wannan karon so beyiwa Dameer da wasa ba dama ka ki yayi Wanda so baitaba ritsawa ba ranar daya ritsaka baxakaji da dadi ba da wannan zancen zucin yakarasa abunda zeyi yafita dan zuwa wajen Dameer.


Karfe daya saura minti goma agogen dake hannun Dameer ya nuna tashi yayi jiki sanyaye ya nufi wajen alwala yayi yashiga masallacin cikin makarantar dan gabatar da salla azhar.
Bayan sun idar fitowa yayi Yakumawa wajan daya baro ya zauna , sam ya rasa mekemai dadi kuma ga dukkan alamun bashi da sa'a ne amma tabbas idan ya rasa samun yarinyar nan zeshiga wani hali yana wannan tunanin ne kiran Dr Mahad yashigo wayarshi jiki du yayi la'asar haka yadauka ya kara wayar a kunne , kwatancen indah yake yamai saiga Dr ya karaso zama yayi kusa da Dameer wanda kana kallonshi kasan cikin wani yanayi yake , kafadanshi Dr mahad yayi sannan yace" Haba Jarumin maza karka bari so yasauyama yanayi mana har yanxu ba'a dace ba kenan, Ajiyar zuciya Dameer yasauke kafin yayi karfin halin furta, baxaka gaane halin da zuciya ta take ciki ba yanxu Dr kuma ni nasoma karaya ga dukkan alamun yarinyar nan ba karatu take cikin makarantar nan ba kuma da ace nasan koda sunanta ne sainaje nayita cigiya har adace da wanda yasan ta a makarantar.

Karka cire rai Dameer bafa aje koh ina ba kake kokarin karaya shiga SO bayason rago a tafiyarshi idan ka karaya yazakayi da zuciyar ka kenan, saikace ba namiji ba karka bani kunya dan Allah inshaAllah ina tare dakai zanbaka du gudumuwar daya dace.

******


Tun wancen lokaci Dameer yana faman neman Lamis kullum saiya shiga makarantar ko za'a dace amma shiru har aka shafe sati guda inda alokacin yasoma fitar da rai da ganin Lamis ya barwa Allah komai yasan idan yana da rabon sake haduwa da ita Allah zenufa, sedai tabbas zuciyarshi nacikin sarkakiya tana azabtuwa da tunanin Lamis kullum cikin nadamar rashin tsayawa sauraranta yake inama akoma baya daya gyara kuskureb dayayi.

******

Sautin nishi ke tashi daga cikin karamun dakin koda na leqa Lamis ce ke kwance inda fuskarta tayi kacha kaca da hawaye tana fitar da kuka Mara Sauri idanunta sunyi jawur wanda dakyar take iya dagasu gefen ta kuwa wasu kwalabe ne birjik a zube wasu babu komai anshanye abun da ke cikinsu,sallama ake bakin kofar amma takasa koda motsawa bare tasamu damar magana, kutso kai akayi aka shigo Kawarta  Naifa ce , saurin yasar da jakar ta tayi ta k'araso kusa da lamis , lamis afiya kuwa kike meya sameki tamata tambayar a Jere , lamis wacce dakyar take iya bude idanunta bata samu nasarar bata amsaba sabida yacce gurin ke juya mata tana ganin komai goma goma,dogon ajiyar zuciya lamis tasauke wanda dagashi bata sake motsawa ba , Innalillahi waEnna Elaihi rajiUn Naifa ta furta da karfi Lamis ! Lamis!! take kiranta tana jijjigata cike da tsoro karara tatattare da ita.





*****

WACE TA DACE DANIWhere stories live. Discover now